Sashe 2
Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mun fito cikin kamfanin inda na dudduba injinan,wata yarinya na gani yar siririya ta min yanayi da yarinyar da Malam Mamuda ya ce min zata haihu min take na ce ke mai gyada kawo,wadanda muke tare sun sha mamaki ganinsu mutum kamar Alhaji Sadiq K.T ya sha karfin wannan gyadar,nace "gyadar ta nawa ce?" Ta ce "dari uku" na bata dari biyar,"je ki bawa almajirai sadaka,ta ce "to ba canji" na ce "ina ne gidanku in ba nisa je ki samo" ta ce "Badikko ne" na ce jeki na bar miki.
Bayan munyi sallama da Manajan Bankin duk da ya so mu tattauna sai na sallame shi na ce mishi nan zan kwana,gobe zan zo mu tattauna.Injina sun min,don haka inaso sai gobe zan zo na shiga mota na ce da direba mu bi yarinyar nan,ya ce "Yallabai ban san in da ta yi ba ,na nuna mishi wani titi nan naga ta bi,mu bi mu na kan titin Ahmadu Bello way ne,ita kuma ta bi titin da zai kai ta gidan Gwamnatin Kaduna ne.
Muna bi kuwa sai ga ta can ta yi nisa, kadan-kadan muke bin ta har muka ga gidan su,ba tare da bata lokaci ba nasaka direbana ya yi sallama da Maigidan,na gabatar da kaina matsayin mai son 'yarsu kuma na yi musu bayanin daga inda nake.
Ban samu matsala ba,cikin wata biyu suka bani auren yarinyar,abinda ya tsaya min a rai shi ne,yarinyar ba ta sona sam,sai ina ganin zata so ni nan ba da jimawa ba,da zaran ta haihu.Yarinyar nan kwananta tara itama ta rasu.
Na tsorata kuma daga kanta na yi alkawarin na daina aure,kuma na hakura da haihuwar,haka muka ci gaba da zama ni da Jummai.Hamshakiyar mace ce mai son hutu,tana da masifa tare da raini ga talaka....
######
[12/8, 08:05] Ummi Tandama😇: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*ÆŠandano page 2*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇ðŸ»*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427
Hamshaƙiyar mace ce mai son hutu, tana da masifa tare da raini ga talaka amma game da zamantakewata da ita tana min biyayya. Mun shafe ku san shekara Bayan rasuwa Hafsat,wata rana naje Zariya sai na yi shawara na ƙarasa Kaduna in gaida Iyayen Hafsat, domin duk matan da na aura ban yada iyayensu ba, duk sanda muka fitar da zakka ina aika musu, haka nan Azumi ko sallah.
Cikin yardar Ubangiji na gaishe su tare da musu ihsani,sai na ɗauko hanyar tafiya daidai shataletalen Bankin Habib nan Shehu Musa Ƴar'adua House, tsautsayi kurum ban san ya ya aka yi ba kurum na buge wata yarinya,tana ɗauke da tiren ƙwai duk da ba taji ciwo ba,sai da na kai ta asibitin Fotifo don su dubata, sannan na kai ta gidansu da ke Abakwa.
Wannan ne silar auren Amina itama sai ta bi ƴan'uwanta,kai wannan yasa nima na san babu lafiya,mata shida? Jummai kam kuka take tana ƙara wa tana faɗin wannan sai wani ya ce da sa hannun ta,na ce babu saka hannun ki Jummai ba ke ki ke halitta ba, kuma ba zaki iya kashewa ba so kada ma ki saka ma ranki wannan."
Ya dubi Abba "My Friend ka san wani abu?" Abba da tsananin al'ajabi ya hana shi magana ya ce "ina jin ka sai ka faɗa". "wallahi sai da nayi aure tara ban da Jummai fa, kuma ban taɓa maida wata ɗakin wata ba,sai dai itama na bata wani ɗakin. Ta taran ma an kai ta kamar yau, washegari ta yi sallar Asubahi ta koma ta ɗan kwanta ashe ƙwanciyar kenan.Tun sannan na haƙura domin sai na ke ganin kamar ni ne ma ke kashe su,ji nake kamar sun rataya a wuyana. Ranar na je gaida Malam Mamuda ya ba ni addu'o'i tare da nafilfili sannan ya bani Istihara na je na yi da kaina tunda na soma Istihara ɗin nan wata yarinya na ke gani yawa yawan mafarkan da nake yi na kan ganta da yara,na kan ce to ni dai na haƙura ba zan kuma taƙalo wani aure ba.
Abba ya yi nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce, "shin Friend ba ka zargin maiɗakinka ko? Kasan mata sun tsani ba haihu ba wasu su zo su haifa.Alhaji Sadiƙ ya girgiza kai sam ba na tunanin haka zahiri Jummai tana da masifa tare da rowa, wulaƙanci da sauran wasu halaye, amma ba ta shige-shigen malamai ina ganin maƙonta ma ba zai barta ta iya bawa malamai kuɗi ba, nafi tunanin ko ina da wasu iskokai ne. Abba ya ce"kenan nima ina ganin friend lokaci ya yi da zan ga irin taimakon da zan maka na daɗe inason in ga nima na maka wani abu amma hakan bai samu ba, saboda duk wani da zan yi tunanin baka kafini ta ko'ina nima lokaci ya yi da zan nema *maka* mafita gurin Ubangijinmu."
Alhaji Sadiƙ ya ce "na ji daɗi sosai Friend Allah ya ja mana gaba,sai dai ka san irin gurin Malaman da za ka gurin su saboda aƙwai masu kauce hanya" Abba ya ce "kada ka damu ni kaina bana ra'ayin su" Alhaji Sadiƙ ya ce "dama kuma ina son maka albishir da cewa in har mun gama daidaitawa kan maganar kamfanin da na yi maka maganar shi a Jigawa, zan damƙa kula da gyaran shi a hannunka, sannan in an kammala gyaran ina mai farin cikin shaida maka insha Allahu kaine za ka zama Manajan kamfanin"kallon shi kurum Abba ke yi ya ma rasa me zai ce, Alhaji Sadiƙ ya yi murmushi ya tuno sanda suke makaranta duk in kaga ya yi shiru yana mishi irin wannan kallon to ya yi mishi alkhairi,don haka ya dafa shi tare da faɗin"a'a Friend kada ka ji komai" Abba ya miƙe tare da tuno baya.wannan kalmar Sadiƙ ke furtawa in yaga yayi shiru ya kasa godiya sai ya ce dole inji komai Friend sai yaushe ne ni zan taimaka maka? Haka shi kuma kan ce lokacin yana zuwa,sai kuma suka saka dariya, tare da tafawa saboda sun tuno baya, sannan Abba ya ce"nagode Friend, Allah ya shige mana gaba, kuma kaima Allah ya cika burin zuciyarka," "amin" inji Alhaji Sadiƙ.
A gajiye ya fito daga cikin motar,yana saka ƙafa cikin falon Hajiya Jummai tana isowa gurin, rungume shi ta yi tare da faɗin "Oyoyo Abubakar Sadiƙ ɗin a" shima matseta ya yi a jikinshi yana shaƙar daddaɗan ƙamshin ta.
"Na yi missing É—in ki da yawa"
Cikin jin daÉ—i ta ce, "har ka kai ni?" Ya kalli manyan idanunta "Na ma fiki,yau fa kwanana huÉ—u a Jigawa" tace "to zamu gani anjima" ya shafi wani sashe na jikinta tare da faÉ—in "kin min tanadi kenan? Ta ja shi ciki "kai dai muje ka yi wanka ka cika tunbinka, daga nan sauran labari ya biyo baya" Suna cin abinci ne yake bata labarin nemo abokinshi da ya yi, ta washe baki "kai na yi murna, yaushe ne za ka koma? Nima da na bika mun saba da Iyalinshi,ya ji daÉ—i don ba zata za ta mishi maganar da mahimmanci ba,don haka sai ya ce, "kada ki damu,ai tunda Allah yasa yanzun mun gano juna, mutuwa ce kurum zata raba mu.Shi yasa ma kamfanin da na je maganar shi, Allah ya yi mun daidaita ranar Monday zan tura musu kuÉ—in su, shi na ba kwangilar gyara kamfanin tare da É—ora shi Manaja in komai ya kammala. Nan take yaga fuskar ta ta sauya, sannan ta ce " ba fa a yiwa É—an adam saurin yarda,yanda mutanen duniya suka lalace da son kuÉ—i"
Ya aje cokalin hannun shi Sannan ya dube ina zaton na jima ina miki bayani halayen dattako tare da riƙe amanar da Friend ya ke da shi kar ki ji komai." Ta yatsina baki bata kuma magana ba,shi ko miƙewa ya yi don ya shiga ɗakinshi,ya warware gajiya. Yana shiga wayar shi ta soma tsuwwa,ya duba. Murmushi ya yi tare da ɗaga wayar.
"Friend na iso har na yi wanka, kuma na ci abinci yanzu ma ƙwanciya zan yi" a can Abba ya ce" to Alhamdulillah,na barka lafiya ka huta."
Umma ta dubeshi "Abban yara mene ne abin damuwa kan wannan? Ai abin murna ne sai muyi ma Allah godiya." Ya ce"haka ne Umman yara,ina tunanin amana ne,kin san amana tana da wahala,sai dai Allah ya taya mu riƙo" ta ce"Amin".
A'isha ta shigo da sallama ta zauna cike da fara'a,"Abba nagode da siyayya, gaskiya ban taɓa sa'ar samun guzurim zuwa makaranta kamar wannan ba." Ya yi murmushi,"Uncle ɗin ku ne ya ba da yace ai miki siyayya, " ta ce kai gaskiya Uncle akwai shi da kirki,ina jin tausayin shi gashi Allah be Baby ba" Umma ta ce"Allah zai ba shi insha Allahu" Abba ya miƙe domin zancan su ya yi mishi tuni ne da wani al'amari da ke gabanshi.
Zaune ya ke gaban Malam Dari,ya koro ma Malam Dari bayani kan matsalar abokin nashi,shi kan shi Malam Dari ya jinjina matsalar, sannan ya ce zai yi wasu bincike a kai, bayan ya tambayi sunan abokin Abba,ya ce mishi Alhaji Sadiƙ Usman,Malam Dari ya ce ka bani zuwa gobe ko dai ma jibi ka zo kaji batu,,ya miƙe bayan ya ajiye mishi dubu ɗaya, tare da faɗin "Ga sadaka" Malam Dari ya ce "to Allah ya karɓa,kuma ya shige mana gaba."sai na ganka" "to" inji Abba "sai na zo ɗin kenan."
___________________________
Ya yi parking a harabar gidan mahaifan nasa,ya fito É—aukacin masu hidima a gidan suna ta isowa don gaishe shi,shi kuma ya shiga amsa musu ya shiga yi musu ihsani, kamar yadda ya saba, duk sanda ya zo, sannan kai tsaye ya nufi falon Hajiyar mu.