← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 22

Sashe 22

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Su ko su Jummai, sai suka shiga cewa don yaga tana da ciki shi yasa
arara ya ke nuna tafi kowa kuma ko gaban wane ne.

Don haka kowacce ta tsaya
acin ran ba ya sonta, ta shiga fushi, tare da shiga fa
i tashin neman asiri.

Hakan da suka yi na yin watsi da shi ya bashi damar more amarcin shi da A'isha, wanda bai yi a baya ba.

Duk ran girkin ta ya kan makara Ofis kuma ya dawo da wuri.

In ya kalli madubi sai ya ce Beby kin sani na yi
yau fa,ko ba ki lura ba ne?

Sai ta ce ai kai Uncle kullum mai
yau ne, komai naka yana da
yau.

Ya ce har da
ar Bebyna?

Ta ce ai ni ba'a saka ni cikin jerin masu
yau, ya ce inji wa?

Kina kallon madubi kuwa?

Ai Beby har yau ni ban ga me
yanki ba, cikin haka suka soma jarabawa, dole ta zauna a
akinsu na cikin makaranta saboda suna karatu ita da su Samira,su Samira sun dame ta wai wane irin ciwo ne wannan da ya sakata yin shegen
yau haka?

Ga wasu (hips) da ta yi,
irji kuma ya
ara cika ta ce zaman gida ne kawai,ai ba za'a ha
a zaman gida da makaranta ba,sai dai cikin ranta ta saka duk ranar da suka yi ban
wana zata sanar da su cewa ita matar Uncle ce, haka suka ci gaba da jarabawa har suka gama.

Ranar da aka yaye su,sun yi hotuna tare da canja lambobin waya,su da
an ajinsu, lokacin da za su rabu, Uncle ya zo tafiya da ita.

Samira Suka ce in za ta yi aure ta fa
i musu,sai ta ce musu sai dai in zata haihu.

Ta gaya musu cewa dama ta
auki al
awarin yau zata sanar da su cewa Uncle mijinta ne.

Dukkansu baki suka saki cike da mamaki.

Ta ce musu yanzun haka ma ina
auke da ciki wata uku, zan sanar da ku in na haihu,ku kuma ina jiran bikinku don Allah da zarar ya zo in sani,nan suka yi ban
wana suna kewar juna.

Ta dawo gida suka ci gaba da zama da mijinta lafiya.

Uncle na kula da ita sosai, sannan ba ta damuwa da lamarin su Hajiya Jummai, musamman da suka ha
e kai da Hadiza.

Sun ha
a kansu, sai su zauna falo suna zuba mata habaici tare da su Suwaiba, musamman ranar da ya kasance ita ce da girki,nan fa za su yi ta surutunsu na cewa salon banza ana yi wa miji girki alhalin ga mai girki sai wannan ta ce ba dole ba ke ko abar wani ya yi ana son a zuba asirin mallaka duk da dai ba ta kula su kuma bata ta
a gaya mishi ba, cikin wannan halin ne wata ranar Litinin yana
akinta misalin
arfe
aya da rabi, haka kawai ya bar komai ya zo wai ya ganta da yaronshi, tana
wance kanta na kan cinyarshi, ya shafi cikin ta ya ce, Beby naga cikin ya
i ya yi girma ya fito ki dinga tafiya da
yar da
yar,na
osa in ga lokacin.

Ta ce Uncle to cikin
wata-
wata watan shi uku fa, ya
aga rigarta mararta a shafe tamkar ba ta da komai, ya ce ni dai wannan cikin naki wane iri ne?

Bai
ara komai ba Beby?

Kafin ta ba shi amsa sai ga Hajiya Jummai ta banko
ofa babu ko sallama, ta ce ashe gaske ne,dama an ce kana zuwa kana cin amanar mu, tunda ai naga yau ba ita ce da kai ba, kuma yanzun ba lokacin dawowarka ba ne ka sato jiki ka dawo.

Kallonta kawai yake yi sai da ta kai aya sannan ya dube ta ya ce,haba Jummai,me zai sa ki tsaya kina zubar da girmanki a gurin wannan
ar yarinyar,ya kamata ace yanda take baki girmanki ki ri
e shi ni a zatona kece mace ta farko da za ki kula min da A'isha,da halin da take ciki,in na tuna yanda a baya ki ka fi ni son ki ga na samu
a, sai naga akasin haka, maimakon haka ma sai ki ka yi watsi dani da lamarina, kuma ki ka nuna tamkar kina fa
a da Ubangijinki, saboda ya bani
yauta, shawarar da zan baki,ki sake hali ki rabu da mugayen
awaye za su kai ki su baro.

Ta soma kuka,ai ni yanzu komai ya zo bakin ka gaya min zakayi tunda mahaifata ba zata iya
aukar cikinka ba.

A'isha ta ce, to kiyi ha
uri Hajiya, Uncle ka koma Ofis shi kenan.

Jummai ta daka mata tsawa ke makira, yi min shiru ba ke ce sanadin canza min halin miji ba,an je makaranta an roro ciki an zo an manna mishi, shi kuma da yake yana neman haihuwa ido rufe ya amsa jiki na
ari,in da ka iya cikin me zai hana Hadiza kai mata in ni ba zan haihu ba.....ya katse ta da tsawa mai tsanani.

Jummai kina hauka ne?

Wace magana ki ke yi haka?

Ya kama hannun A'isha wannan yarinyar
aramar yarinya ta fi min duka manyan matan da na aura, wannan yarinyar ita ce mace mai daraja ta farko a idanuna ni nan nine na yi mata ciki tunda kin tono bari in sanar da ke.

A ranar da na kauda budurcinta a ranar cikina ya shiga jikinta, dan haka ki kama bakinki Jummai.

Ta fita tana masifar cewa eh dole ka ce kai,ni dai ban yafe satar min
wana da ake yi ba.

A'isha tana zaune ta zabga tagumi mamaki take yi wannan kuma wanne irin sharri ne?

Hawaye suna zubowa daga idanunta,ya zo yana bata baki ta ce ka tafi Uncle ba komai.

Ya ce, Beby ki zama mai ha
uri, ina nufin ki
ara kan naki, ta share hawayenta tana murmushi ka koma Ofis Uncle, ya dinga bata ha
uri har sai da ta tabbatar mishi da cewa ita fa hayaniyar da suka yi ne wato sa'in'sar da suka yi ne yasa ta hawaye, nan ya fita yana shi mata albarka, A'isha ko ta maida
ofa ta rufe.

Bayan sallar la'asar Wani bacci A'isha ta ringa ji,ta
wanciya saboda ta san cewa baccin la'asar ba shi da
yau,ko a musulunce, ta zauna tana kallo wai don kada baccin ya
auke ta.

Da yake an ce gwanin sata ne baccin, sai ko ya sace ta har ma bata san lokacin da ta
wanta ba.

Can cikin baccin sai take jin numfashinta yana yin sama, ta soma kokowa da numfashinta, bu
e idanunta ke da wuya sai taga haya
i ta kowanne bangon
akin,nan ta shiga salati da
arfi tare da ihu, amma muryarta ba ta fita.

Nan fa haya
in ya cika
aki, ya toshe mata numfashi.

Biyar dai-dai Uncle ya shigo gidan, ya nufi
akin Beby domin zuciyarshi ta kasa nutsuwa,yana shiga ya same ta kan gado tana ta mutsu-mutsu, numfashinta yana wuya ko sauka
irjinta ba ya yi, bakinta na ta motsi.

Amma ba a jin me take cewa, sannan shi bai ga haya
in ba, ya
auke ta yana jijjiga ta,yana cewa Beby!

Beby!!

Ai ina ta daina ma motsin ta yi lagaf
asan zaninta kuma wata laima ya ji mai
umi,tana sauka a hannunshi, da sauri ya duba kun san me ya gani?

Jini.

Da
arfi ya furta jini?.

Tabbas jini ne, sai mun ha
u cikin kashi na uku don jin shin cikin da ake nema shekara da shekaru a ka sha wuya kanshi,ya zube?

Asirin Hajiya Jummai zai tonu?

Da sauran wasu abubuwan.

Daga taku har kullum Halima K/Mashi.

Na gode
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
Ummi Tandama
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Default Paragraph Font
Table Normal
No List
Times New Roman
Times New Roman
Symbol
Symbol
Arial
Arial
Calibri
Calibri
SimSun
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
42b0547611b642d6a74b2996f6b53622
Chapter 22 · 0% Book details