← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake komawa tayi tacanza wasu kayan dubanta yayi yawatsar yace " hmmm yazanyi tunda anhad'ani da daqiqiya zonan "
Sosai wannan kalmar tadaki zuciyar Hanan amma babu yanda zatayi tanahawa saman bed d'in yajawota jikinshi kama kunnanta yayi yamurd'e sakin qara Hanan tayi sabida mugun zafin dataji yanashigarta dakamata tsawa yayi yace " kiyi abunda nasakaki sha sha sha kawai " hawaye Hanan taji suncikamata ido cikin kakkausar murya yace " karkisake kiyimin kuka hawaye 1nagayasauka saman wannan fuskar taki ko hmmmm"

Jin haka yasa Hanan saurin shanye hawayenta tafarayime tausa lumshe ido yayi yanasauke sassauqan numfashi

Baki d'auke da sallama Hamut yashiga cikin parlour shi kai tsaye yanufi bedroom din Hamidat batayi tsammaninshiba shiyasa tabar qofar abud'e arazane tad'aqo ido ganin shine yasa tasaki wayar hannunta sabida ta tsorata dashi sosai akan abinda yayimata jiya kallonta yayi cikin takaici yace

" kicigaba dayin wayarki nasan bazai wuce da uban wannan cikin najikinki kikeyiba dama zuwa nayi nayimiki albishir dacewa Allah yabani lafiya in sha Allah zanyi auran huce haushi anan kusa kekuwa babu duka babu zagi dakanki zakisamar makanki mafita marar alqawari maciyiya amana kawai kin kusa girbar abinda kika shuka "

Juyawa yayi cikin 'bacin rai zaifita cikin sauri Hamidat tasakko daga kan bed tashagaban shi marayrayce fuska tayi tace " D please am so sorry wallahi nayi nadamar duk abinda nayimaka tunjiya nike nadama dan Allah kamanta komi murufamakanmu asiri kagafa idan asirina yatonu kamar nakane yatonu sabida ni da kai duk abu 1 n........." Qaryane akwai banbanci dayawa idan asirinki yatonu nakine de yatonu bana Hamut ba haquri kuma ke yakama baniba nagode ma Allah dayanunamin rashin dacewarki matsayin mata agareni gaskiya Hammat yayi dace kuma yayi matuqar sa'a dasamun Hanan amatsayin mata nima Allah kabani mata mai irin halin Hanan ba ballagaza irin Hamidat ba "

Yanagama fad'in haka yatureta daga gabanshi yafita cikin takaici Hamidat takoma bakin bed tazauna iska tafesar daga bakinta sannan tace " hmmmm wallahi senatarwatsaku badai bakadamagana seta Hanan ba to nasha alwashin tarwatsaku kuduka tasanadiyyar Hanan d'in bazata qaremin ni 1 ba " wani shi'umin murmushi tasaki

Jakadiya tadubi hajiya Hajara tace

" Hajiya naji zance akan cewa za'a shirya wani gagarumin shagali dah agobannan ma to amma yanzu anbarshi senan da kwana 2 sabida baqi nanesa wai hajiya meye dalilin yin duk wannan ? "

Wani mugun tsaki hajiya hajara tayi ad'an fusace tace hmmmm Jakadiya karki qaramin abin haushi mana kamar yadda bakisaniba to nima haka aykin banza lamarin cikin masarautarnan yafarazama da renin hankali a cikin shi tayaya za'a dinga ajemu agefe hmmmm nalura idan har Hajiya Kilishi tanaraye tofa mu bazamuta'bayin kima da daraja a cikin masarautar nan ba "

" To yaya kenan yakamata ayi hajiya ? " cewar Jakadiya kafin hajiya hajara tayi magana Hajiya mariya dake tsaye bakin qofar tace " kasheta zamuyi kawai kowa yahuta " zaro ido Jakadiya tayi cikin rawar baki tace " a a a deee sakee wata shawarar ranki yadade kisa yayi tsauri dayawa girmanshi bakadan bane "

Harara sukawatsa mata Hajiya Mariya tace " babu canji hakan zamu aywatar kuma kece wadda zakigudanar dakomi idan kikayi wani yunquri akan tonamana asiri muhad'a har dake wajan kisan tashi kibamu guri "

Cikin matuqar gigita Jakadiya tafito daga cikin part d'in zufa tashiga tsastsafo mata duk dacewa basanyi akeyiba tofa tsaka mai wuya kenan

Tsayin lokaci Hanan tanayima Hammat tausar amma yakasayin bacci sabida muguwar shi'awar dake taso mishi jiyakeyi kamar wani salone Hanan keyime duk tasake hargitsashi tsaki yaja yace
" dalla tashi baki'iya komiba sha sha sha kawai " cikin rashin kujari tasauka daga bed d'in parlour tafita zuciyar ta a cunkushe babu abinda keyimata dad'i kitchen tashiga tafarayin qoqarin d'aura abinda yasakata babu jimawa hadimai suka iso da breakfast d'insu kalakala gaidata sukashigayi cikin girmamawa sannan suka shiga jera abincin sunagamawa suka fita sabida sunsan halin Hammat bayason hadimai suyime koda shara balle wani gyara fitowa Hanan tayi tashiga gyaran ko ina dukda babu wani guzari jikinta amma haka takeyin komi cikin lokaci kad'an ko'ina yad'auki kamshi misalin 9 Hanan tagama komi har cikin bedroom d'in shi tagyara komawa tayi cikin bedroom d'in ta ganin Hammat zaune yasatajin fad'uwar gaba dubanta yayi yajatsaki yamiqe yafita bedroom d'in shi yashiga yanashiga yafad'a toilet yayi wanka misalin 10:30 am yafito cikin shigar manyan kaya yafito angon sak gaskiya yayi matuqaryin kyau wata farar pepa yagani adede qofar bedroom d'in Hanan nufar gurin yayi yad'auki pepa yabude rubutune kamar haka

" _Assalama'alaikum burin zuciyata Hanan dan Allah inaso kinatsu kikaranta wannan saqon nawa nine yayanki Hamut Hanan sonki yashiga cikin zuciyata inaji bazan'iya rayuwa babukeba duk da kina auran bro na bazan iya barinkiba kiyarda muqulla wata alaqa tasirri mudinga hutawa tare dan Allah Hanan inajiran amsa daga masoyin ki Hamut_"

Murmushi Hammat yasaki yace " hmmmm lalle wato anfarayimin renin wayo kenan har abada bro na bazaiyi hakanba kuma ko cikin magagin bacci nike zangane asalin rubutun Hamut koma waye wannan soyaye yashiga tsakanina da d'an'uwana hmmmm har abada ba'ahaifi mutunba yazama dole nagane wanda yayi wannan abun komade Hanan d'in ce ? "

Yana gamafad'in haka yashiga cikin bedroom d'in afusace

Please Comment fatan alkairi gakowa kuyi haquri najinashiru nadawo daga Kd sekuma mukafara shidimar biki shiyasa kukaji shiru nadawo yanzu in sha Allah posting kullum

Mameen Zarah da Sudees ce 😊🤝🏻💖
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 47 & 48*

*G* anin yadda yashigo yasa Hanan saurin miqewa daga zaunan datake dubanta yayi daga sama har qasa tayi shigar atamfa wadda tasha dinkin zamani riga da siket tayi masifar amsarta sezuba kamshi takeyi qarasawa yayi gaf da'ita har suna iya jiyo numfashin juna cikin tsoro da rawar baki tace

" Dan Allah yaya kayi haquri bansan kafitobane shiyasa banzo nabaka abincin ba dan Allah yaya karkamin komi iya bugun da zuciyata keyi idan naganka ya i'sheni hukunci Yaya Allah zan'iya mutuwa idan bugun zuciyata yazarce haka dan........."

Sakar mata tsawa yayi had'ida fad'in " to kimutu d'in mana inada asarane kinga ayma nahuta dazama da qaramar yarinya marar asali irinki "

Nufar wordrop yayi yad'akko book da pen miqamata yayi cikin dakakkiyar murya yace " Ammi nikeso kirubutama saqon gaisuwa akaimata " amsa tayi cikin sanyin jiki tashiga yin rubutu kamar haka
_Amincin Allah yatabbata agareki Ammi na inafatan kintashi lafiya Ammi inamiqo gaisuwa agareki nayi matuqar kewarki uwar kirki Umar marainiya Hanan Allah yasakamiki da Aljannat Firdausi Ammi na ina_ ......."

Fige book d'in yayi cikin fusata yace

" kinanufin zantatsayuwa har sekinyi sanranki bakikai matsayin ba "
Yage wajan rubutun yayi yafita cikin bedroom d'in shi yakoma zama yayi bakin bed yadubi wannan rubutun sannan yadubi na Hanan qwafa yayi yamiqe afusace yafita

A 'bangaran Hamut kuwa jinshi yakeyi sakayau amma dukda haka zuciyar shi tacushe yakasa manta mafarkin jiya koyaya yarumtse ido Hanan yake gani kwanciya yayi saman bed idanunshi nakallon sama afili yace

" Ya Allah kayayemin son Hanan kamar yadda kayayemin wannan lalurar danacire rai da warkewa ya Allah kataimakeni "

Sauke ajiyar zuciya yayi yatashi zaune qoqarin danne zuciyar shi yakeyi amma tanasake yungurowa jin sallamar Hamidat yasashi tamke fuska sosai d'an kauda kanta tayi tace

" D dama Jakadiya ce tace Ammi nason ganinka "
Miqewa yayi batare dayacemata komiba yafita bin bayanshi tayi da kallo sakin shu'umin murmushi tayi tace

" hmmmm nasan shirinane yayi tasiri bade Hanan ba nasha alwashin takanta zansa kawahala "
Rurin dawayarta keyi yasata dakatawa da zancenta ganin number Muhseen yasata zaro ido waige waige tashigayi dukda tasan babu kowa cikin bedroom d'in amma sabida rashin gaskiya yasata dube dube d'agawa tayi cikin yatsina fuska tunkafin yayi magana ko sallama babu tace

" kai Muhssen ba d'azu nacemakaba nabar wannan layin mijina yasama lafiya yanzu dan haka babuni babu kai kajiko ? "
Wata irin dariya muhseen yasaki sannan yace
" ai wallahi baki'isaba hakan bazai ta'ba yiyiwaba wato ni zakirenama hankali ko ? kinsamu wani zakitureni badan mijinki zakibarniba sabida dama batun yanzu kike bin mazaba shima ahaka kikazomai ni nasan halinki batun yanzuba dan haka yazama dole kibini ko nafasa kwai kuma kisani idan wani abu yasamu wannan cikin to wallahi sena shafe rayuwarki yazama dole wannan d'an yajawomin dukiyar Hamut zuwa gareni dan haka inason ganinki ayau d'innan kizo inda kikasaba zuwa kisameni 2pm"

Baijira tace komiba yakashe wayar kwafa tayi cikin takaici tace " hmmmm wallahi baka'isa katonamin asiriba nasan yadda zanyi dakai "

Fita tayi daga bedroom d'in Hamut rai 'bace

Cikin matuqar razana Jakadiya tadubi Hajiya Mariya

" Hajiya wallahi inajin tsoro tayaya zan'iya zubama Hajiya kilishi wannan gubar idan akaganonifa ? "

Tsaki Hajiya Hajara tasaki tace " tokibari aganokid'in tundake shashasha ce idan kika aywatar da wannan aykin dede tofa million 5 zamubaki dan haka yanzu sekiza'ba million 5 ko Hajiya kilishi kuma somukeyi zargin yahaukan Hanan inanufin lalle yazama Hanan ce zatabama Hajiya kilishi abinci mai guba kinga idan akayi hakan babu mai zarginmu "

Dariya Jakadiya tasaki tace " ay Hajiya seyanzu naji sanyi million 5 zan'iyayin komi akanta keko Hanan akanki komi zaiqare nabarku lafiya " tafita cikin farinciki

Sallama Hamut yayi yashiga cikin parlour zaune Ammi take fuskarnan tata bayyane da murmushi qarasawa yayi yazauna cikin ladabi dubanshi tayi tace

" Hassan dama Siyama ce zaka d'akko daga airport yau zatadawo daga saudiyya a matsayin cikakkiyar likita "

Sosai ran Hamut ya'baci sabida basayin shiri da Siyama duban Ammi yayi kafin yayi magana Ammi tace

" nasani Hassan bakwa zama inuwa d'aya da Siyama itama nasan bazataji dad'in zuwanka d'akkotaba to amma hakanan zakuyi haquri umarninane yadda kake d'ah agareni itama haka r take 'yah sabida 'ya'yan yayana 'ya'yanane nahaqiqa tashi kaje Allah yayi maka albarka "

Miqewa Hamut yayi jiki babu qwari ranshi a'bace dede lokacin Hammat yashigo afusace ganinshi ahaka yasa Hamut rud'ewa cikin nuna kulawa Hamut yakama hannun shi sukazauna yace
Chapter 19 · 0% Book details