← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 27

Sashe 16

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana qarashe fad'ar haka yafita daga bedroom d'in had'ida jan tsaki kuka Hanan tasaki cikin damuwa sosai wani irin zafi taji zuciyar ta nayi kuka ne yakwace mata sosai takeyin kuka cikin kuka tashiga cewa

" ya Allah kaine kad'e kasan dalilinka najefani cikin wannan muguwar qaddarar ya Allah kabani ikon cinyewa Allah kakawomin mafita cikin wannan masifar danike ciki " haka Hanan tadinga kuka gaciwo dake cinta aqasanta ga zazza'bi da ciwon kai

Baki d'auke da sallama Hajiya Fulani tashiga cikin part d'in Ammi zaune Ammi take tanayin waya da Ansar ganin shigowar Hajiya Fulani yasa Ammi yin sallama da Ansar gaida Ammi Hajiya Fulani tayi cikin girmamawa bayan sungaisa Hajiya Fulani tafarayin magana kamar haka

" Am Hajiya dama watamaganace takawoni dakuma wani karanbani danayi tabbas nayi matuqaryin farinciki da auran Hanan da Hammat kuma naji dad'i dayakasance suka kafa tarihi kamar yadda akeso acikin wannan masarautar to nide Hajiya nayiwani karanbani kuma ni gudummawace agareni ganin cewa Hammat zaitafi da Hanan can qasar dayake ayki yanzu shine nashiryama Hanan wani mihimmin abu sabida nalura cewa mijinta zaikasance cikin maza masu qarfin shi'awa dubada irin wahalar da Hanan tasha akaro nafarko kuma gata qaramar yarinya shiko babba agareta gashi Jarumi mecike da izza yanzune yake kan maytar mace shine nad'auki niyyar gyara Hanan takowane 'bangare kafin tafiyarsu kama daga ni'imar mace zuwa gyaran jikinta dawasu sinadarai namusamman tunda kinga bamusamu yin hakanba kafin aure sabida yadda auran yazo cikin lokaci kad'an dukda cewa Hajiya tayimata wasu abubuwan amma tanabuqatar wasu namusamman daga garemu Kodan Hanan tasamu cikakkiyar soyayya daga gun Hammat kowayasan yadda zuciyar shi takeda tsauri sosai idan bamuyi wani abuba tofa Hanan zatasha wuyar samun kanshi dukda cewa shine yace yanason auranta amma iname roqon afuwar ki idan nayi badede ba "

Murmushi Ammi tasaki tadubeta sosai tace

" Fulani ay wannan abundakike yunqurin yimin babbar gudummawace agareni tuni inayin wannan tunanin wasu abubuwane suke dakatar dani kinga de Hanan matsayin 'yah take guna shima Hussein haka kinga idan nice nace zanyi dole akwai kunya musamman kinga bazai yiyu naginga zaryar zuwa part d'insuba amatsayina na uwa agaresu kuma ni zuciyata batayarda da nadinga saka Jakadiya agaba ba wajan wasu mihimman lamurorina ba sabida kinsan yadda zamantakewar gidan masarauta yadda yake bakowabane abun yarda musamman ma Jakadiya sabida ita takowace zakuma ta'iyacin amanar kowa inagodiya agareki da wannan gudummawar taki agareni hakan yasaka nakuma tabbatarwa ke bakishiyabace Qanwace agareni "

Murmushi Fulani tayi tace " tabbas hakane Hajiya tuni hakan nad'auka amma ganin yadda bakishiga harkar kowa yasa nakejin shakkar shigemiki "

Murmushi Ammi tasakeyi kafin tace komi Hamut yashigo cikin part d'in cikin sanyin jiki sallamar tashima cikin sanyin murya sosai yayita ganin shi haka yasa Ammi jin matuqar damuwa gaidasu yayi sannan yashiga cikin bedroom d'in Ammi duban Ammi Fulani tayi tace " amma Hajiya tabbas akwai abunda yakedamun Hamut dukda de damashi mai sanyine to Amma gadamuwanan tabayyana cikin idon shi qarara " ajiyar zuciya Ammi tasauke tace

" qware kuwa nima nagahakan Fulani bari naje naji damuwarshi idan nacisa'ar yagayamin dan kinsan d'annaki akwai zurfin cikin tsiya " jinjina kai Fulani tayi tace " hakane kam toni bari naleqa 'yata amarya " murmushi Ammi tasake sakar mata sannan tanufi bedroom d'in tanashiga taqarasa cikin sauri sabida yadda takejin sautin kukan Hamut hadda shassheka da'alama yasha kukan tun kafin zuwanshi part d'in Ammi zama tayi bakin bed d'in tadafa kanshi dake duqe cikin tashin hankali tashiga cewa

" lafiya Hamut meke damunka haka haba Hamut bansan zuciyarka da rauni irin hakaba tanada juriyar abubuwa dadama masu girma tayaya wani lamarin zai sakata takarye kayi haquri Hamut in sha Allah komi yakusa zuwa qarshe zakasamu lafiya nankusa in sha Allah itakuma Hamidat Allah shine zai bayyana komi akullum addu'a niketayi akan haka kaji Hassan "

Kukanne yasakecin qarfinshi d'ago kanshi yayi yad'aura saman cinyar Ammi cikin kuka yace

" Ammi kibarni nayi kukan nan sosai najima inason kukanma yazo amma yaqizuwa Ammi se tsabar qaunar zuciya da qunci Ammi yaya zanyi natabbata ciwon zuciyane zaiyi ajalina Ammi ayanzu lamarin Hamidat yarage damuna sosai Ammi sede abubuwa 2 zasuyi sanadin ajalina Ammi nasan Allah shine yajarafceni da wannan lalurar nasan kuma in sha Allah zaiyayemin amma Ammi akwai wani ciwon dayakamani wanda nasan shi daga zuciyatane Ammi inasonta matuqar so bansan cewa tuni soyayyar ta tamamaye zuciyataba se yanzu data su'bucemin Ammi nashiga Uku Ammi zuciyata tanayin matuqar zafi kuma tanabugawa tamkar zatafashe "

Kukanne yaci qarfinshi yasake fashewa da kuka cikin gigita darashin fahimtar inda zancanshi yadosa Ammi tace

" haba Hassan daure kasanar dani wacece ita kuma tayaya kake tunanin cewa tasu'buce maka ? gayamin dawuri nikuma zansamar maka damafita in sha Allah " ajiyar zuciya yasauke maiqarfi yace " a a Ammi babu wata mafita tabbas tayi matuqar yin nesa dani nisan dabazata ta'ba dawowaba Ammi Hanan tayi nisha daga gareni dole mutuwa zanyi Ammi kiyimin alqawarin cewa har abada kobayan namutu Hammat bazaisan da wannan mugun lamarin ba " zaro ido Ammi tayi zuciyarta tashiga buqawa bugu matsananci takasacewa komi se bakinta dayashiga furta Innanillahi wa'inna ilehirraju'uuun

Marmyn Zarah ce 👌🏻🤝🏻
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 39 & 40*

*T* sayin lokaci Ammi takasacewa komi shiko shima Hamut yakasa denayin kuka zuwa can Ammi tasauke nannauyar ajiyar zuciya tashiga shafa kanshi cikin taushin murya sosai da sigar lallashi tashiga cewa

" Haqiqa Hassan zuciyar ka tasaka abu mai tsauri a cikinta wanda nikaina zatasaka nashiga cikin mugun tashin hankali inama kafin auran Hussein da Hanan kazomin da wannan zancen danakasance cikin farinciki sosai sabida alokacin zan'iya juya lamarin kasancewar shi Hussein bason Hanan yakeyiba biyayyace kawai yayimin Hassan inda kaine inada tabbacin cewa zakakulamin da Hanan fiye da yadda Hussein zai kulamin da'ita koda ace yanasonta zatasamu tausasawa da tausayawa da cikakkiyar kulawa da Soyayya amma kas alokacin danaso haka sekanunamin bakara'ayin Hanan kodan alokacin soyayyar Hamidat tarigada ta toshe maka komi nafahimta Hassan ayanzu babu abinda zan'iya yimaka sede addu'a akan Allah yayaye maka wannan masifar Hanan tarigada tazama mallakin Hussein kasani nasani ayanzu idan akwai rabo mai gaggawa to munasaka rai Hassan dan Allah kayi qoqarin cire wannan abun cikin ranka karkacutarmin da kanka bazan iya jure hakanba in sha Allah addu'a ta zatayi tasiri akanka kaima katayani kaji "

Ajiyar zuciya Hamut yasauke mai nauyi yad'ago idanunshi dasukayi jah sosai sabida kuka cikin rawar murya yace[
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 41 & 42*

*C* ikin idanunta nashi suka sauka hakan yasata saurin duqar dakanta sabida yadda yayi mata gwarjini sosai zuciyar ta taji tanabugawa cikin sauri d'anjim nawani lokaci sannan Hammat yaja wani irin mugun tsaki yashige ciki bin bayanshi da kallo Hanan tayi har yashige cikin bedroom sauke ajiyar zuciya tayi sannan itama tanufi nata bedroom d'in kimanin awa 1 tajiyo wani kamshin turare wanda yasaka zuciyarta cikin muguwar kad'uwa

" wannan irin kamshi bazan ta'ba mantawa dashiba har qarshen rayuwata ina yaya Hammat yasamu irin wannan kamshin wanda yazamo mugun kamshi aguna ? "

Cikin zuciyarta take fad'in haka jin dakakkiyar muryarshi yasata saurin d'agowa tadubeshi cikin tsarin murya yace

" ke hakadama akekula da miji bakisan yaya cikin shi yakeba yaci ko baiciba hmmmm matsalar auran qaramar yarinya kenan dallah tashi ki had'amin abinci "

Cikin rawar jiki tamiqe tafita zuwa babban parlour binta yayi da kallo yadda take tafiya ahankali tana d'ingisa qafa wani irin shu'umin murmushi yasaki irin namugunta wanda shi kad'e yasan ma'anar shi tsayawa Hanan tayi wajan dining duban jerin kalolin abincin da'aka jera tashigayi ajiyar zuciya tasauke cikin zuciyarta tace

" ikon namiji akan mace made dabanne nasan yagani zamafa kawai zaiyi yaci amma seyasaka nad'auka nakaimai zuwa can amma hakanma qarin wata ladarne "

Had'a mai tashigayi cikin natsuwa kitchen tashiga tad'akko babban tire mai kyau da tsari tadawo parlour jeramai komi tayi sannan tad'auka wajan tafiya kuwa cikin cije lips d'inta takeyi sabida yadda takejin zafi idan tanad'aga qafa cikin sanyin murya tayi sallama yana zaune a qaramin parlour nata hannunshi riqe da waya yana latsawa aje tiran tayi agabanshi sannan tashiga had'amishi wanda zaici bayan tagama tace " yaya ga abincin nan " tamiqe zatanufi cikin bedroom yadakatar da'ita dafad'in

" mai kike nufi ? kina nufin nida kaina zanci aykin meye hannunki yakeyi sekace ba aure nayiba ? "

Jin haka yasata jin wani yanayi cikin zuciyarta tace " toni tayaya zanfarayin haka gaskiya hakan zaiyimin nauyi " tsawa yadaka mata had'ida fad'in " bakiji abinda nace bane ? " ganin yadda yafusata yasata dole tazauna gefanshi cikin shakkarshi tashiga bashi abincin cikin yanga yake amsar abincin sekace wani yaro itako cikin takatsantsan takebashi sabida tanajin tsoron kar tayi lefi tsayin lokaci sannan yadakatar da'ita duban fuskarta yayi sosai yace

" duk wannan kalliyar dakikayi tawaye ko saurayin nakine yace kiturame pic d'inki ? " sosai maganar tadaki zuciyar Hanan amma setayi qoqarin dakewa tace " a a nibana da wanda zanyima hakan se kai " cije lips dinshi naqasa yayi yad'an nisa sannan yace " kenan kinwarke kinshirya daukar ninkin darasin jiya ko ? "

Jin haka yasa Hanan razana har batasan sanda kuka yazomataba tace " a a Yaya Allah bazan iyaba jikina akwai ciwo sosai dan Allah kayi haquri " miqewa yayi yasake dubanta yace
Chapter 16 · 0% Book details