← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

misalin 9:pm Hajiya Fulani tashiga part d'in Sarki Jabir cikin tsananin damuwa a kishin gid'e tasameshi gaidashi tayi cikin girmamawa kamar kullum ko kallonta baiyiba balle ya amsa cikin damuwa sosai tace " ranka shidad'e dama maganar makarantar su Fadil ne naji cewa su Ansar zasutafi nanda sati 1 amma naji bakayimin maganar su Fadil ba kaga shi yad'an jima yanajira to senayi zaton had'asu kakesonyi dasu Ansar shiyasa banyi magana ba " wani irin mugun tsaki yaja yace " tashi kibani guri jin muryarki ta'isheni haka idan kuma kikacigaba dazama zakisha mamaki ........ " kamar Yaya fa Maimartaba ? " Cewar Hajiya Kilishi dake tsaye bakin qofar part d'in tun bayan shigowar Hajiya Fulani qarasawa ciki tayi tazauna tadubeshi sosai tace

" Gaskiya Maimartaba hakan baikamataba nikam abinda kakeyima Fulani yafarabani tsoroma kenan har yaran nakama abin yake neman shafa ina gaskiya ni bazan iya jurar hakanba idan har baza'ahad'a su Fadil dasu Ansar tafiya Skul ba tofa suma su Ansar d'in sede suhaqura sutazama har zuwa lokacin daka canza tsari dan kam bazan iya jurar zargin jama'a ba sabida wallahi nasan nice abin zagi tunda nice mai yara barima nace nasanar dasu sudakatar da duk wani shiri bayanzuba " tana gama fad'ar haka tamiqe zatabar parlour dakatar da'ita yayi dafad'in

" Dakata Hajiya Kilishi to meye kuma nayin fushi bayan bakiji nace hakaba nifa tare nanemar musu Skul amma senaga kamar mahaifiyar tasu batabuqatar hakan shine dalilin dayasa nike ganin kamar batashiryabane " girgiza Kai Ammi tayi tace " haba Maimartaba itakam maiye nata idan kace ayi akwai wanda zaice a a ? dan Allah kayi adalci atsakaninmu dakuma tsakanin yara dan gujema fad'awa cikin fushin Allah da azabar shi dan Allah kar kasa nima nadinga zargin kaina wajan hanaka yin adalci sabida nice babba duk cikinsu kuma munada kyakkyawar fahimta ni da Kai dan Allah Maimartaba kaji tsoran Allah "

Ajiyar zuciya yasauke yadubi Fulani wanda raban daya d'aga ido yakalleta har tamanta yace " kiyimusu duk wasu shiryeshiye tare zasutafi Ansar da Fadil Hanan da Fadila idan akwai wani abu kituromin Fadil ko Fadila susanar dani ke basekinzoba " murmushi Hajiya Fulani tayi tace " in sha Allah zanyi yadda kace nagode Allah yaqara girma ina godiya agareki Aunty Kilishi Allah yaqaramiki tsoran Allah " daga haka tamiqe tafita jiki a sanyaye binta dakallo hajiya Kilishi tayi cikin tausayawa shiko Sarki Jabir fuskar Hajiya Kilishi yake kallo dawoda dubanta tayi gareshi kafin tayi magana yace

" Basekince komiba Kilishi banada amsar baki banace ga lefin Fulani agareniba zuciyatace kawai ta tsaneta lokaci d'aya babu dalili nasha bambayar kaina meye dalili amma har yanzu nakasa ganoshi badan babu saki a gidan sarautaba idan babu wani dalili mai qarfiba datuni nasaki Fulani kodan itama tahuta to amma babu dalilin yin haka " nannauyar ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " gaskiya yakamata kadage da addu'a dukda nasan kanayi to amma kaqara Allah yashiga tsakanin nagari da mugu " shima ajiyar zuciyar yasauke yace amin dubanta yayi sosai yace " wato Hajiya Kilishi akullum jinki nikeyi sabuwa fil cikin wannan zuciyar tawa " yata'ba setin zuciyar shi kuma har qarshen numfashi ahaka zaki dauwama " murmushi tayi tace nagode sosai amma inaso acikin kasona na soyayyata dake cikin wannan kyakkyawar zuciyar taka karabashi 2 kabama Hajiya Fulani rabi zanyi matuqar farinciki idan kayi hakan " rumtse idonshi yayi yace " bazan iya hakanba kiyi haquri amma daga yau zuciyata zata dinga tunasar dani cewa Hajiya Fulani tanada alfarma awajan abar qaunata har abada yanzu tashi muje ciki wannan kamshin turaran naki yajawo miki magana ina matuqar son wannan turaran naki "

Murmushi Ammi tayi tace " ayya shiyasa yamantar dakai cewa yau ba Hajiya Kilishi keda haqqin sauke maka buqatar takaba ? Hajiya Fulani ce kabata duk kulawar da wannan zuciyar taka tayi shirin bani dan Allah " tana kaiwa nan tayi saurin miqewa tafita tana shiga part d'in ta babu jimawa tafito tanufi part d'in Hajiya Fulani tana shiga tasamesu zauna saman Cushion d'aya itada yaranta suna kallon Sunna TV sallamarta yasa suka maido hankalin su wajanta cikin sauri Fadil da Fadila suka miqe suka isa gareta rungumeta sukayi suna gaidata cikin farinciki shafa kansu tayi suduka had'ida saka musu albarka sannan taqarasa ciki nufar bedroom kowa yayi sukabar iyayen nasu cikin farinciki Hajiya Fulani tashiga yimata barka dashigowa bayan sun gaisa Ammi tadubeta sosai tace

" Hajiya Fulani ayau zanyimiki magana akan abinda yake faruwa tsakanin ke da Maimartaba gaskiya lamarin yanacin zuciyata batun yanzuba amma kasancewar lamarine na tsakanin miji da mata kuma ni ina matsayin kishiya baikamata nashigaba sabida nima dole ina cikin abun zargi sabida zaman kishi lamarin yanada wuya idan ke baki zargeniba to babu shakka wasu senun zargeni sede ni nasan har ga Allah kowannen ku zuciya 1 nike zaune dashi tsayin 18 yrs kuna zaman rashin jituwa a tsakaninku amma nayi tunanin ko wani lefi kikayi mishi to amma yau nayimishi magana akan haka abin mamaki shima bashida wani dalili hakanne yasa nazo nabaki shawara koda yau 1 ki'aje matsayin kishiya agareni kid'auka Aunty kice zatabaki shawara yakamata kisake dagewa da addu'a aduk lokacin dakikayi sujjata kidinga karanta wannan addu'ar barinayimiki misali da kaina dan nima karki cireni cikin zargi halin kishi ne

ALLAHUMMA DAMMIR KILISHI KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA ) ALLAHUMMA DAMMIR HAJARA KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA ) ALLAHUMMA DAMMIR MARIYA KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA )

harama shi kanshi Maimartaba daduk wani wanda kikejin zuciyarki bata amince dashiba dasauran wasu addu'o'in neman tsari da kariya daga dukkan sharri in sha Allah zakiga kariyar Allah Allah yayi jagora sannan a garshe inaso yau kiyi amfani da wannan turaran " tamiqamata wani tsadadjen turare dake hannunta dashi nikeyin amfani akoda yaushe Sabida Maimartaba yanason shi sosai kije gareshi cike da karfin gyuwa kinji fatan alkairi Hajiya Fulani "

Sosai Hajiya Fulani tayi farincikin wannan shawara ta Ammi godiya tayimata sosai tamiqe dan rakota cikin sauri Jakadiya tabar bakin parlour daga la'ban datake tun shigar Hajiya Kilishi cikin part d'in amma takasa jin komi sabida sautin Tafsir d'in dake tashi cikin parlour nufar part d'in Hajiya hajara tayi cikin sauri

Bayan Hajiya Fulani taraka Ammi takoma part d'in ta cikin farinciki yau shiri tayi namusamman zuwa part d'in Maimartaba cikin 'bacin rai Hajiya Hajiya tamiqe tashiga kaiwa da komowa sannan tadubi Jakadiya cikin fushi tace " ayko yazama dole kibi duk wata hanya dan ganomin mai suka tattauna akai idan kikayi haka kinada kaso mai tsoka idan kuma kika kasa zan rage matsayin ki agareni zanbama wata damar shiga cikin lamarin mu na sirri " risinawa Jakadiya tayi cikin girmamawa tace angama Hajiya bani wani d'an lokaci kad'an " jinjina Kai Hajiya hajara tayi sannan tace " kya iya tafiya cikin sauri tafito wasu hadimai dake shirin shiga cikin part d'in suka dubeta bayan tawuce suka ta'be baki hadida cewa " hmmm su Jakadiya kenan iyayen kulma tunda kika ganta cikin part d'in Hajiya hajara a wannan lokaci tabbas wani munafincinne " jin kamar motsi yasa sukajabakinsu sukayi shiru suka idasa ciki

Sallama Hajiya Fulani tayi tashiga cikin part d'in Maimartaba baya cikin babban parlour hakan yasa tashiga cikin qaramin parlourn nanma bayanan kallon gofar bedroom d'in shi tayi sosai zuciyarta tashiga bugawa cikin qarfin hali tanufi qofar tsayin lokaci tana tsaye sannan tatura tashiga zaune tasameshi bakin bed yana duba wasu takardu dake gabanshi jin kamshin turaran Hajiya Kilishi yasashi saurin d'agowa amma seyaga Hajiya Fulani ce dukda bahaka zuciyar shi tasoba amma yaji wani sauyi sauke idanunshi yayi had'ida amsa sallamarta wadda yajima baya amsawa a fili sede a zuciya zama tayi agefanshi tanason yimai magana amma takasa tsayin lokaci har bacci yafara daukarta shiko kamshin wannan turaran yasa yamakasayin komi se faman juya takardun yakeyi tashi yayi yamaidasu sannan yashiga toilet tsayin lokaci yafito yashirya kwanciya dubanta yayi yakauda fuska sannan yatadata yace

" gyara kwanciyarki " mamaki abin yabata sosai sabida raban data kwanta saman bed d'in shi har tamanta babu musu tamiqe tazare abayar dake jikinta kyawawan kayan baccin jikinta suka bayyana tahau saman bed d'in saurin nufar makunnin wuta yayi yakashe sannan yadawo kwanciya yayi bayan ya kwanta cikin shakka da fargaba Hajiya Fulani tamatso jikinshi sosai yaji jikinshi ya tunasar dashi amaryar tashi amma kuma zuciyar shi tana qin haka rungume shi tayi sosai tasaki kuka tana fad'in

" Tabbas haqurina yakusa qarewa buqata tana neman halakani Maimartaba dan Allah kakulani koda zuciyar ka batason haka idan kuma babu aure tsakanin ni da Kai ne kasanar dani nasan matsayina " sake fashewa tayi da kuka tsayin lokaci baice komiba se zuwa can yace " banida dalilin sakinki sede nadena sonki amma yau zan sauke miki haqqin ki sabida dalili 2 kwai daga haka yasake rungumota sosai daga nanfa sassan jikin shi suka shiga bayyana mishi tsananin missing dinta dasukayi a wannan daran kamar wasu ango da amarya haka suka kasance sabida kowa yakasa gajiya duk da shikam zuciyar shi bataso amma yakasa hana kanshi nuna yunwarshi akan Hajiya Fulani

Bayan kwanaki 2 Jakadiya takasa samun cikakken bayanin da Hajiya hajara tasata samowa sede ta qirqiri gyarya tafad'a Hamut da Hamidat sunbar qasar Nigeria zuwa Jordan hakama Hammat yabar Nigeria su Hanan kuwa yaune suma suka bar Nigeria semuce Allah yabada sa'a madedecin gidane mai kyau da tsari iya tsaruwa yatsaru akwai komi namore rayuwa aciki aka siyama Hanan da Fadila ankuma had'asu da kuyangu sabida hidima sannan ansaka Security sabida tsaro kamar yadda akayima su Hanan haka akayima su Ansar

MAFARIN WATA BABBAR MATSALA GA HANAN

BAYAN WASU WATANNI

Kamar kullum yauma sundawo daga Skul agajiye suna shiga Hanan tanufi bedroom dariya Fadila tasaki tace haba Hanan duk gajiyarce ? Ayde kya bari muci abinci ko kumafa kinga yamma tayi karki kwanta bacci " juyowa tayi cikin yanayin gajiya tace
Chapter 7 · 0% Book details