Sashe 1
Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*ÆŠandano page 1*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇ðŸ»*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
Ya shigo gidan cike da fara'a yana faɗin "ina Umman yaran gidan nan ne?" Daga ciki ta amsa da cewa "gani Abbansu" ya iso cikin kitchen ɗin, tsaye take tana haɗa lemun soɓarodo yayin da A'isha ke jera ƙwanuka domin raba abinci, tace sannu Abba, yace yauwa ƙawallin Ummanta,ya dubi Umma "ina da babban baƙo fa" ita ma ta dube shi cikin kulawa"daga ina?"
Ya fadada murmushin sa "zakiyi mamaki idan nace miki Alhaji Sadiq Usman kt ne" cikin mamaki take dariya " lallai munada babban bako yau kam zanga wannan Alhaji Sadiq naka" ya juya tare da cewa " muna falo na" tace "to".
Ta amshi rabon abincin daga hannun Aisha tace "kawo nan in zuba musu,ki kai musu abin sanyaya makoshi,kafin na zuba masu abinci ko? Aisha tace "to Umma" nan ta shiga hada kaya kan tire,lemun zobo ne mai dan karen sanyi tare da ruwan leda shima mai sanyi guda hudu sai kofuna guda biyu.
Tayi sallama falon Abba,inda suka kaure da hirar yaushe gamo? Suka amsa mata cike da fara'a ta shiga kan tebur ta daura tiren sannan ta dan jaa teburin zuwa gabansu,durkusawa tayi gwuiwa biyu a kasa tana zuba musu zobon cikin kofuna tana ce da bakon " Uncle ina wuni?"
Ya dube ta " lafiya lau yar Uncle "gabanshi ya yi wani mugun faduwa ya daure yace "yaya karatu?"
Tace "Alhmdllh, yaya hanya?" Yace "lafiya lau hanya,me sunan ki? Ta mike ta mika musu zobon sannan tace " sunana Aisha".
Ya dubi Abba yace " yanzu ya'yan ka nawa Mustapha?" Abba cikin fara'a yace "su hudu ne" Aisha fita sannan ta dawo ta kawo masu abinci Ummanta tana biye da ita cikin fara'a suka shigo ta gaisa da Alhaji Sadik Usman dan mutan KT,ta zauna tana zuba musu abincin tana cewa "yau dai naga Alhaji Sadiq KT" Alhaji Sadiq ya dubi Abba yace " Friend kace kaima ko yaushe kana labari na?"
"Sosai ma" inji Abba ya cigaba da cewa "ai kai ba abokin da za a manta dashi bane"
Sukayi dariya.
___________
Kwance a masaukin baki na sukuni (Guest House) da ke nan cikin Dutse,Alhaji Sadiq ne zurfi ya yi cikin tunani,ko shakka ba ya yi Aisha yar abokinshi Mustapha ita ce yarinyar da duk sanda ya yi Istihara yake gani cikin mafarkinsa,kuma ita ce Malam Mamuda ya kwatanta masa cewar ita ce uwar ya'yansa.
Sai yanzu ya tuna wata tattaunawa da suka yi da Malam Mamuda ya sanar da shi cewa yarinyar da zata haihu da shi tana wani gari ne mai nisa da Katsina,kuma a cikin Istiharar ta shi yana zaton akwai matsaloli can kasa cikin al'amuran,ya sani matsalolin ba za su wuce na kaddarar da ke faruwa kan duk matar da ya aura ba,ya sani ba kowa zai yarda ya ba shi auren yarsa ba matsawar yasan wane ne Alhaji Sadiq K.T.
Mikewa ya yi yana kai komo cikin masaukin nashi,ko dai ya sanar da aminin nashi matsalarshi? To in ya gaya mishi anya zai yarda ya ba shi auren yarsa Aisha? Me zai yi yanzu? Alwala ya yi cikin toilet ya fito ya cire kayan barcin shi ya maida jallabiya ya tada kabbara zabin Ubangiji ya shiga nema tare da addu'ar Allah ya kawo mishi mafita cikin lamuranshi,cikin barcinshi yake ganin yarinyar zaune tare da wasu yan yara guda biyu masu kyau da kuma kama da shi.
Da safe ya fito cikin yadin boyel fari tas,ya murza hula kube fari ya fi yawa jikin hular,takalmanshi sawu ciki ne suma farare kamshin sa tun fil'azal ya na tashi.
Alhaji Sadiq kyakkyawan Bakatsine ne,dogo mai cikar zati yana da kyau,tare da kwarjini,wankan tarwada ne fatar shi kurum in ka kalla ka san cewa ta goge da hutu,kamshinsa kawai zakaji ka san ya kama kasa,gidan Friend din ya nufa wanda ba ya da nisa daga masallacin dake bakin titi wato kan layin in an fito.
Aisha ce sanye da dogon hijabi ya fasa shiga layin ya tsaya,ya sauke gilashin motar,ya leko "ina za ki je ne Aisha?" Ta dubi gurin motar,ta dan saki fara'a.
"Sannu Uncle,Ina kwana?"
Yace "lafiya lau Aisha,ina zaki je?" "Zan je hadda ne."
"Ina Abbanki?"
"Yana gida,yanzun naji ya ce za yaje gurinka."
"To shigo in kai ki."
"Ba nisa Uncle,kuma gurin lungu ne mota bata shiga sai dai mashin."
Ya miko mata sabuwar dari biyar "ki hau mashin din"
"A'a ka bar shi,Abba ya ba ni."
"Eh amshi nawa."ta amsa sannan ta ce "nagode" ya ja mota ya tafi.Tafiya take amma ranta cike da tunanin kyautar da ya yi musu ta jiya,dubu hamsin ya basu wai a sai musu sweet bai samu ya yi masu tsaraba ba.Kai gaskiya Uncle yana da kirki,ya burge ta musamman ma da ta ji taimakon da ya yi ma Abbansu,Allah ya ba shi haihuwa,ta kula burin shi kenan,in ta yi la'akari da yanda ya yi ta nuna sha'awar su.
Ya fito da mashin don zuwa masaukin Friend din nashi sai kuma ya hango motarshi tana shigowa cike da fara'a suka tari juna.Tafawa suka soma yi tare da kiran juna,Friend kamar yanda suke yi zamanin suna B.U.K "ina zaka da?" "Gurin ka na nufa" "da kaje ma sai dai mu dawo don kunu nake son sha,sukayi dariya sannan suka nufi cikin gidan,kunnun tsamiya Umma ta yi da kosai,ya ci sosai ya ce "kai na dade rabona da na ci wani abu kamar yau. Ina son wadannan abubuwan amma ba na samu"
"Ban gane ba ka samu ba iyalinka ba za ta yi maka ba?" Dan tsaki ya yi sannan yace "kasan matanmu mace tana ganin kana da hali shi kenan sai ta kwanta wani kato dole za ka dauka yana muku girki kana biyan shi"
"Allah ya kyauta " inji Abba "amin dai" Abba yace "Yauwa inason in tambaye ka,shin ka taba neman taimako daga Malamanmu na addini domin samun haihuwa? Sannan me likitar suka ce kan matar ka?" Alhaji Sadiq ya gyara zama ya sani yana da abokai da yawa,amma ko da wasa bai hada su da Mustapha ba,dan shi yana da amana tare da zurfin tunani,in ya baka shawara za ya yi wuya kaga rashin fa'idar abin.Tuno hakan yasa shi sanar wa abokin nashi abinda ke ranshi game da matsalarshi,ya dube shi friend ka san wata matsala? Abin ala'ajabi duk inda muka yi yawon ganin likita sai ace Jummai ba za ta haihu ba,saboda ta yi amfani da kwayoyin hana daukar ciki kuma sun lalata mata mahaifa su ko Egypt da muka je cewa sukayi an taba mahaifarta ne sakamakon cire ciki da ta yi.Abin ya bani mamaki sosai,amma ta musa min,kuka sosai ta yi tare da ce min sun mata sharri ne ban da tacewa tunda yar'uwata ce dole ne na rufa mata asiri.
Abba ya ce "to me ya hana ka ka kara aure?"
Yayi dan guntun murmushi irin na damuwa din nan,sannan ya ce " Abokin Alhajinmu ya ba ni auran yarshi Murja,karamar yarinya mai kyau da kyan hali,aka yi bikinmu,amma cikin rashin sa'a a ranar da ta cika sati biyu ta ce ga garinku nan? Tana sallar asubahi ya ci gaba,ranar da ta cika kwana arba'in da mutuwa aka daura min da kanwarta,abin al'ajabi kwanan ta goma ta ce ga garinku nan,cike da zargin wani abu Abba yace " ba a gwada ta aka san mene ne musababbin mutuwar ta ba?" "Likitoci sun gwada ba wata guba ko duka ko irin toshe numfashi din nan sam,bayan yan watanni bayan rasuwar ta na hadu da wata yarinyar layin su Hajiyarmu,Jamila ta dawo Islamiya na tsaida ita,dabi'unta da yanayin maganar ta sun sata shiga raina,ta nuna min gidansu zuwana uku manya suka shiga maganar saboda an san juna tsakanin gidanmu da na su,Hajiya Jummai matata itace ta hada min akwatuna matsayin gudunmawarta,don itama tana son ta ganni da dan kaina kamar yanda kullum take min korafi.
Bayan biki na shiga yin amarci tare da sabuwar amaryata.
Ranar dana cika kwana bakwai na bar dakinta,ran kwana tara na dawo mata.Ina cikin yin auratayya da ita sai na ji yarinya bata motsi sai na tsaya na dubata,abin al'ajabi sai gawa."
Ya yi shiru,sannan ya furzar da wani huci mai zafi saboda tuno tashin hankalin da ya shiga ranar,ya dafa Abba sannan ya ce, "wallahi Mustapha ba zan iya shaida maka tashin hankalin da na shiga ranar ba" Abba cike da mamaki yace "ikon Allah,ba ka samu malamai ba don taya ka addu'a? Duk da cewa mutuwa ta Allah ce".
Ya cire hularshi ya ajiye "me ka ji ma tukunna" ya cigaba "Alhajinmu da kanshi ya tashi muka je gurin Malam Mamuda,Malami ne mai takawa ba irin na tsibbu ba addu'a muka bukaci a taya mu da ita sai ya ce za yayi Istahara kan al'amarin ya bukaci mu tafi bayan kwana biyu uku mu dawo,sanda muka dawo cewa ya yi mu ma muje mu cigaba da addu'a,ya ga matsaloli da yawa,sannan kuma zan samu haihuwa ko nan kusa ko bayan shekaru.Sannan matar da zata haifa man yaran yarinya ce karama,kazalika akwai sanayya kuma tana nesa da garin katsina,yar fara ce mara jiki.jin haka na soma neman aure a wajan Katsina,farko na auri Rukayya a Kano,kwananta sha daya itama ta ce ga garinku nan,faruwar haka sai mutane suka shiga cewa kila ma arzikina da yake bunkasa ina cikin kungiyar asiri ne,wasu su ce yankan kai nake yi sai jama'an gari suka shiga tsorona har ma ba a barin yara su bi ta layin gidana,ban damu ba.
Wata rana na je Kaduna don siyan wasu injina da banki ya yi gwanjonsu,saboda bashin da yake bin wani kamfani.