← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai-dai sannan Alhaji Saddiƙ ya gama waya ta ɗan saci kallonshi da gefen ido. Wata jiƙaƙƙiyar shadda ya saka kalar ƙasa,ya yi ƙyau sosai ta zamo daga kan kujera don ta gaishe shi.

"Ina yini Uncle?"

"Bana cin miƙe A'isha, daga nan za ki gaishe ni?".

Ta saka gyale ta rufe fuskarta, sannan ta miƙe taje gefenshi ta tsugunna,muryarta ƙasa-ƙasa ta sake gaishe shi. Ya amsa yana dariya.

Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta burge ta, A'ishan ta mata ƙyau,sai dai yarinya ce ƙwarai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi A'isha ya ce, "Ga ƙanwata Nafisa." Ta kuma duban Nafisan.

"Sannu da hanya"

"Yauwa," Nafisa ta amsa da fara'a.

A'isha ta miƙe tana kallon Nafisa, "Bari na kira ƙawayena." Har za ta fita, ya ce "Zo" Ta dawo ta tsugunna.

"Wa zaki ce musu ya zo?"

Ta rufe fuska,tana ɗan murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu labarina ne?" Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle ɗina ne." Ta miƙe ta fita da sauri. Dariya Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddiƙ duk da A'isha yarinya ce kun matuƙar dacewa, Allah dai ya yi mana jagora tare kuma da shige mana kan matsalarmu." Ya ce "Amin sister."

Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle ɗinta ne daga Katsina, suka shigo suka gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ƴar garinmu? To sannuku,ku dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na gode." Suka fita suna mamakin dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba ta taɓa gaya musu ba? Zainab kam so take ta tuna inda ta san shi.

Nafisa ta miƙe, "A'isha bari na bi ƙawayenki na ɗan miƙe ƙafa," A'isha ma ta miƙe ta fito, kira ta ƙwalawa su Zainab.

"Ga baƙuwa ko zaku je school shop."

Suka ce, "To" ta dawo ofis É—in ta zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da godiya, shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda aikin shi ya koma Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga Dutse?" Ya ce "Haka ne,to yanzu yaushe ne zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar zuwa shida." Ya ce, "To so nake a shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a É—aura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce, "Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya ce, "wannan babu komai, sai makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya ce, "No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."

Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C ya rako shi har gun motarsa. A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan Zainab,ya zo ya bi su Uncle É—in ta mana tunda suma Katsina za su je.

Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ƙwalaye a ƙasa daga boat ɗin motar,Sani yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddiƙ K.T. mutumin da ya yi kuɗi da jinin mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu yana son shan jinin ƴan makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.

Alhaji Saddiƙ ya miƙa ma Nafisa bandir ɗin kuɗi yace ba ƙawayan nata. A'isha ta leƙo tana cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ƴan garin." Ya ce, "Ni fa ko Nafisa kaɗai ki ka sani?" Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai je". Alhaji Saddiƙ ya ce, "To ya shiga mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina da aboki nan cikin Munjibir,ta je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.

Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle É—in ki?

Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."

"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji SaddiÆ™ Usman K.T É—in ne baki sani ba."

Zainab ta dafa ƙirji da ƙarfi.

"Kana nufin me kuÉ—in jini?" Ya ce "shi ne mana."

A'isha ta zaro ido,me kuÉ—in jini kuma?" Sani ya ce, "tabÉ—i,ke da baki san halin Uncle É—in na ki ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."

Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min gaske ne?" Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo mu ƙwashe kayan nan." Ta ce, "ai ni bazan ɗauki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da Zainab har ma da Sani suka shiga ƙwashe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin baƙon al'amarin, har suka raka Sani suka dawo.

Zainab ta zauna kusa da ita, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-aure ya ke yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma, uwargidan ce kaÉ—ai bai cinye ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka zuuu sai dai ka ganka a cikin wani É—aki a gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a cikinshi, ko ba ki san gidan ba?"

A'isha cikin tsananin tsoro ta ce "ban taɓa zuwa ba".

Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ƙyan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne wani mahaukacin gida ga bishiyoyi."

A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk kayan da ya kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ƙwana uku ta ƙwanta ciwo,ƙwananta biyu ta ɗan samu sauƙi. Amma duk ta rame su Zainab sun yi ta matsa mata da son jin gaskiyar lamarin ta da Alhaji Saddiƙ don sun ga yanda ta ɗauki abin da zafi ƙwarai. Ta gaji ta gaya musu cewa Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da addu'a, Allah ya shiga tsakaninta da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.

A daddafe dai suka yi jarabawa, Abba da Abdulrahman ne suka zo ɗaukanta, Abba ya dube ta, "A'isha ciwo ki ka yi haka? Na ganki ne babu ko ƙyan gani?" Hawaye ya soma zubo mata, cikin sanyi murya ta ce "Abba nayi ciwo ne sosai."

Sun isa Jigawa misalin ƙarfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon sabon gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa iyayenta suna cin kuɗin ƴarsu ne. Nan take hawaye ya soma zubo mata,ta shiga ciki.

#######
[12/2, 08:00] Ummi Tandama😇: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*ÆŠandano page 7*

Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani tsararren kitchen ta hangi Umma, Umma tana juyowa ta yi arba da Æ´arta, da sauri ta fito tana cewa ga Æ´an makaranta ga Æ´an makaranta." A'isha ta faÉ—a jikin Umma tana kuka.

Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da Abdulrahman suka shigo, Abba ya ce, "ƙawallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga yanda ta ƙare?" Umma ta ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai duk jikina ne bana jin daɗin shi. Suka shiga falo kan kujera ta ƙwanta tana ƙara kallon yanda aka tsara falon da kuɗin jini, duk sai ta samu kanta da ƙyanƙyamin komai na gidan. Umma ta zubo mata abinci ta tasa shi ta kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ƙi cin komai. Hankalin Iyayen ya tashi, cikin dare zazzaɓi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole da safe suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka yasa mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.

Ƙwananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba ta magana. Umma ta matsa mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke damunta. A'isha tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi kuma ya yi faɗa. Ko ma ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.

Abba yana zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma ta shigo ɗakin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika ɗaki da kaya bane tunda cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce kana nan na fito ban ganka ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin a gabana in gani," Umma ta ce "to nima dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ƙoƙarin ganin ta ci abincin,ko don hankalin iyayenta ya ƙwanta, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji Saddiƙ ne?" Da sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba ne Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai mun gama magana,jiya ma nake sanar da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon ki ba, saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."
Chapter 7 · 0% Book details