Sashe 14
Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙwanƙwasa ƙofar tare da buɗewa ne ya katse ta,a hankali ya yi sallama tamkar yana ciwon baki,ko kuma baya son ya tashi ƙaramin yaro. Kanta na ƙasa ta amsa, amma bata ɗago kai ba,ya tako har gabanta ya tsugunna,sam bata ma san ya iso ba, sai dai ta ji yace Beby (a hankali) ta ɗago idanu ta zuba mishi. Yana sanye da wandon jeans baƙi da rigar sanyi tafkekiya ta saƙar baƙin zare da fari, sai ta ganshi tamkar ɗan matashin saurayi,ko kusa ba ya kama shekarunsa,ƙyawun fuskarshi ya sake fitowa saboda ƴar rama da ya yi,ta sauke idanunta ƙasa, hancinta yana ci gaba da shaƙar ƙamshinsa,ya yi ɗan murmushi yanda Bebyn tasa ke dubansa, cikin yanayin damuwa ya ce Beby baki ci abinci ba, saboda me? Ta gyara zama bana jin yunwa ne Uncle, ya ce Nafisa ta ce min kina cikin damuwa ko ruwa ba ki sha ba,why Beby? Kina fargaba ko? Ta ce ba haka ba ne Uncle, ya ce to gaya min ya ya ne? Ta rasa me zata ce, ya ce ok,kina tunanin cewa in kinci wani abu na gidan nan shi ne zaki mutu ko? Da sauri ta dube shi, Uncle ba na nufin haka, ya ce to in ba ƙya nufin haka ki ci wani abu in gani, ta ce to,ya ce me ranki yake so a kawo miki shi yanzun? Ta ce komai ma zan ci ba sai na daban ba, maimakon tsugunnon da yake sai ya zame ya zauna sannan ya kira wayar Uche. Ya ce ka kawo min kaza mai zafi in kuna dashi a kitchen da maltina ko fresh milk ya kashe wayar ya dubi gefe,su Naja ƙawayan naki sun yi bacci da sun taya ki ci ko? Itama ta dube su,sun gaji ne, ya ce dole su gaji don da nisa. Uche ya ƙwanƙwasa ƙofa, ya miƙe yaje ya amso tiren ya dire a gabanta sannan ya zauna, "ci in gani" nauyinshi take ji don haka sai ya kauda kanshi gefe ya ciro wayar shi ya soma neman wani layi, aka ɗauka suka ci gaba da hirar kasuwancinsu.ita ko nan ta soma cin kazar nan wadda ta ji haɗi ta kuma gasu, ta ci sosai ta sha maltina kaɗan sai ruwa. Ya dube ta har kin ƙoshi? Ta ce,eh ya ce yauwa to tashi kije ki ƙwanta zuwa ƙarfe uku in gajiyar mota ta barki sai ki tashi kiyi alwala ki yi nafila ki tsananta roƙon Allah ya albarkaci aurenmu, ta ce to, kanta na ƙasa ta tashi ta hau gado ta kwanta tsakiyar su Naja ya ce sai da safe,kizo ki rufe muku ƙofa kiyi addu'a fa,ta ce to. Bayan ta karanta ƙulhuwallahu,falaƙi da Nasi,ta tofa cikin tafukan hannayanta sannan ta shafa tun daga kanta da fuskarta har da sauran gaɓobin jikinta,ta yi haka har sai uku ta karanta Ayatul kursiyu.....
######
[12/5, 20:22] Ummi Tandama😇: *📗Page 13*
Amanar rasulu, sannan ta karanta da sunanka ya Ubangijina na ƙwanta kuma da izininka ne nake tashi in ka riƙe raina da (mutuwa) to ka ji ƙanta in ka sake ta ya Allah ka kiyayeta da abinda ka ke kiyaye bayinka salihai da shi, sannan ta ce:--
Allahumma innaka kalaƙta nafsi wa'anta tawaffaha naka mamatuha,wama hayaha in ahyetaha,fahfadha wa'in amattaha,fagfirlaha. Allahumma inna as'alukal afiya,tana koyi da Manzon Allah (S.A.W) in tazo ƙwanciya sai tasa hannunta na dama ƙarƙashin kuncinta ta ce:--
Allahumma ƙiyni,azabaka yauma tab'asu ibadaka. Sau uku, sannan ta ce bismikallahumma a mutu wa'ahaya. Lokacin ta soma hamma sosai don haka sai ta tsaya nan gurin ta kuma ƙwanta.
Shigar Alhaji Saddiƙ ɗakin da fitarshi kai har zuwan Uche duk a kan idanunta ne. Hajiya Jummai ta yi ƙwafa sannan ta ce lallai ban da yarinyar nan mutuwa zata yi ƙila da na ƙunshi takaici gidannan,dubi yanda mutumin nan ke ta faman sintiri a ɗakin yarinyar nan tun baƙi na nan,ta ciji yatsa tare da cewa kash, da na sani da har ƙawayan nata na ce su je can shi ko nasan da nan zai ƙwana ba kuma zai bar ta ba,in ya so tana mutuwa suyi zaman makokinsu gaba ɗaya an huta,su koma Jigawa su dawo, amma tunda an riga an yi haka shi kenan,sun dawo ɗin tunda ya kama su ne.
Washegari tuni tasa Uche a dama koko ga ƙosai. Rahina mai aiki tana ta suya. Sai ga ƴan aikin Hajiyarmu tare da Nafisa ɗauke da ruwan zafi gwangwanayan madara milo suga da kuma ƙatuwar kula mai ɗauke da soyayyan dankali da kuma ƙwai. Sanda su Sofy da Suby suka shigo ɗakin babu ko sallama suka aje bokitin koko sun same su suna ta wadaƙarsu da shayi sororo suka tsaya sannan suka fita suka koma gurin Jummai in da take ce ma Rahina rage ƙosai ƴan ƙauyan banza shiyasa na ce ayi musu koko tunda shi suka sani, Suby ta ce Hajiya ai ba zasu sha koko nan ba, domin tea da ƙwai suke ta bikin sha.
Hajiya Jummai ta dube su,a ina suka same shi? Sofy ta ce,oho ƙila daga gidan waɗancan tsegumammun ne, gidan su Hajiyarmu. Hajiya Jummai ta suri ƙwanon ƙosai ta nufi ɗakin baƙin,tana shiga sai ta saki fara'a sannunku da tashi baƙi, suka ce yauwa ina ƙwananmu? Bayan sun gama gaisawa sai ta ce, to ga ƙosai nan da koko in zaku ƙara dashi, domin naga abin marmari ne na ce ayi muku, suka ce to mun gode, sai dai gashi duk mun ƙoshi gara ma ƙosan ma ɗan taɓa, Allah dai ya baku zaman lafiya.
Hajiya Jummai ta fita tana faÉ—in amin a baki, amma a cikin zuciyarta tsine musu take yi.
A ranar ne aka yi buɗar kai suka gyara mata ɗaki sosai, sannan suka shirya ta suka kaita gidan Hajiya Babba inda suka danƙa amanarta gurin Hajiyan, sannan suka dawo in da dangin nashi suka tara mata kuɗi daga nan aka kaita gurin Hajiya Jummai wadda ke hakimce tare da ƙawayanta, itama ance ga amana nan ta kuma ce ta amsa tare da cewa Allah ya taya ta riƙo,wata cikin ƙawayan nata ta ce ba a karɓar amanar kishiya fa Jummai. Hajiya Jummai ta ce ke daina gaya min wannan zancan,ai jahilan mata ne suke wannan abin yarinyar nan na ɗauke ta ƴar'uwa Allah yasa ki haifa mana ƴan dagwai-dagwai a gidan nan, suka ce amin,ta miƙo rafar ƴan ɗari bibbiyu to gashi ƙanwata. Nan aka shiga godiya kowa yana yabonta cikin dangin amarya.suka maida ita ɗakin ta,nan suka ƙara yi mata nasihar ta bi mijinta da matarsa, sannan ta bi danginshi ga dai shi ta gani kowa sonta yake yi. Suka shiga shirya kayansu,nan fa A'isha ta soma kuka suna ta lallashinta.
Hajiya Jummai ta fito da tiraman zannuwa goma sha huɗu ta basu wai suyi tsaraba, nunawa ta yi itace ta basu alhalin Alhajin ne ya bada kuɗin da zannuwan,tirmi ishirin, sannan ya bada ne kan Naira dubu uku uku ta siya ƴan dubu da ɗari bibbiyu,su dai suna ta godiya. Lokacin da suke shiga motoci ne a harabar gida motarshi ta shigo, kusa da su ya ce direban ya tsaya ya fito,yana cewa ina ce sai gobe ko jibi zaku tafi? Suka ce an gama komai Alhaji gara mu je gida dama ƙwana ɗai-ɗai muka ce zamu yi,ya ce to Allah ya kaimu da alkhairi, kuma ya sauke ku lafiya. Ya dubi direbanshi bani kuɗi nan in da na zauna,shi kan shi bai san ko nawa bane ya dai san ƴan dubu ɗai-ɗai ne. Suka ce har da wahala haka? Dama ka barshi gashi ma Hajiya ta bamu zannuwa, ya ce ku ƙara, suka ce to mungode Allah ya sa muzo suna haka, ya ce amin. Nan dai suka ɗau hanyar Jigawa suna yabon waɗannan mutanan.
Shi ko ɗakin amarya ya nufa domin ya san yanzun tana cikin damuwa,hakan ce kuwa ya taradda tana ƙwance tana ta shirga kuka na fitar hankali. Da sauri ya isa gaban gadon,ya zauna a bakin gadon, tashi mana Beby ta so ki gaya min zaki bisu ne? Tashi inji" ta tashi zaune,ya ce kina son ki bisu ne? Ɗaga kai ta yi alamar eh, yace"to taso ki ɗakko hijabinki" ta share hawayenta,ta zauna tana ajiyar zuciya. Ta kasa tashi,ya ce "to muje Beby kada su tafi," ta ce "Abba zai min faɗa har da Umma" ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce to kiyi shiru,in naga kin kwantar da hankalinki zan ɗauke ki muje in kaiki,in da ni ne zasuyi miki faɗa? Ta ce a'a ta sake yin ajiyar zuciya sannan ta ce in dai ba zaka ce musu ina kuka ba,to baza su yi min faɗa ba,ya ce ai kafin muje ma kin daina kukan ko baki daina ba? Cikin shashshekar kuka ta ce na daina, wasu hawayen suka sake zubowa,ya ce a'a to gashi kina yi kuma? Ta ce to na daina, ya ce wai ba ki son gidan ne? Ko kina ganin za ki mutu ɗin ne? Ta ce ba haka bane, ina tuno su Umma ne da su Jafar.
Ya ce,ba ki ce da Abdulrahman ya gaida su ba ne? Ta ce na gaya mishi,ya ce to ki daina kukan kin ji ko? Da ƙyar dai ya shawo kanta ta yi shiru kusan awa ɗaya da rabi yana lallashi, lokacin ne aka yi kiran magriba sannan ya fito bayan tayo alwalla,sai da aka yi issha sannan ya dawo lokacin ma yayo wanka yana sanye da jallabiya mai ruwan toka mai gajeren hannu.