← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafisa ta lura da hakan da suka yi don ta gani,don haka sai ta tsargu da wannan girkin,don haka sai ta ce to bari Uncle
in yazo ya kira Likitan don ya ce duk abinda ta ce zata ci sai yazo tukunna.
#######
[12/16, 08:36] Ummi Tandama
Page 14*
Hajiya Lanti ta ce,ke rabu da su, wa
annan likitocin masu tsirfar tsiya,ba ni plate nan ki gani in bata.

Nafisa ta ce,ki dai yi ha
uri mu bi dokarsu kada ta ci ta kuma yin aman su ce sun fa
a mun
i ji.

Hadiza ta ce, haka ne kuma a bari
in.

Tana magana tana ta
a Hajiyar alamun ta bari.

Uncle
in ne ya yi sallama ya shigo da sauri Hajiya Lanti ta ja baya tana fa
in sannu da shigowa Alhaji, ya amsa da cewa yauwa sannu da zuwa.

Suka gaisa har tana dur
usawa.

Ta ce,ya ya me jiki?

To Allah ya inganta mana yasa a sauka lafiya, ya ce Amin nagode.

Hadiza ma cike da fara'a ta gaishe shi, tare da yi mishi murna.

Ta
ara da cewa, insha Allahu
an biyu zata haifa,sai a bata
aya.

Ya ce, Allah ya bi bakinki Hadiza.

Hajiya Lanti tana dariya tana cewa,kai wa
annan yara.

Ita dai A'isha tana
wance tana jin su.

Ya matso kusa da gadon ya du
a ya ce "Sannu Beby" a hankali ta ce,zan ci naman da su Hadiza suka kawo,da hanzari ya ce Nafisa zuba mata,me su Hadiza suka zo dashi?

Wai zata ci.

Nafisa ta ce, sai in Likitan ya zo,
azun ya ce kada ta kuma cin wani abu sai in yazo.

Hajiya Lanti ta ce,ni dai na ce da kun bata,ba lallai ne tayi aman ba.

Nafisa ta ce bari dai in kira Likitan.

Uncle
in ya tashi, bari in kirashi ta ce zauna kawai Bros,bari na kirashi,ta fita.

Ko da ta samu Likitan cikin Office
in shi, suka gaisa ta ce mishi,ta zo ne don Allah ya yi ma yayansu magana ba kowa ba ne zai kawo abinci ta ringa ci, saboda yanda ya da
e babu haihuwa, wasu za su yi ba
in ciki,da samun cikin musamman kishiyoyinta,don haka ya zo yanzun ma an kawo wani nama wai zata ci, kuma ita bata yarda da naman ba,don haka tana son ya hana ta ci.

Da hanzari Likitan ya mi
e tare da cewa, Madam nima nayi wannan tunanin,ba zan so wata matsala ta faru ba,na gode da wannan taimakon da ki kai min."
Likitan ya shigo suka gaisa da Uncle
in,ta hanyar ri
e hannu.

Ya ce,ka ce inzo?

Uncle ya ce eh, wani nama ne aka kawo shine take son ci.

Likitan ya ce, "Yalla
ai ba zata ci komai ba yanzun ba sai zuwa da safe, saboda wannan ruwan da muke
ara mata yana tare da abinci,ba ma bu
atar ta ci komai yanzui."
Fuskar su Hajiya Lanti Nafisa ta kalla, sai ko taga sun kalli juna da
acin rai.

Likitan ya fita tare da cewa,in ka fito ina Ofis,ya ce to Doctor nagode."
Hajiya Lanti ta ce, to ni zan tafi ke zaki jira mijinki ne?

Ta ce , to.

Tana dubanshi ya ce to jira sai muje
in.

Hajiya Lanti ta ce to bani cooler in tafi da ita mu ma ci can ko?

Hadiza ta ce to ko Nafisa tana so?

Nafisa ta ce a'a nagode." Ta
auki kular,wai bari ta rakata ta hau mota.

Nafisa ta ce , to.

Suna fita shima ya nufi gurin Likita, Nafisa ta koma kusa da A'isha ta ce,ke wace irin wawiya ce zaki ce za ki ci?

So kike
an cikin muna murna kisa ayi watsi dashi?

Baki san su Lanti ba ko?

Kar su kuma kawo wani abu ki ce za kici kin ji ko?

Ta ce,to.

Shima Uncle
in naki yasan komai don dai su maza ba su cika
aukan irin wa
annan abubuwan da mahimmanci ba ne, likita ya ce baya son kowa ya kawo abu ace ki ci, ya yi taka tsantsan, duk abinda tace tana so ta ci to ya kasance shi ne zai sa wa
anda zuciyarshi ta yarda da su su dafa mata.

Uncle ya ce shikenan.

Likitan ya ce ko gidan mahaifiyarka kawai ya fi dacewa a dinga kawo mata duk me zata ci,ya ce
warai kuwa na gode insha Allah zan kiyaye.

Hadiza kuwa suna tattaunawa da mahaifiyarta kan cewa, duk wannan Nafisar ce ta
ata musu shiri, Hajiya Lanti ta ce,ni ba wannan ne matsalata ba, damuwa ta ku
in da na kashe gurin amso wannan maganin.

Kai ina ma wannan cikin jikinki yake,kinga tun cikin asibitin nan sai mun
washi ku
i.

Hadiza ta ce,ke dai bari, Hajiya yanzun ya ya zamu yi da wannan abin?

Lanti ta ce wa?

Ai tunda ranta na so sai ta ci shi, gobe zan
ima tunda yau ne aka ce kada ta ci saboda ana mata
arin ruwa, gobe da sassafe in zaki taho ki biyo ki amsa.

Ki zo mata dashi,sai ki ce wani ne ki kayi.

Ta ce, to shi yasa ai na ce su bari na tafi da shi tunda ba zasu ci, tunda ba nice nazo dashi ba,na su zaton ke ce ki ka dafa.

Haka ne inji Hadiza, zan biyo, suka yi sallama,ta dawo Hajiya Lanti kuma ta hau mota.
**** *****. ****
Goma dai-dai Uncle ya kula Nafisa tana hamma, A'isha tuni ta yi bacci,don haka ya mi
e ya je bakin A'isha ya tsugunna ya sumbaci kumatunta, sannan ya zo gurin Nafisa ya ce "Sister tashi ki je ki
wanta kema sai da safe." Hadiza ma tayi musu sai da safe, sannan suka fita.

A cikin mota take ce mishi "Darling amma ran A'isha ya biya da naman nan ko in yo mata wani gobe tunda tana so?

Gashi ance mace mai ciki in ta bu
aci abu a bata in dai da shi kada ta haifi
anta da tabo." Ya yi
an murmushi, "inji hadisin hausawa ko?" Hadiza ta ce, "Allah gaske ne." Ya ce,to ki kawo mata, amma fa ba lallai ba ne ta ci tunda Likitan bai ce da safe zata ci wani abu,kai ko dai ki barshi kawai ma." Hadiza ta ce, a'a zan mata ko bata ci ba na san mutanan gurin za su ci, ya ce shikenan.

Ranar
wana Uncle ya yi yana sallah, ya kasa bacci.

Washegari tunda Asubahi ya kira Abbanta.

Bayan sun gaisa, Abba ya tambaya ko lafiya?

Uncle ya ce, A'isha ce bata jin da
i ba, tana asibiti.

Abba ya ce, "assha gado aka bata kenan?" Uncle ya ce wallahi, amma da sau
i ba sai kun zo ba.

Sannan ka taya ni addu'ar Allah ya sauke ta lafiya.

Abba ya ce,ashe?

Lallai nayi murna Friend, Allah ya bamu masu albarka.

Uncle ya ce Amin.

Daga nan ya nufi asibitin don yaga yanda suka
wana.

Zaune ya same ta tana sallah, gaskiya yaji da
i sosai,ya zauna har ta idar ta juyo ta dube shi, ina
wana Uncle?

Ya ce lafiya lau Beby ya ya jiki?

Ta sunkuyar da kai ta ce,da sau
i.

Ya ce ina Nafisa?

Ta ce ta shiga wanka.

Ya ce,to da
yau,kema kin yi ne?

Ta ce eh, nayi shi ne na ji
arfi.

Ya ce su Abba suna gaishe ki,ta ce gaya musu ka yi bani da lafiya?

Ya ce eh mana, har ma nace musu kina da ciki." Ta saka kanta a gwiwarta tare da fa
in haba dai don Allah.

Ya ce to mene ne?

Ta ce,ni ina jin kunya yanzun su Hajiyarmu sun ji?

Ya yi murmushi.

"Sun ji mana,tun lokacin da Likitan ya sanar damu."
Ta ce, "Shi kenan ba zan kuma zuwa gidan ba" ya ce "Don me?" Ta dube shi, yanzun kowa ya san abinda na yi na samu cikin kuma?

Ya yi dariya, sannan ya ce, a'a ba wanda zai sani,ke da ki ke makaranta, wasu za su ce a ruwa ki ka sha." Ta
an yi murmushi don ganin ya maida ita doluwa,ta ce "Ai na san ba'a sha a ruwa." Yasa dariya.

Nafisa ta shigo tana cewa "Bros ka zo kenan?" Ya ce, "wallahi ya ya kuka kwana?" Ina ta tunanin dare?

Nafisa ta ce bacci sosai mu ka yi kaga gashi har ta yi wanka,ta yi sallah.

Ya ce aiko naga da sau
i yanzun me zaku ci inje gidan Hajiyarmu in sa ayo muku?

Nafisa ta ce,Mama two me zamu ci?

Ta
ata rai Anty Nafisa bana so, Uncle ka ce ta bari fa, cikin murmushi ya ce , Sister bama so gaskiya, ya dubi A'isha
yale ta Beby gaya min me zaki ci?

Ta ce,da zan samu waina ko irin
an waken nan?

Ya ce zaki samu ya mi
e, har ya fita.

Ya dawo zaki ci farfesun irin na jiyan a zo miki da shi?

Ta ce a'a, ya ce shi kenan.

Hadiza ta zo lokacin suna karyawa.

Hadiza ta aje mata kular a gaba gashi kin ji
ar'uwa na yi miki wani ne.

A'isha ta ce na gode, yanzun kam na
oshi amma anjima zan ci.

Ta mi
a ma Nafisa ta ce Anty Nafisa gashi ki sa can gefe kada ku ci min fa.

Nafisa ta ce, to A'isha Hadiza kam da
i ne ya rufe ta.

Hajiya Jummai kam an bazama nema,an nemo kuma an samo,ana kan aiwatar wa.

Satin A'isha
aya a asibiti, ta samu sau
in aman.

Sai dai kasala tare da tsirfa iri-iri har yau abinci in ba daga gidan Hajiyarmu ba ne bata ci.

Hajiyarmu kuwa ko yaushe mai aikin ta tana kicin tana dafa duk abinda A'isha ta bu
ata, sannan addu'o'i ko yaushe tana nan tana tofa mata su cikin ruwa tana sha.

In za'a kawo abinci sai an kawo, shi kam Uncle shi ne mai jinya, duk wadda yake
akinta zai je ya bata ha
inta in ya kintsa jikinshi zai dawo gurin A'isha.
Chapter 19 · 0% Book details