← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 18

Sashe 3

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A zaune ya same ta kan kujera.Dirariya mace mai kyaun haiba, tare da taƙawa.tana da son addini,kana ganin ta ka san itace mahaifiyar Saddiƙ, tana taimako musamman asibitoci zuwa masallatai, cike da fara'a ya shiga ya zauna gabanta ita da shi suna yiwa juna kara nauyin shi kasancewar shi ɗan fari shi kuma bai shaƙu da ita ba,shi yasa ya ke jin nauyin ta, yanda ya zauna gabanta da ace akwai mutane a gurin tashi zatayi.

Ya dube ta, sannan ya sunkuyar da kai. "Ina kwana Hajiyar mu?"

Ta amsa da "lafiya lau, ashe ka dawo?" Ya ce"eh,na dawo jiya ban samu shigowa in duba ku jiyan ba, dafatan za ku min afuwa?" Ta dube sannan ta kauda kai, tunda dai an iso lafiya Alhamdulillah,ina kuma fatan tafiyar ta yi nasara?

Ya yi murmushi.

"Nasarori ma kuwa, domin bayan nasarar sayan kamfanin na haÉ—u da Aminina Mustapha Gumel, wanda ko yaushe ya ke raina." Ta dube shi tare da faÉ—in"ikon Allah! Lallai tafiya ta yi nasara, domin ba ta manta yanda koyaushe yake É—alibta da batun Mustapha Gumel. Ya ce"Alhajinmu yana nan?" Ta kalli gefen É—akinshi, "yana ciki amma yanzun zai fito."

rufe bakinta ya yi daidai da fitowar Alhajinmu,miƙewa tsaye ya yi tare da faɗin,"sannu da fitowa Alhajinmu" ya amsa da cewa"yauwa Abubakar Saddiƙ ,ka dawo lafiya" daidai sanda ya zauna,shima Saddiƙ ya zauna inda dama yake "lafiya lau kuma anyi nasara" ya shiga yi mishi bayanin yanda kamfanin yake girmanshi zuwa kyan injinanshi tare da gyare-gyaren da za a yi, sannan ya bashi labarin haɗuwarshi da abokin nashi tare da hukuncin da ya yanke.Alhajinmu ya ce," to Allah ya yi jagora?". Hajiyar mu ta yi gyaran murya, alamun zata yi magana, sannan ta ce "Fatima ta ce a gaya maka alkawarin motar da ka yi mata, Nafisa kuwa tayo waya daga can makaranta ka tura mata kuɗi don kuɗin ta sun ƙare."

Ya yi murmushi.

"Nafisa Æ´ar auta, ta dai kusa gama karatun nan ta huta."

Alhajinmu ya ce"ai ni na ƙosa ta ƙarasa karatun nan,na fi son auren ta." Sadiƙ Ya ce"insha Allahu zata yi Alhajinmu." dube shi "Dama na jima ina zargin kai ke ɗaure mata gindin ƙin auren nan ko?" Ya yi ƴar dariya , "ba haka ba ne Alhajinmu, Allah za ta yi ka san shi aure lokaci ne, kuma insha Allah kwanan nan zata yi" Ya miƙa ta Saddiƙ ni zan fita zuwa ofis, da akwai masu jirana." Cikin tausayawa Alhaji Saddik ya dubi tsohon nasa, sannan ya ce"ya kamata Alhajinmu ka zauna ka huta da zuwa ofis ɗin nan tunda ina kula da kusan duk harkokin ka,na fi son ka huta."

Cikin jin daɗi Alhajinmu ya ce "kada ka damu Saddiƙ,nima ina jin tausayinka ne abubuwa sun maka yawa,ni dai roƙona ga Ubangiji koda yaushe bai wuce Allah ya baka mai rama maka, inason naga zuri'arka."

Zan can Alhajinmu ya taɓa shi,don haka shima sai ya yi shiru yana jin wani abu a iranshi sai yana jin tamkar ya yi shela ya gaya wa matan duniya cewa duk wadda ta haihu da shi zai raba dukiyar shi ya bata rabi, Hajiya dake zaune tafi su damuwa tana matuƙar son ta ga ƴaƴan ɗan su namiji guda ɗaya,shi kaɗai ne namiji gun su sai ƙananan shi mata guda uku,Sadiya ta na auren ɗan gidan Sarki, Fatima tana auren shugaban ƙaramar hukuma.sai auta Nafisa ƴar lelen yayan ta Saddiƙ,yana matuƙar son Nafisa,sai dai kuma sam ba shiri da matarshi Jummai, duk da kasancewar ta ƴar uwar su. Ya fito don raka Alhajinmu wurin mota sannan ya dawo gurin Hajiyar mu don ƙara gaisawa duk da ba wata hira suke yi ba,yana son ya ganshi zaune gaban ta sai ya dinga jin shi tamkar ɗan yaye.

*Page 3*

Abba zaune gaban Malam Dari,suka gaisa da masabaha,sannan Malam Dari cikin al'ajabin abinda binciken shi ya nuna mishi,ya soma magana.

"Malam Mustapha,bayan kai abokin ka yana da wani Amini a garin nan?"

Ya girgiza kai,"ba shi da wani aboki da ya wuce ni." Ya gyara zama " abinda na gani cikin Istaharata shine,zai auri yar Amininshi da ke nan garin,abinda na yi ta bincike. Nayi bincike zata mutu ko bazata mutu ba,zata haihu ko bazata haihu ba? Allah be sa na fahimta ba,amma lallai yarka ce mata ta goma sha daya da zai aura,kuma kila ta zama uwar ya'yanshi,Allah shi ne masanin gaibu."

Zufa ce ta keto mishi ko ta ina. Ya yi shiru yana mamaki,can ya ce "Malam...." Malam Dari ya katse shi da cewa Istihara ce,in kana shakku kaima bari in baka kaje ka yi ta,ka yi ta da kyau insha Allahu ko cikin mafarki ne Allah zai nuna maka."

Bayan barin shi gidan Dari,guri ya samu ya zauna don jikinshi ya yi sanyi,shi kan shi ya kasa sanin dalilin da ya sa shi shiga cikin tashin hankalin duk da hana zaton baya rasa nasaba da mutuwar da duk matar da Alhaji Sadiq ya aura take yi. Yana son yin nazari kan lamarin,da kyar dai ya isa gida.Umma taso ta gane yana cikin damuwa ganinshi da ta yi wani iri,amma dage mata ya yi kan cewa babu komai kanshi ne ke dan ciwo yama sha magani,sallah yake son ayi ya samu ya dan huta kila bacci ne.

Bayan ya yi nafilar sannan ya gabatar da addu'o'in kamar yanda Malam Dari ya yi mishi bayani. Ya kwanta shiru maimakon bacci sai tunanin yanda zai yi,shi dai damuwarshi daya kada ya bashi itama ta mutu. To zai iya hana Saddik wani abu nashi? In ko ya yi haka bai yi butulci ba kuwa?Me zai sa ya manta da abinda Aminin nashi ya yi mishi a baya? Sai dai kuma yana tausayin Aisha,don yarinya ce karama,kashinta bai yi kwari ba. To ko dai ya yi shiru ne tunda Aminin nashi bai san komai game da maganar Malam Dari ba? Nan take wata zuciyar ta soki hakan,da cewa ka sani ko tun can Katsinan an gaya mishi cewa yarka ce zai aura? Nan take ya yardar ma kanshi cewa ga shi ma ya misalta mishi cewa tsakaninsu da nisa,tabdi! In ko Sadiq ya sani dole ne ma ya hakura da Aisha,ya aura mishi koda hakan ya na nufin itama zata bi 'yan'uwanta,wato matan da ya yi ta aure suna mutuwa. Da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba da shi.

Aisha ya gani cikin mafarkinshi goye da yaro,sai dai ba ta walwala,tana tafiya da alama cikin tashin hankali ta ke. Firgigit! Ya farka ya na addu'o'i,ya koma ya kwanta yana tausayi 'yar ta shi.Karama ce Aisha 'yar shekaru sha biyar,ga ta siririya,damuwar Aisha ita ce karatu. Tana da burin zama likita,ko yaushe ta zo hutu daga makaranta sai tace Abbanmu don Allah ka cika min alkawarin da kai mini wanda ka ce insha Allah sai na zama likitar mata,ni ina son na taimaki musulmi,ya kan ce insha Allah zaki zama,Aisha kin ma zama in dai kin dage da karatu,wannan burinta ne tun tana yarinya,gashi Allah bai yi ba. Tunda a daren ya yanke hukuncin ba yar da Aisha ga Amininsa,sai dai ya kwana addu'a,Allah yasa ita ce uwa ga yaran shi,Aminin nasa.

Da safe gurin karin kumallo bayan sun gama ya sallami 'yan mazan sannan ya dubi Ummar su "ina kawallin ta ki ? Ta ce "ta na dakina,tana gyarawa." Ya ce " da ta bari ta karya ai ko?" Umman ta dube shi "ka manta yau alhamis ? Aisha tafi mu kokarin Azumin nan na Litinin da Alhamis,tun dan zazzabin da ka yi kwanaki ni da kai muka saka shiririta cikin azumin"'. Ya gyara zama "shi yasa ina matukar son Aisha ,duk da haka kuma gashi lokaci ya yi da zamu rabu,ta dube shi da sauri "ban gane zaku rabu ba? Ya dan yi jim sannan ya ce "Aure zan mata" da sauri ta mike,"Aure! Aure dai? Ya yi karfin hali,"mene ne to na daga hankalin?". Ta zauna cike da damuwa,tare da fadin "dole ne na tada hankali,to ko dai kana tsokanata ne?" Ya dube ta" kin ga na taba miki irin wannan maganar?" Ta girgiza kai tare da shafe zufar da ke keto mata, "amma Abban yara Aisha ba ta isa aure ba,gata dama ita ba kiba ba baka ganin da kwara?".

Ya girgiza kai ba wani kwara a cikin aure,bautar Ubangiji ne,bana son ki nuna damuwarki,har ki karya mata gwiwa ina son mu lallashe ta nasan zata damu ko don yanda take matukar son karatu,ki bani goyon baya,nima inason na rama akhairan da Aminina ya jima yana min ne,wato Alhaji Saddik." Ta dube shi.Tsura mishi ido ta yi "Alhaji Saddik za ka ba ta?" Ya ce "shine" shiru ta yi yace "me ki ka ce?" Ta girgiza kai " babu komai,sai dai tausayin ta,yarinya ce ga shi kuma suna katsina ba kusa ba ne" ya ce"kada ki damu,aure babu in daba ya ksi mutum,batun yarinta kuwa duk ba komai bane,shekara kusan sha biyar ai ta girma,jiki ne ba ta dashi.Nasan Friend za ya kula da ita,yanzun kira ta in sanar da ita" Cikin jimami ta ce " To Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ta tashi ta kira Aishan,kallon ta yake yi a ranshi shima yana kara tausaya mata,saboda sam batada kauri don tsinken hannun tamkar na yara kanana.
Chapter 3 · 0% Book details