← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ƙila zai neme ta. A'isha ta yi ajiyar zuciya,lallai ya kamata ta sanar da Umma, domin dai ba su san komai kan Uncle ba. Sai da Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki abinda ke damuna, amma sai kin yi min alƙawarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin fargaba Umma ta ce, "Sanar dani,ba zan gaya mishi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe Uncle ɗan yankan kai ne? Ashe duk kuɗin shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da cewa "Wane Uncle ɗin?" A'isha ta ce, "na Katsina, kinsan ƙawata ƴar Katsina ce nan dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da Uncle ɗin nata, Umma ta shiga damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya kuwa A'isha zancan nan gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta yi ƙarfin hali ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, domin dai duniya yanzu babu gaskiya, kuɗi suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum shi ko yana da nashi burin a kanka".

A'isha ta soma kuka tana faɗin, "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai taɓa yarda ba saboda ya yarda da Uncle ni dai na haƙura zan auri Uncle ɗin tunda dai dama na san ƙarshena mutuwa zan yi."

Abba da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin tun ɗazun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A ranshi ya ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke ɓoye musu,ya zama dole ya shiga ya sanar da su gaskiyar lamarin domin ya yarda Alhaji Saddiƙ ba zai mishi ƙarya ba,ba zai cuce shi ba,ba zai ci amanar shi ba, kuma ba zai kasance ɗaya daga cikin masu shan jini ba.

Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ƙarfin halin cewa "kuna hira ne? Umma cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da faɗin "lafiya dai ko? Umma ta ce "da sauƙi dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da yake yi kenan?" Abba ya ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddiƙ mana ta shiga jero mishi bayani yanda A'isha ta sanar da ita. A'isha dake ƙwance jikin Ummanta tana kuka,ta ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so ba, amma duk da haka zan aure shi.

Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da kansa ya yi min bayanin zargin da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya Jummai duk Mata da ya aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma ne? Duk sun rasu," A'isha ta zaro ido, Abba ya ci gaba da cewa, "ina so ku sani cewa, dukkan mai rai mamaci ne, haka nan matansa da suka riga mu gidan gaskiya,ku yarda wa'adinsu ne ya zo, batun yana yankan kai babu gaskiya cikin zargin da mutanan unguwar suke mishi."

Umma cikin matsananciyar damuwa ta ce, "to yanzun Abbansu matan nasa suna mutuwa haka za'a bashi A'ishan?.

Ya ce, "Haba Fatima,ya ya ki ke dawo da hannun agogo baya? Na gaya miki na sake gaya miki aure babu fashi, mutum baya mutuwa face ƙwananshi ya ƙare. Ya fita yana cewa "ki zo."

Ɗakinta ya shiga, Umma ta biyo shi jikinta babu ƙwari. Ya dube ta yace, "Haba Fatima,me zai sa kiyi min haka? Ke kin san son da nake ma A'isha,kin sani ba zan cutar da ita ba, aure bautar ubangiji ne, zan yi murna a ce ta mutu tana ibada,don haka ki natsu kuma ki ƙwantar da hankalin ki,ki bani goyon baya. Ki yaƙi shaiɗan mu tattaushe ta,nima wallahi ƙarfin hali nake yi,in tana ganinmu cikin damuwa zata kasa ƙwantar da hankalinta kullum zata zama cikin fargaba."

Umma ta ce, "Shikenan, zan yi yanda ka ce," ya ce "yauwa, addu'a kurum ita ce magani,ki tsaya tsayin daka da addu'a,ba dare babu rana. Itama A'ishan ki tsaya kanta ta dage da yin azkar safe da yamma. Cikin fargaba ta ce "To."

Sanda Umma ta shigo ɗakin A'isha, ta samu A'ishar tana zaune gabanta wayar ta ce tana ta ruri tsabar tsoro ya hana A'ishar ɗaga wayar Umma ta kalli fuskar wayar Uncle ɗina haka taga an rubuta nan take ta gane,ta cewa A'isha an sa shi mana? Ki natsu ki ƙwantar da hankalinki,ki mishi magana cikin natsuwa,kada ki ɗaga mishi hankali,kin ji?" Ta ce "Ina jin tsoron shi ne Umma" Umma ta ce "Daina tsoron shi, shi ba mugu bane sharri ne mutane suke masa, ɗauki wayar." Ta kai hannu zata ɗauki wayar, ta katse a karo na biyu.

Ya sake kira a karo na uku, Umma ta ɗauki wayar ta miƙa mata, hannunta yana rawa ta amsa ta danna green ta sa a kunne. Cikin muryar nan tashi mai natsuwa da hikima yace, "amincin Allah ya tabbata a gareki Humaira Beby". A'isha ta dubi Umma,harara Umma ta zabgo mata, sannan ta fita can gefen. Ya ce "kina jina ƴar Abba?" Ta daure, sannan ta ce, "Ina yini Uncle?" Ya ce, "lafiya lau,kin dawo lafiya?" Ta ce, lafiya lau, ya ce "Masha Allah" a zuciyarta kuma faɗi take, Allahumma kafihim bima shi'ita,tana maimaitawa tana sake faɗa,ya ɗan yi gyaran murya,ya ce "A'isha ina labari?" Ta yi shiru,ya ƙara sanyaya murya,ya ce "A'isha kina ji na?" Ta ce, "Umh" ya ce, "zan zo week end,tun Friday kin ji? Kamar ta ce A'a, sai kuma ta ce Umh, ya yi ƴar dariya sannan ya ce "to Bebyna,me da me zan kawo miki?" Ta ce,babu komai.ya ce Shikenan, sai na zo, tace, "To ka gaida Nafisa" cikin jin daɗi ya ce "ita kaɗai ban da Hajiyarmu?" Da sauri ta ce "har da su." Ta ƙosa ƙwarai ya gama maganganunshi, kamar ko ya sani, ya ce "to bari na ƙyale ki sai kin ganni ko?" Ta ce Uhum, ta riga shi kashewa,ana shi gefen bai damu ba zaton shi kunya ce.

Daran juma'a,sam A'isha bata runtsa ba, tama rasa tunanin da zata yi, duk da lallashin da Umma take mata, bayan sun karya, Umma ta matsa mata suka shiga kitchen don girka abin tarbar baƙo.

Sun gama sha biyu da rabi nan Umma ta bar ta ta haɗa mishi zoɓo da sauran kayan sha. Ta shigo falo ta ƙwanta kan kujera, Umma ta fito don zuwa kitchen ta ce har kin gama?" A'isha ta ce,eh, Umma ta miƙa mata waya ga shi yana ta kira ni ina wanka." A'isha ta amsa Umma ta koma ciki.

Wayar ta soma ringing. Ta tsurawa wayar ido, ita dai kullum ƙara tsoron shi ma take yi, amma ba ta da yanda zata yi dole ta ɗaga wayar tare da addu'a a can ƙasan zuciyarta. Sannan ta ce, "Salamu alaikum" ya ce "wa'alaikumus Salam, Beby ina ki ka shiga ne? Ina ta kiran wayarki?" Ta soma magana cikin in'ina, "ina....am......wannan ne a kitchen ne," ya yi ƴar dariya, "ni kike yiwa girki kenan?" Ta yi shiru, ya ce "ok,shiru yana nufin eh ne,to na gode. Yanzu haka na shigo Jigawa, masauki kawai zamu je, sai na iso kenan" ta ce,to, Ya kashe wayar.

Ta tsaya tana kallon wayar,daddaɗar muryarshi har yanzun tana yi mata gizo, murya mai cike da kamala kamar yarda fuskarshi take nunawa ta tuno suffarshi a fili ta ce lallai Uncle bashi da makusa in ban da na mugun halinshi koda dai su Umma suna ƙaryatawa.

Ta fito wanka tayo alwalla tana idar da sallar azahar mai ta shafa sama-sama saboda zafin garin ta zazzago farar hoda a hannunta,ta ɗan murza a fuskarta ko madubi ba ta duba ba,dama ita bata ƙwalliya. Don haka ba ta ma duba madubi,kai ita fa ko kaya bata da zaɓi duk wanda Abbanta ya sai mata sun yi,don tana saka kaya ne don suturta jiki ba wai don gayu ba, ta ɗaga aƙwatinta ta ciro kayan da ke sama. Wata atamfa ce ta mutanan Ghana, fara ce ta saka taje ta ɗauko abincinta,ta zauna tana ɗan cakula tana dai cin abincin ne amma hankalinta duk yana kan Uncle ganinta ƙila ma tun yau zai gama da ita. Jafar da Munnir suka shigo,suna cewa Umma ga Uncle ɗin mu ya zo yana waje yana waya. Umma ta ce, "tare da Abbanku su ke?" Suka ce "a'a shi kaɗai ne, amma Yaya Abdulrahman yana gurinshi, ta ce "Abbanku yau ina ga aiki ya mishi yawa ne,ko gida bai dawo ba, ina ganin daga Office ɗin ya wuce Masallacin juma'a.

Jafar ya fita waje,jim kaɗan ya dawo. "Umma Yaya Abdulrahman,ya ce ki bada makullin ɗakin baƙi" taje ta ɗauko, A'isha kam tana zaune kamar gunki tana jin su. Yaya Abdulrahman ya shigo, "Umma Uncle yana ɗakin baƙi ya ce yabi ta Ofis ɗin Abba,sun tafi masallaci, shima yaje ya yi sallah ya koma Ofis ɗin basu dawo ba shi ne ya zo nan gida". Umma ta ce, "bai kira wayarshi ba?" Yana ta kira bai samu ba sai yanzun. Umma ta ce, "To ai shi kenan, tunda ma ya sameshi. Ta leƙo falo "A'isha tashi ki je ki shirya mishi abinci,ki kai mishi." Jiki babu ƙwari ta tashi ta fita.

____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*ÆŠandano page 8*

*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT}:--1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account É—in namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*```

Babban tire ne ta shaƙe shi da kuloli masu ɗauke da kalolin abinci. Sai plate da cokali, da sallama ta shiga,ƙasan zuciyarta kuma tana maimaita addu'ar Allahumma kafihim bima shi'ita.
Chapter 8 · 0% Book details