Sashe 12
Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To kin ji yanda muka ƙwashe da Alhaji,babu abinda ya fi bani haushi wai har an kai lefe bani da labari saboda rainin hankali, ke kayan faɗar kishiya ma shi ya siyo min, saboda haka ina son mu koma gurin Boka, gashi bakon ya ce in biki ya rage ƙwana goma in koma,to gashi yau sauran ƙwana taƙwas. Tunda jiya tara ya ce min ne ko nawa ne ma oho."
Hajiya Kari ta ce, "To gobe sai mu je,in ce dai kin binne abin da ya baki?" Ta ce "ina fa ni ban fa san taƙamaiman lokacin ba sai jiya,na san zai kama zigar waɗannan ƴan iskan ƙannan nashi ne" Hajiya Kari ta ce "Bari mu gama da amaryar, har su ba za'a barsu haka ba, sai mu shiga tsakaninsu." Hajiya Jummai ta ce, "Da ko kin taimaka min,ba ma dai irin tsinanniyar Nafisan nan, gashi yafi ji da ita duk cikin su."
Ta binne surkullen da aka bata,ta kuma yayyafa na yayyafawa kamar yadda aka umarce ta. Sannan ta nutsu don tana son samun kuÉ—i a hannunshi, duk da wannan karon ya tsuke mata bakin aljihunshi, ta samu dai-dai gwargwado.
Lokaci na ta zuwa gida kam ya sha fenti da gyara, yanda ya ba ta kuɗin canjin kayan ɗaki, haka ya ba su Fatima da Sadiya da Nafisa kuɗi su siyo na ɗakin A'isha, sannan shima nashi gefen sai da ya canza komai. Nan fa ta tada balli kan cewa shin wannan amaryar ta fi sauran ne yake ta faman kashe kuɗi har da sa mata kayan ɗaki? To ba zai yiwu ba,ya ce Jummai ki daina tada jijiyar wuyanki akan abinda ba za ki hana ba,yarinyar nan ko ba ni ne zan aureta ba kusan dole ne in mata kayan ɗaki, ballantana gidana za'a sa,kina cewa ba zata yiwu ba,za ki hana ne? Kema fa na baki haƙƙinki."
Su Hajiya Karima ne suka tausasheta da cewa yarinyar da ba mazauniya ba ki ke damun kanki? Gawa ce fa.
Ita ko A'isha, amarya duk ta gama sukurkucewa,iyayanta ma suna daurewa ne kurum,tuni Æ´an'uwa da abokan arziki sun cika gida don yin biki.
Ranar É—aurin aure ta kasance asabar,don haka Æ´an ango sun iso juma'a domin ana gama É—aurin aure za'a É—auki hanya da amarya. Alhaji SaddiÆ™ ya kasa zuwa É—aurin auren,waya ya yi wa Friend É—in shi kan cewa ba zai samu zuwa ba,don ba ya jin daÉ—i. Lafiyar shi lau sai dai yana ganin kamar za'ayi ta nuna shi,ko kuma Friend ya shaidama Æ´an'uwanshi halin da ake ciki,ko su iyayan in sun ganshi su dinga mishi kallon wanda zai yi musu sanadin Æ´arsu da dai sauran tunani kala-kala.
Daren juma'a aka sanya amarya a lalle,ba ta saka kowace ƙawa ba, sai dai ƴaƴan ƴan'uwa sa'anninta. Da dare suna ƙwance a kan katifa zuciyar A'isha cike da tunanin gobe zata rabu da Ummanta da Abbanta,ƙila ma rabuwar kenan. Hawaye ne suke bin gefen kumatunta, wayarta tana ta ruri. Naja ta ce Amarya wayar ki na neman agaji, A'isha tasa hannunta ta lalubo wayar,muryarta a dusashe ta ɗaga wayar tare da cewa "Assalamu alaikum, Nafisa ce?" Ta ce "amaryar mu,na so in zo ban samu zuwa ba, sai dai in kin zo gobe mun haɗu, " ta ce "to ina yini ya ya su Hajiya? Nafisa ta ce, kowa lafiya, gama Hajiya nan,sai dai nasan ba zata ɗaga wayar ki ba saboda Brother ɗinmu ɗan fari ne,tana mishi kara.
A'isha ta ce,to ki gaida ta,ta ce to ga Uncle ɗin naki dama yazo ne nace ya kira min ke gobe. Ta ɗan yi ƙasa da murya kada ki manta da addu'o'i daren yau, saboda Allah ya yi mana jagora a cikin ɗaurin auren da za'ayi a gobe. Shiru kawai A'isha ta yi mata, sai kawai ta ji Muryar Uncle yana cewa, Beby kina jina? Ta ce eh, zuciyarta kuwa sake karyewa ta yi hawaye ya shiga sintiri a kumatunta, ya ce na kasa zuwa ne Beby sai ina ganin tamkar ban yi wa mahaifin ki adalci ba, ina jin nauyinsu, kukan da take maƙalewa ya kufce mata, ranshi ya daɗa tsinkewa, ya ce "A'isha kiyi haƙuri daina kukan zan yi miki magana ne," ta share hawayen ta sannan ta yi ƙoƙarin tsaida kukan ta ce, ina jin ka, ya ce ina son ki tashi daga wannan kukan ne kiyi alwala, nafila za kiyi tare da addu'o'i kin ji ko? Alkhairin da ke tare da auren,ki tsaida zuciyarki,ki daina wasi-wasi,ki saka a cikin ranki cewa duk yanda Ubangiji ya yi dake dai-dai ne,kin amince?" Ta ce "Uncle dama ni bani da wani zaɓi sai wanda Allah ya yi min, sannan zan yi duk yanda kace." Ya ce yauwa Beby sai da safe.
Tsam,ta miƙe,Naja ta bita da kallo,ta shige (toilet) ta ɗauro alwala.
Naja ta dube ta, Angon yayi lallashi kenan mu ko munyi mun gaji kin ƙi kiyi shiru? Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce,Naja kenan ba zaki gane ba ne, sannan ta tada sallah. Sai ya kasance wannan dare duk wanda yasan halin da ake ciki tsakanin Katsina da Jigawa idanunshi biyu ya kwana, kuma tsaye gaban Ubangiji, ana ta kai kuka. Zuwa wayewar gari kowa ya tattara komai ya miƙa wa Allah, sai sauraro duk sun nutsu da cewa duk abinda Allah ya yi daidai ne.
A'isha kam sai ta wayi gari zuciyarta sake duk ƙuncin da take ji ya washe, sai dai ɗan abinda ba za'a rasa ba. Hakan ya yiwa Umma daɗi har ta isko Abba cikin ɗakinshi,tana shaida mishi cewa...
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*ÆŠandano page 11*
*ƘARSHEN FREE PAGES*
*Alhamdulillah Æ™arfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi Æ™oÆ™ari ki mallaki naki akan farashin masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇ðŸ»*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account É—in namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
Shaida mishi cewa yau kam A'isha ta saki ranta,suna cikin zantawa sai ko ga A'isha ta yi sallama domin gaida Abbanta, bayan ta gaisheni ne ya ce "yauwa ƙawar Ummanta dama ina son in kira ki domin inyi miki nasiha duk da cewa tun da bikin nan ya matso muna tayi miki,na farko dai nasihar da zan miki ita ce, zaman aure ya banbanta da zamanki na gida,don nan iyakaci kici abinci ki ƙwanta da dai sauransu. Yanzun kam da zaran an ɗaura aure Akwai wasu haƙƙoƙi guda goma da suka hau kanki na mijinki.
Na farko shine ki yi masa biyayya duk abinda ya ce kiyi,ki yi masa, matsawar bai saɓawa addini ba, kamar yanda ki ka sani babu biyayya ga abokin halitta don saɓawa mahalicci.
Kima zama mai tsafta kamar yanda ki ka ga Ummanki tana yi, tsafta bata jiki kurum ba har da muhallinki.
In kuma ya kira ki zuwa shinfiÉ—arshi kada ki bijire.
Ta dubi Abba da sauri kamar tana neman ƙarin bayani, domin A'isha yarinya ce sannan ba wai suna zama da ƙawayanta suna hirar samari ko ta aure ba ne,haka nan bata da wata ƙawa wadda ta yi aure ballantana ma taji labarin zaman auran, kazalika ita ba ma'abociyar karance-karance ba ce, ita ana ta zaton in an mata aure zata na girki tana kai ma mijin ruwan wanka tasa mishi na buta kamar yanda ta gani Ummanta tana yi, sai ko gyaran ɗakin Abbanta da Umman bata bari wani ya yi sai ita.
Abba ya katse mata tunani da cewa, ma'ana in ya neme ki kada ki guje shi, Umma ta ce,nima na miki duk nasihar da ta dace,na sani ke dama mai biyayya ce,ki girmama Æ´an'uwansa,ki É—auki mahaifiyarsa tamkar taki, haka mahaifinshi, matarsa ki yi mata biyayya."
Hawaye suna zuba daga idanunta, ta ce insha Allah zan yi Abba da Umma, suka sa mata albarka tare da yafe mata,ta miƙe ta fita suka bita da kallo cikin tausayin ta yayin da ita kuma ta wuce cikin tsananin damuwa.
Ƴan ɗaurin aure sun hallara in da aka ɗaura aure. Maroƙiya ta shigo tana rangaɗa guɗa, A'isha dai-dai lokacin tana wanka wanda Umma Rabi ta matsa mata ta yi umma Rabi ƙawar Ummanta ce,tun suna dutse tana fitowa ta ji gidan ya kaure da guɗa, duk sai taji wata fargaba a cikin zuciyarta. Inna Uwani Ƙanwar Umma, ita ta ciro mata wani leshi baƙi mai ado, ruwan lemon zaki tasa ka,sun bata siket da bes da kuma pant duk baƙaƙe.
Aunty Hasiya mata ƙanin Abba ta ce ni ban ga ma rigar nono ba cikin kayan? Umma ta ce ba a saka ba, Umma Rabi ta ce to me za'a sakama ƙirjin ba komai, ita dai A'isha tana jin su, Ummanta ta ce kin ji saka kayanki ki tafi nan duk iyayan banza ne suka taru. Ta gama shirinta ta fita, bayan an ɗan natsa da gama ɗaurin aure sai kuma aka shiga shirin tafiya Katsina,kai amarya. Duk wanda ya cancanta ya yi wa amarya nasiha ya yi mata,dangin Uwa da na Uba. Idanu ta zuba ma Ummanta a zuciyarta tana raya cewa, ta yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe. Haka nan aka fita da ita tana ta rusa kuka.
Abbanta da sauran mutane suna waje gurin mota suna ta ce waɗanda zasu je Katsinan,don kowa yana son zuwa, kuma tafiya ta gari ba kusa ba,don haka suka ce dole ne wasu su haƙura ba kowa da kowane zasu je ba, an fito da ita tana cin kuka ganin Abbanta sai kuma ta ƙwace ta nufi gurinshi.