← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi matuƙar ƙyau cikin shadda mai tsada kalar ja mai duhu,hular da takalman duk kalar jan ne,ƙamshin daddaɗan turarenshi ya cika falon. Duk da tsoronshin da take ji bai hana zuciyarta yaba ƙyanshi ba. Ta dire tire kan tebur ɗin, gabanshi ta jawo teburin sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce sannu da zuwa Uncle, ya ce "yauwa ƴar Bebyn Uncle,I hope kina lafiya?" Ta ce "lafiya lau,ya ya su Nafisa da su Hajiya?" "Duk suna gaishe ki, cikin jin daɗi yake bata amsa, domin yarinyar ta shiga ranshi har yana mamakin yanda wasu lokutan ya kan shagala da tunaninta,ya kan ji kewar ƴar siririyar muryarta, da Beby face ɗin ta, abinda bai taɓa yi kenan a kan mace ba, duk matan da ya aura baita jinsu kamar yanda yake jin A'isha ba,a ranshi. Ta cika kofi da ruwan zoɓo mai sanyi ta miƙa mishi cike da ladabi, ta koma gefe ta zauna, ya ce "No, come on hau kujera ki zauna,ta ce nan ya yi Uncle, ya ce to nima bari na sakko ƙasan, ta yi sauri ta hau kan kujerar ta ɗan ɗofanu yana ƴar dariya shima ya gyara zaman shi.

Sannan ya soma shan zoɓon ta gefen idanunta ta ke kallonshi. A ranta ta ce "Oh,ga mutum har mutum, amma cikin zuciyarshi gara kura da shi. Ya katse shirun da cewa "Beby in Allah ya gwada mana ki ka koma gidana, ina son kina min wannan zoɓon kin ji?" Ta ɗaga kai alamar ta ji ya ce "to abincin fa zo ki zuba min," ta ce to, tana buɗe kular farko yaga saƙwara fara ƙar-ƙar, ya ce "ai shikenan Beby yau kuwa har in tafi ita zan ta ci.

Nan ta zuba mishi da miyar agushi, ga nama manya-manya,ya cika cikinsa dam,ko magana ba ya iya yi, sai da ya gama sannan ya dube ta yana goge fuska da fari ƙar ɗin handkachief ya ce, Beby kin ganni babu ba ka sai kunne ko? Ta sunkuyar da kai.

Ya ce,"Beby sai naga kamar kin rame min a ido hakane?" Ta ce na ɗan yi mura bayan haka kuma ga makaranta," ya ce "kin manta ɗayar ga kuma maganar aure". Ta rufe fuska, ya yi ƴar dariya sannan ya ce zan sa su kawo kaya da zarar na koma gida nan da sati biyu zuwa uku,kin zama ƴar mutanen K.T? ko?" zancan ya daki zuciyarta, nan take ta raya ma ranta haka yana nuna nan da sati huɗu zuwa biyar zata baƙunci kabarinta, tunda an ce matan nashi ba sa wuce sati biyu zuwa uku suke mutuwa.

Ya katse ta. "Ko ya yi nisa a rage?" Da sauri ta girgiza kai,ya ce "a barshi haka?" Ta ɗaga kai alamar Eh. Nan ya ciro mata tsarabar ta, abubuwan ci ne tare da turaruka har da wata ƴar Tedi ta wasan yara. Ya miƙa mata ledojin ya ce "to duk da kin ce baki son tsaraba gashi nan ki basu Jafar ke kuma ga naki" ya miƙa mata Tedi.

Baki ta saki tana kallonshi, shima ita yake kallo tamkar masu kallon soyayya, sannan cikin sanyin murya ta ce "Uncle me zan yi da wannan?" Ya ce "wasa mana" ta ce, "am not a small girl," ya ce haba? Ta sunkuyar da kai tace,da gaske,ya ce shikenan to ki ajiye min in kin haifa mana Small boy sai ki na bashi yana wasa," ga mamakin shi sai ya ji tace "in kuma na mutu fa?"

Da sauri ya dube ta,a ranshi ya soma zargin ko taji cewa matanshi suna mutuwa ne? Amma a fili sai ya ce,"nima ina yawan tuna haka, sai dai duk sanda na tuna cewa zan iya mutuwa ko ke ki mutu ban ga ɗan kaina ba, ina shiga wani mawuyacin hali, zuciyata tana sonki da yawa." Ta sunkuyar da kanta ƙasa,ko dai mummunan zato ne a ke mishi? Ko dai zargi ne? Ƙwanan matan nasa ne suke ta ƙarewa? Ya katse mata tunani da cewa, "ki na tsoron mutuwa ne? Ko kina zaton in kin aureni zaki mutu ne?".

Cikin dabara ya sako mata tambayar,don yana son ji ko ta samu labarin matanshi suna mutuwa ne? Nan take ta gane nufinshi,don haka sai ta ce "a'a bana tsoron mutuwa,sai dai kullum tunanina yana kan ayar da ke sanar damu (kulli nafsin za'ikatul mauti), kaga dukkan Musulmi yana da ƙyau ya dinga tunawa ranshi zata ɗanɗani mutuwa, sannan in ajali ya yi kira ko ince in ajali ya zo ba za'a ƙara ma mutum ko second ba.

Alhaji Saddiƙ ya dube ta cike da farin ciki,ya ce haka ne Beby, lallai kina da kaifin basira. Haka nan duk bawan da yake yawaita tunanin mutuwa zata iya riskarshi a kowane lokaci,za ki sameshi yana mai matuƙar kiyaye dokokin Ubangijinshi, ina saka rai kema kina ciki? Ta sunkuyar da kai tare da faɗin insha Allah ya ce, to ba zaki taɓe ba.

Sannan ya canza zancen da cewa,me kike shiryawa bikin? Ina nufin waɗanne shagulgula za kiyi ke da ƙawayanki? Saboda in na tafi ba zan dawo ba, sai ɗaurin aure, shiyasa nake son in sallame ki."

Ta dube shi,a ranta ta ce, inyi shagalin me? Bayan ni ƴan ƙwanaki ne suka rage min,a fili kuwa sai ta ce, "ba zan yi komai ba." Ya ce, "Haba! Ko walima?" Ta girgiza kai tare da ƙoƙarin maida ƙwallar da ke son zubo mata. Ta ɗan saka hannu ta ja hancinta kamar tana mura, sannan ta ƙago murmushi ta ce "kasan Uncle bani da ƙawaye bayan haka ma ni ban cika son hayaniya ba,so kaga gara na barshi ko?" Ta faɗa tare da duban shi,ya ce "shikenan Bebyna" ya saka hannu cikin aljihun ya ciro rafar ƴan ɗari biyar guda biyu dubu ɗari kenan,"gashi gudunmawata," zatayi magana ya tare ta da cewa, "kul ki kakiyi magana, ke dai ce ne Allah ya cika mana burinmu,a ranta ta ce Amin in ba shanye mini jinina ba ne. Ya ce zaki shiga gida ko? Da sauri ta ce,eh tare da kallonshi ya yi ɗan murmushi sannan ya ce, "kin ƙosa ki tafi ko?" Ta sunkuyar da kai tare da girgiza kan alamar a'a, ya ce "to ga kayanki nan ƙwashe. Ta miƙe tare da ƙwashe kayan ta ce mun gode. Ya ce,ba ki ɗauki Tedi ɗin Small beby ɗin tamu ba,ta kalli Tedin sannan ta ɗauka ya ce in Abbanki ya shigo sai ki ce ina jira, sannan ki bar wayarki a kunne kin ji? To tace,ta fita.

A gadon Ummanta ta zube kayan tare da zama gefen gadon ta rafsa tagumi. Umma ta fito daga (toilet) ta tsaya tana kallon kayan da iyayen kuɗin da ke zube a kan gadonta, ta ce "A'isha waɗannan kayan fa?" Ta ce "Uncle ne ya ce in kawo ma su Jafar?" Ta ce, "wannan kuɗin fa?" Me yasa ki ka amsar masa kuɗi?" Ta ce "Umma nayi-nayi ya bar su yaƙi wai cewa ya yi gudunmawa ya bani don na ce mishi ni ba zan yi shagalin biki ba.

Umma ta ce duk da haka da dai baki amso ba, A'isha ta dubi Ummanta ta ce, "ki aje a gurinki ni sai in dinga ganin tamkar yana biyan kuɗin jinina ne da zasu sha....." Ke! Tsawa Umma ta daka mata, sannan ta ce "A'isha bana son jin irin waɗannan surutan daga bakinki kenan kema kin yarda da mummunan zargin da al'umma suke ma mutumin da zai zama mijinki? Duk kin bi kin ɗaga hankalinki, maimakon ki tsaya kan addu'a Allah yasa ki shiga gidanki cikin Sa'a ko? Ta miƙe ranta ɓace ta fita falo ta bar ta ɗauke da tagumi tana nazarin yanda ma za'ayi ta iya ƙwantar da hankalinta.

"Sofy! Sofy," Hajiya Jummai ce ke ƙwala ma ɗaya daga cikin ƴammatan da take ɗaukowa cikin danginta kira. Sofy ta zo cike da yatsina, ta ce "gani Anty Jummai," ta ce suby fa? Sofy ta yi wani luu da idanu, sannan ta ce tana bedroom in kirata ne?" Jummai ta ce, "eh kirata aikenku zan yi yanzun ku fito cikin shiri." Suka fito cikin riga da wando ya ɗame kowacce cikinsu, Sofy ce ma ta ɗan yafa wani ɗan kucilin gyale, Jummai ta dube su kun yi ƙyau, sai dai kema Suby je ki yana ko ɗan irin na Sofy ɗin kin san Alaramma yana gari. Haka take kiran Alhaji Saddiƙ in zata yi wani abu daya hane ta. Ko in ya yi mata nasiha, to ranar yini zata yi tana ce mishi Alaramma,ko Alagafarta. Soby taje ta ɗauko tana mitar ita bata son wani yafe-yafen gyale duk takura ne, Jummai ta ce "ya ya zakiyi tunda kina gidan Ustazai,ka ce shi yafi kowa sanin Allah" ta ce "ga wannan ta miƙa musu wani ƙullin abu cikin tsumma,ku kai ma Hajiya Kari,ku ce mata ga ƙasar ƙafar nan za kuma mu yi waya.

Sofy ta ce, "motar wa zamu ɗauka tunda ta mu tana gurin gyara?" Hajiya Jummai ta soma masifa, "ku hau mashin ba zan ba ku motata ba,ku je ku buga min ku ja min asara." Suby ta ja tsaki tayi gaba tare da cewa, "Sofy ta baki kuɗin mashin ɗin, amma ai ba mutuncinmu bane hawa acaɓa." Hajiya Jummai ta ce "shegun yara kada ku yi mutuncin mana, tare da jeho musu ɗari biyu Sofy ta ɗauka tana mita haka suka tafi suna zaginta, da cewa masifaffiyar mata.

Sofy ƴat ƙanwarta ce,Suby kuwa ƴar autar su ce,yaran sam basu da tarbiyya,ba sa shakkar kowa sai maigidan. Hatta Hajiya Jummai maida mata magana suke yi. Foly suke zuwa da ke nan Katsina. In kin ga yanda suke ɗaukan kai da shan ƙamshi zaka zata ƴaƴan shugaban ƙasa ne. Alhaji Saddiƙ kaɗai ke taka musu birki in yana gari.
Chapter 9 · 0% Book details