← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya riƙe mata hannu yana cewa haba menene haka kuma? Ganin yanda take rusa kuka har ma wasu daga cikin dangi suma sun soma taya ta, sai Abban ya kama hannunta ya ce,zo muje, ɗakinshi suka je ya zaunar da ita ya shiga lallashinta da cewa menene na damuwa bayan ta yi musu biyayya sannan ya san Friend ɗin shi zai kula da ita, zatayi karatun ta duka biyun, kuma suma da an ƙwana biyu za su zo shi da Ummanta. Ya miƙe ya ɗauko alƙur'ani izifi sittin da fiƙihu da Tauhidi ya ce ki riƙe wannan kin ji A'isha?" Ta share hawayenta tasa hannu biyu ta amsa tare da cewa , to Abba da gaske za kuzo? Ya ce in Allah ya so, tashi muje ga mutane can sun shiga mota ke dama ake jira. Allah ya yi miki albarka zan kira ki in kun isa,ta ce to. Abba da kanshi ya kai ta har mota inda ta zauna tsakiyar Inna Uwani da kuma Aunty Rabi matar ƙanin Abba. Suka nufi Katsina bayan ta yiwa gidan su kallon ƙarshe, tare da duban Abbanta da Yaya Abdulrahman Munnir da kuma Jafar.

Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki akan farashin masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account É—in namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

[12/4, 20:23] Ummi Tandama😇: *📗 Page 12*

Can katsina kuwa, gidan Alhaji Saddiƙ yana cike da danginshi, na gefen Hajiya Jummai da kuma ƙawayanta. Amma shaƙiƙan ƴan'uwanshi irin su Fatima, gidansu Hajiyarmu suke yin bikin su. Kuma a nan suka yi girkin saukar amarya domin suna isowa direbobin zasu kira su a waya kamar yanda suka shedawa direbobin.

Gefen Hajiya Jummai kuwa tana ɗaki tsakiyar aminanta suna ta tofin Ala tsine ga Alhaji Saddiƙ ɗin da ƴan'uwanshi da kuma amarya da danginta. Tuni suka sa ma amaryar suni mai ƙararran ƙwana.

Yamma ta yi sanda motar amarya ta iso, tunda suka shigo Katsina direbobin suka yi waya suka sanar da su Hajiyarmu. Nan take su Fatima Anty Sadiya su Nafisa da sauran dangi suka ciko mota da kuloli ɗauke da nau'ikan abinci kalolin abin sha, suka nufo gidan Brother ɗinsu. Suna shigowa kallo ya koma kan su nan dai aka je aka tsegun tama Hajiya Jummai ita da ƙawayenta suka fito falon suka shiga yada habaici, domin tsarin gidan ƙaton mahaukacin falo ne mai ɗauke da ɗakuna huɗu, falon ya shiryu da kalolin kujeru na alfarma gefe-gefe.

Kusan seti uku ban da (dinning), ɗakin Hajiya Jummai sai na su Suby sai ko na A'isha, yanzun ɗayan na baƙi ne, sai hanyar da zaka bi don zuwa gefen shi yanda ya shirya kujerun falon yana nufin kamar kowace mace da nata, domin kalar kujerunki kalar labulanki kuma suna daf da ɗakinki kayan kallonki kuma suna nan a gurin, domin tsakanin kowane ɗaki zuwa wani ɗaki da ɗan tazara. Akan kujerun A'isha suka zauna babu jimawa sai ga motocin amaryar sun iso,suka fito suka tari amarya,in da Nafisa taje ta rungumo A'isha tana cewa amaryarmu sannu da zuwa. Ta laluba kunnan A'isha tana cewa kada ki manta ki shiga gidanki da ƙafar dama tare da addu'o'i,kai A'isha ta ɗaga. Dama tun kafin su shigo gidan take zabga addu'o'i,suna shigowa sai wata cikin matan ta soma rangaɗa guɗa.

Hajiya Jummai ta miƙe zumbur tana haki,su Hajiya Karima suka riƙe ta tare da cewa,haba-haba Hajiya Jummai ai an wuce nan,me yasa ki ke tada hankalinki? Kada idanunki su rufe ki manta matsayinki, ta sauke huci, da zuwa zan yi in ɗauke matar da ta zabgo min wannan guɗar a cikin gidana da mari suka ce a'a Hajiya Karima ta jata cikin toilet me zai sa ki nuna kanki? Kada ki manta da zaran ya sadu da ita ta zama gawa kamar yanda yake faruwa da sauran matan,nuna musu faran-faran yanda za'a tafi ana yabonki,me yasa wannan karan duk ki ka kasa control ɗin kan ki ne?.

Ta dubi Hajiya Karima nima ba zan ce ga dalili ba, sai dai ina samun kaina da matsanancin Kishin yarinyar. Na tsane ta fiye da sauran kuma naga Alhaji ya fi nuna É—okin aurenta fiye da sauran na baya. Hajiya Karima ta ce don Allah manta da kishin nan gawa ce fa, yanzu dai zo muje mu taryesu ki canza kayanki kiyi sabuwar shiga,mu rufa miki baya ki gaishe su kada ki nuna mata kishi don Allah, ta ce shikenan suka fito. Nan ko take ta zabga wani uban sun less mai shegiyar tsada, suka rufa mata baya zuwa É—akin amarya.

Lokacin wasu suna sallah yayin da wasu ke cin abinci, A'isha dai lokacin tana zaune bakin gado. Nafisa tana kusa da ita tana waya, tamkar mutuniyar ƙwarai ta durƙusa tana gaishe su ƙawayanta ma suka gaishe su,ta ce ina ƙanwar tawa? Umma Rabi ta ce gata nan ta ƙudundune kai, Hajiya Jummai ta ce zamu ganki ne har mu gaji suka ce ƙwarai kuwa, Nafisa dai ko kallon ta batayi ba, amma don makirci har da cewa Hajiya Nafisa waton yau ana gurin amarya kenan ko?.

Nafisa ta gama waya amma sai ta cigaba da magana tamkar ba ta gama ba, don kada ma suyi magana da Hajiya Jummai. Suna fita kuwa su Umma Rabi suka soma yabonta kan cewa gaskiya wannan mata tana da kirki, Allah ya haɗa kansu. Nafisa dai bata ce komai ba,don ba wai suna zarginta da kisan matanshi ba ne, a'a shirine kawai basayi da ita,su kuwa suna komawa ɗaki Hajiya Karima ta ce,ni ban ga mutum ba a nan? Jummai ta ce,ai shine duk da tana rufe amma yarinya kamar ƴar kalan hanji? Wata da suke kira Hajjaju ta ce don rashin tausayin namiji sai fa ya ce zai neme ta ko? A, sosai ma, inji Hajiya Jummai, duk matan haka yake auro su amma ba ya ɗaga musu ƙafa, wannan ma ba zai kalleta ba,bugu da ƙari ma ni nafi son ya take ta. Hajiya Karima ta yi saurin ƙwabarta da cewa to ke dai ya isa zancan haka,mu dai Allah ya bada zaman haƙuri ki dai kauda kanki kawai,ta yi haka ne saboda wannan kashe-kashen sirrinsu ne sauran ƙawayan ba su sani ba. Nan take Jummai ta gano kuskuran da ta so tayi don haka sai suka shiga wani zancan.

A'isha tana zaune kan sallaya ta idar da sallar isha'i, Nafisa ta durƙusa ta ce sai da safe tunda kin ƙi cin komai sai dai zan faɗa ki da Uncle ɗin naki cewa tunda ki ka zo kin ƙi shan ko da ruwa ne.

A'isha ta dube ta,haba don Allah kar ki gaya masa. Umma Rabi ta ce ai gara dai ki sanar da shi ɗin. Nafisa ta fita tana cewa to sai da safenku, suka ce to ki gaida Hajiyarmu mun gode sosai,ta fita Inna Uwani ta ce yanzun A'isha haka za ki ƙwana da yinwa? Ta dube ta Allah Inna ni bana jin yunwa fa.

Hajiya Jummai ta shigo da sallama, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce,sannunku, sannunku fa suka ce yauwa ta ce duk kun yi sallah kenan? Suka ce mun yi Hajiya. Ta ce,to bari a kawo muku abinci, suka ce wallahi duk mun ƙoshi,kin gan shi can ma wani ne ko buɗa shi bamu yi ba,ta ce to shikenan ku zo muje in kai ku masaukin baƙi,in ya so sai amaryar da ƙawayanta su ƙwana a nan. Suka ce to, suka miƙe suka bi ta sai sa'anninta uku aka bari.

Ita dai tana zaune kan sallaya,ɗakin baƙin yana da girma ga ƙaton gado sannan ga wasu manyan katifu guda biyu an baje duk sun sha shinfiɗa. T.V na bango ne a ɗakin kamar dai na falon sai dai shi ƙarami ne,ga (AC) ga kuma bayi. Ta buɗe wordrobe ta ciro musu manyan barguna kasancewar lokaci ne na sanyi, sannan ta ciro parnpas ta ce, masu yara gashi nan suyi musu nafkin,ta kunna musu T.V tashar da ake yin wasan Hausa,wato fim ɗin Hausa. Ta ce,in zaku yi bacci sai ku cire soket ɗin, kada ku manta da yiwa yara addu'a kun ji ko? Ku karanta musu ƙulhuwallahu,falaƙi da Nasi ƙafa uku-uku, da kuma ayatul kursiyu duk ku shafe jikinku da shi dana ƴaƴanku, suka ce to mungode fa Hajiya, Allah ya saka miki da alkhairi,ta ce haba ba komai sai da safenku,ku huta gajiya suka ce to Allah ya bamu alkhairi,ta fita ta ja musu ƙofa,su kuwa suna ta yabonta da cewa Allah ya saka mata tana da kirki,lallai A'isha ta yi dacen dangin miji da kishiya,ita kuwa fita ta yi tana cewa ƴan iska ba zaku gane ba ne sai kun zo zaman makoki.

Ita ko A'isha tana nan zaune kan sallaya ta zuba tagumi, yayin da su Naja suka yi É—ai-É—ai kan gado har sun soma bacci saboda gajiya zuciyarta ta nata neman dalilin da yasa É—azun da Hajiya Jummai ta zo musu sannu da zuwa gabanta ya yi mugun faÉ—uwa, yanzun ma haka. Tana sallama ta ji gabanta ya faÉ—i,in ko haka zata ci gaba da ji lallai zata bani tunda guri É—aya suke. Ta soma tambayar kanta da cewa menene ma na jin tsoron ta ko faÉ—uwar gaba dan ta ganta? Mace mai karamci da mutunci.
Chapter 13 · 0% Book details