← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" kenan bazaki'iya zaman auranba sau 1 kawai amma kinaneman gazawa tokuma gashi ni nayima Ammi da bro na alqawarin cewa zansauke miki duk wani haqqi naki dake kaina kinga kenan kukanki dawata matsalarki duk batashafeniba inama lefina dazanjure shiga cikin gonar dawani yashare to yaya Hammat zaiyi umarnin iyaye kawai yabi amma badan son ranshiba kuma bazan ta'ba soba har abada sannan kisani bazan ta'ba yin shuka cikin wannan gonarba sabida baikamata Hammat yayi dashe cikin gonar dabashi yashareta ba kuma ba'ason ranshi yake bintaba ruwane kawai zetayin gudu acikinta amma babu tsirre koda wanda ba'aso dazefito acikin ta kishirya amsar haqqin ki zuwa anjima ina dawowa kuma kitabbatar kinci abinci sabida jijjigar yau seta ninka tajiya batare da jin tausayiba zan murgushe qaramar yarinya kamar yadda kaka ta'isheni dafad'a sekace nine nace a aura min qaramar yarinyar sekiyi shirin zama babbar mace sabida duk dahaka nifa kinyimin kad'an "

Daga haka yasakai yafita daga parlour sakin Spoon d'in hannunta Hanan tayi rawa kawai jikinta yakamayi cikin idanunta kuwa hawayene yafara tsiyaya bugun zuciyarta yaqaru sosai ga tsoro gakuma baqincikin maganganun da Hammat yake jifarta dasu

Mameen Zarah ce 🤝🏻👌🏻
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 43 & 44*

*T* ashi tsaye Hamut yayi daga bakin bed yashiga yin safa da marwa dede lokacin Hamidat tashigo dubanshi tayi tasaki murmushi nufar shi tayi tarungumeshi tabaya rumtse idon shi yayi take yaji wani irin mugun takaici cikin zuciyar shi juyowa yayi afusace yatureta daga cikin shi yabud'e baki zaiyi magana tari yasargeshi adede lokacin wanda yasa shi yazauna dole tsayin lokaci yanatafaman tari sannan yasamu yalafa duban Hamidat yayi da idanun shi wa'inda suka kad'a sukayi jah sabida wahalar tarin cikin dashewar murya yace

" Tabbas ayau nasake tabbatar da mugun butulcinki Hamidat kisani kincutar dani a rayuwa kuma Allah bazai barkiba ayanzu ke bakiqi nama mutuba kina kallona inayin wannan mugun tarin amma ko azzikin ruwan sha bansamu ba dukda nima bason hakan nikeyiba amma darajar igiyar aure tafi gaban wasa koda bazanshaba yakamata kibani kaice da wannan rayuwa taki Hamidat wallahi inada tabbacin inda Hanan ce matsayin mata agareni bazata ta'ba tsayawa tana kallona ina cikin wannan halinba nayi imanin sematafini shiga damuwa wayyo Allah nayi rashin wadda tadace da rayuwata amma nagode ma Allah dayasa d'an'uwana yakasance miji agareta bawani canba "

Wani shi'umin murmushi Hamidat tashigayi zama tayi agefanshi tadafa kafad'arshi tace

" ayya my D yakamata kadinga tuna cewa nifa balefina bane kaine kaja dakabani haqqina da haryanzu ina cikin tsananin soyayyar ka to amma hakan bazai ta'ba yiyiwaba sabida karigada kazama mace kaga kenan bakada amfani agareni har abada sannan inaso katuna wani abu duk irin son dakakeyima Hanan bazakata'ba samuntaba sabida Hammat yarigaka d'auketa kodama Hammat bai auri Hanan ba kai yaya zakayi da'ita ko kallonta zakadingayi kamar mirror hmmm Yaya Hamut daga yau kadena sakomin sunan Hanan acikin kunnuwana sabida natsaneta matuqa sabida wani babban dalili yaya Hamut duk wani alfahari dazakayi da Hanan bazakata'bayin alfahari da'ita wajan asaliba domin kuwa batadashi rigar naku asalin tasaka take yawo aciki bacin haka hmmm toda bolama setafita jaraj....... "

Wasu irin zafafan marika Hamut yashiga sauke ma Hamidat cikin mugun matsanancin fushi wa'inda sukakai kimanin 6 sabida zafin marukan har seda Hamidat tazibe qasa dukda hakan Hamut bairabu da'itaba yashiga shurinta daqafa ganin idan tatsayafa zai'iya nakasata yasa tasamu tamiqe da kyar tabar bedroom d'in biyota yayi cikin zafin rai ganin hakan yasata shigewa cikin bedroom dinta aguje tarufe qofar bugun qofar yashigayi yanafad'in

" kibud'e mana idan ke kincika marar kunya kiga idan asibiti baiyi baqoba shasha sha kawai ballagaza in sha Allah Hamidat sekinganni tsayayyen namiji kuma cikakke kafin kibar hannuna senasaka kinji ihun mace adaran angoncina na 2 ihu irin wanda ango yakesaka amaryar shi kamar irin angoncin d'an uwana Hammat "

Yaqarashe fad'ar hakan cikin kuka mecin zuciya zibewa yayi saman gyuwoyin shi yad'aga hannuwanshi sama yashiga cewa

" ya Allah gabawanka yanacikin tashin hankali da damuwa Allah ni mailefine agareka Allah natuba kayafemin Allah banayin baqin ciki sabida qaddarar wannan lalurar dakad'auramin sabida kaine kad'ai kasan dalilin d'auramin ita ya Allah kanaganin yadda wata takeyin isgili ga wannan hukuncin naka ya Allah ni Hassan ayau iname tawassuli dasunanen ka tsarkaka dawanda yafi girma daga cikin su Allah kayayemin wannan lalura ya Allah nayi tawassuli da biyayyar danikeyima iyayena da qaunar danikeyimusu Allah kayayemin wannan lalura Allah nayarda cewa babu abun bautawa dagaskiya se kai nakuma sheda cewa Annabi Muhammad bawankane kuma manzon kane ya Allah nayi imani cewa akwai ranar qarshe bayan mutuwa zakatashemu Allah kaine kasamar damu bayan babumu sannan kaine zakasake tasar damu bayan munkoma gareka nayarda cewa ni bazan iya amfanar dakaina komiba bakuma zan'iya samarma dakaina komiba se yadda kayi dani Allah kar kabarni dakaina dede da kittawar ido natuba gareka ya Allah astagfirullah astagfirullah astagfirullah "

Yana kaiwa nan yamiqe cikin sanyin jiki har yajuya yatsaya yace " Hamidat ayau inaji cikin zuciyata cewa Allah ya'amsa addu'ata koda bansamu lafiya ba nasamu wata ni'imar agun Allah sabida zuciyata tasamu sassaucin rad'ad'in datakeyi kinga kuwa wannan babbar ni'imace agareni " daga haka yajuya yakoma bedroom d'in shi seda yayi alwala yad'aura sallar nafila sannan yakwanta

A'bangaran Hanan kuwa kasacin abincin tayi iya ruwan tea kawai tahad'a tasha magungunanta sannan tashiga toilet tasake gasa jikinta tafito shafe jikinta da turarukan da Hajiya Fulani tabata tayi sannan tazura doguwar rigar bacci mai taushi da santsi sannan tahau saman bed amma zuciyarta cike take damatuqar tsoro babu jimawa da kwanciyar ta tajiyo shigowar shi mugun kamshin turaran nan nashi yadaki hancin ta rumtse ido tayi sabida yadda bugun zuciyarta yatsananta qarasowa yayi yadubeta yadda tawani dunqule waje d'aya a saman bed hannu yasaka yashafi sajan shi cikin dakakkiyar murya yace

" ke mekike nufi tashi zaune " sake d'aukar kyarma jikinta yayi cikin sanyin jiki tatashi zaune dubanta yayi sosai sannan yace

" banabuqatar wannan rigar tajikinki sabida wahala zatabani tarufemin wajan hutun nawa sosai koki canza kisaka 'yar qarama kokuma kicireta duka kizauna haka 2 minutes nabaki idan kika sa'ba lokaci hmmm basenace komiba kinsan sauran "

Cikin mutuwar jiki Hanan tasauka daga bed d'in hawaye taji suna sakkowa daga cikin idanunta hard'e hannuwanshi yayi saman girjin shi yana kallonta har tasauya kayan zuwa wata 'yar qaramar riga iya cinyoyinta samanta kuwa shara shara yake ahankali tafara takowa zuwa wajan bed d'in idanunshi suna kanta ko kiftasu bayayi se cizan lips d'in shi yakeyi qarasowa yayi bakin bed d'in cire doguwar rigar jikin shi yayi yazama dagashi se singlet da boksa saurin rumtse idon ta Hanan tayi hawa saman bed d'in yayi yajawota jikinshi matseta yayi sosai yana shaqar kamshin jikin ta kwantar da'ita yayi yarufamata faffad'an qirjinshi hannu yasaka yana shafar lips d'in ta kai bakinshi yayi dede kunnanta yace

" banason wannan rawar jikin tunda kinriga da kin iskantani to yaya zanyi gashi kuma Ammi tace dole senabaki duk wani haqqi naki to yaya zanyi dole hakan yazamemin badan raina yasoba zanbaki shawara kiyi qoqarin kamsar dani idan bahakaba koda gari yawaye bazan bud'e qofar part d'innan ba zan wuni akankine kuma babu maicemin maiyasa "

Wani siririn kuka Hanan tasaki cikin sanyin murya tace

" dan Allah yaya kayi haquri Allah bazan iyaba akwai ciwo jikina kabari nawarke daga lokacin nayimaka alqawarin cewa bakada shamaki da jikina koda zakakasance dani tsawan 24 hours bazan nuna gajiyawata ba dan Allah yaya idan kakusanceni yanzu zakacutar dani qilama na'iya mutuwa "

Sake kai bakinshi yayi cikin kunnanta yace " tosemai idan kincutu idan kuma mutuwa kikayi dede kenan kingama ni nahuta zan'iya yimiki abu 1 sabida bro na yace karna cutar dake badan hakaba babu maganar d'aga qafa aguna tundakin iskantani ay yazama dole kiji dani yanzu kiyi duk yadda zakiyi kigamsar dani idan kika kasa tofa babu ruwana zansakebin waccan hanyar dukda anyimata gyara nikam babu ruwana kinga dasafe se'akumayimata wani gyaran "

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Hanan tasauke tasake sakin kuka cikin kuka tace " Allah yaya bazan iya sanin meye yakamata nayiba bansan komiba dan Allah kayi haquri kabari nawarke zanjure komi naka "

Iska yahuramata cikin kunne wanda yasata jan numfashi maihad'e da shassheka wannan sautin sedayasaka Hammat jin yarrrr cikin jikin shi amma yayi saurin dakewa seseta muryar shi yayi yace

" bakisan komiba ko amma tayaya jikinki yasaba amsar irin wannan saqon ? lokacin dakikabama wani kanki waye yakoyar dake ? kodayake kince fayd'e ne akayimiki kinada hujjar hakan meye yasa bakifad'a an qwatar miki 'yancinkiba ? sede kizaunar da shasha sha kijerame duk wannan amma baniba "

Sake fashewa dakuka Hanan tayi sekuma tadake muryarta cikin dakewa tace

" sabida yayimin barazana da saka Ammi na cikin matsala kuma idan nasanar da Ammi sauran rayuwarta zataqarene cikin baqinciki shiyasa nagwammace nashanye baqincikin ni kad'e amma fa inaji ajikina komawaye d'an cikin masarautar nan ne kuma duk lokacin danaganeshi wallahi senajefashi cikin baqinciki kamar yadda yasakani senasakashi yin muguwar nadama a rayuwar shi "

Jan iska Hammat yayi yafesar daga bakinshi yace " wace madafa gareki tayin hakan sannan tayaya zakiganeshi idan kika ganshi kinga karkizomin da shashanci "

A wannan karon cikin raunin murya tayi magana tace

" Allah shine madafata kuma zan'iya ganeshi sabida yanada surar jiki maicike da izza kamar kai kuma maganar shi akwai kaushi zazzalumine bashida tausayi yayimin magana mai kaushi cikin kunnena kamar yadda kakeyi ayanzu sannan kuma kamshin turaran jikinshi sak irin naka yaya komanshi sak irin naka amma nasan yayana bazai iya cutar da qanwarshi irin wannan cutarwar mai muni ba sabida inada tabbacin cewa nasihar Ammi tanayin tasiri akanmu muduka kuma kullum maganarta akanmu shine muji tsoron Allah karmuyi zalinci muguji aykata sa'bo kuma nasan in sha Allah zamukiyaye dan Allah yaya kadena jifata da kalmar zina hakan yanasa inajin zafi adukkan jikina bama zuciyata ba kawai "
Chapter 17 · 0% Book details