Sashe 15
Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana riƙe da jakar laptop da wayoyi ya shigo ɗakin da sallama,tana zaune kan sallaya kanta yana ƙasa kewar gida ce ta cika ta har ma hawayenta suke zuba. Jin sallamarshi ta miƙe da sauri tare da share hawayenta. Ya tsura mata idanu, sai ta sunkuyar da kai ya isa kujerar da ke gefen gadon ya aje kayan hannunshi sannan ya zo kusa da ita. Beby! Beby! Har yanzu dai kukan ne? Ta ce a'a ai na daina,ya kama hannunta ya zaunar da ita bakin gado, sannan ya ce sanar dani me ke saka ki kuka ne? Ta ce, tunanin gida kawai nake yi,ya ciro waya bari na kira Abban,bata san lokacin ta riƙe hannunshi da sauri ba,ta ce Uncle don Allah yi haƙuri kada ka kira shi zai min faɗa,ya ce to shikenan kin ci abinci? Ta ce na ƙoshi ne. Nan dai ya yi wa Uche waya ya ce kada ya shirya mishi abinci a dinning,ya kawo mishi ɗakin amarya,nan yasa ta shinfiɗa mishi babbar darduma.
Uche yana kawo abincin ya shirya mishi a kai ba tare da neman izini ba,ya ce zo nan muci abinci,ta kalleshi ganin fuskarshi É—inke sai ta je,ya jawo plet ta amsa cikin natsuwa ta buÉ—e kulolin,tuwan shinkafa ne da miyar agushi, sai dafadukan taliya mai haÉ—e da kayan lambu.
Ta ɗago ta dube shi, kafin ta yi magana ya duk wanda ki ka ga ya yi miki a ranki sa mun. In to bashi ranka ke so ba fa? Ka ci dai duka, cikin natsuwa ta ke maganar ya ce ɗaya zan ci kuma ke ce zaki zaɓar min da abinda ya dace in ci matsayin abincin dare, ba ta kuma cewa komai ba ta janyo plet ɗin ta saka tuwo da miya sannan ta saka cokali ta aje mishi a gabanshi. Ta tsiyaya mishi ruwa da jus,itama kaɗan tasa tuwon tana yin loma ɗaya sai ta ji babu wani ɗanɗano duk da ƙamshin da ya cika ɗakin amma haka ta daure tana ɗan tsakura. Amma shi yana ta cin abinsa da alamu ya saba da shi, wayoyinsa suka soma ringing lokaci ɗaya ta miƙe ta ɗebo mishi su, sannan ta koma gefe ta sha ruwa ta zauna tare da tsura ma guri ɗaya idanu da alamun ta faɗa cikin tunanin nata,kusan minti talatin yana amsa wayoyi, sannan ya kira Uche ya kwashe kayan ya dubi A'isha, "Beby tunanin ko?" Ta sunkuyar da kai ya miƙe ya isa gurin T.V wanda ke manne a jikin bango ya kunna sannan ya shiga neman tasha,MBC 3 yasa sannan ya dube ta ga irin naku ko Beby? Ta kalla Cartoons suke yi na Tom & Jerry tana son cartoon,sai dai ta kula shi Uncle ya maidata wata ƴar mitsitsiyar Yarinya. Nan ko ta gyara zama ta shiga kallonta, shi ko ya jawo laptop ɗin shi ya shiga al'amuranshi na kasuwanci daga bisani ta ji bacci yana fizgarta,don haka ta hau gado bayan tayo alwala ta zauna ta jero addu'o'inta sannan ta kwanta bacci kuwa ya yi gaba da ita,sam bata tare da fargaba irin na amaren nan game da angwayensu, uku dai-dai ta farka har lokacin yana gaban laptop alwalla tayo ta zo ta soma na filfilu, hankalinshi ya yi nisa sai daga baya ne ya ji motsinta, nan shima ya yo alwalla.
Hajiya Jummai tana da tabbacin ango ya kwana É—akin amarya fatan ta dai Allah yasa sun sadu .
Da safe har ɗaki A'isha taje ta gaida Hajiya Jummai ta same ta tare da su Sofy, cikin fara'a ta amsa ma A'isha, sannan ta ce dasu Sofy ba za ku gaida Antyn taku ba? Har suna haɗa baki gurin jan tsaki, haka da A'ishan ta gani yasa ta gaishe su ba su amsa ba, A'isha ta fito tana tunanin su kuma waɗannan su wanene? Tana shiga ɗakinta ta soma gyaran gado,ta gyara ko'ina sannan ta shiga toilet tana wankewa ya shigo cikin shirin fita motsin da ya ji a bayin ya sa shi tsayawa ya san tana ciki,jim kaɗan ta fito. Ya ce na zaci wanka ki ke yi? Ta ce a'a ina wanke bayin ne. Ta durƙusa ina ƙwana? Ranshi ya yi fari sannan ya ce lafiya lau tashi na gode. Ya ci gaba ni zan fita ne don Allah kada ki yi kuka ko tunani sannan ki ci abinci kuma wannan aikin da ki kayi yanzu akwai masu gyaran ɗakunanku. Zan sanar da ke komai sai in na dawo yau da yamma zan haɗa ku da Jummai, ta ce to, har ya soma tafiya ta ce Uncle ka....sai kuma ta yi shiru,ya dawo har kusa da ita, nayi me? Sanar da ni mana. Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta sannan ta ce ina nufin kayi break fast ne? Ya yi murmushi, abinda Hajiya Jummai ba ta taɓa damun kanta a kan ya yi ba kenan, haka gaisuwar da A'isha ta yi mishi ya sa shi jin cewa shi ɗin maigida ne. Ya ce A'isha bana yin break a gida saboda baƙwa karyawa da wuri ni ko bana son mutane su yi ta jirana a Ofis," ta ce "to acan ana saida abu ne? Ya ce zan sha copee a Ofis da rana kuma muna kusa da gidan cin abinci," ta ce "to sai ka dawo Allah ya bada Sa'a" ya ce amin Bebyna,na gode miki kiyi kallonki kin ji? Zan kira ki" ta ce to,ya fita ta bishi da kallo. A zuciyarta tana tunanin duk in da Abbansu za shi komai sauri sai Ummanta, ta mishi Abinda koda ba zai ci ba saboda sauri zai riƙe.
######
[12/6, 07:59] Ummi Tandama😇: *📗 Page 14*
Shi ko ya fito ne yana jin daɗin yanda A'isha ta nuna kulawarta kanshi, ƙaramar yarinya kenan. Sai sha ɗaya sannan aka kawo mata abin kari tea kawai ta iya sha domin hatta dankalin ɗanɗanonsa bai mata ba.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi tana zaune kan abin sallah tana karatun Alkur'ani tun bayan da ta idar da sallar azahar, Hajiya Jummai ta shigo tare da ƙawarta Karima, ta miƙe tana musu sannu duk cikin fara'a suka amsa. Karima ta ce wayyo ashe ma yarinya ce ƙarama.
Ita dai A'isha kanta yana ƙasa. Jummai ta ce eh, yarinya ce,sai wayar Jummai ta soma ringing sai ta fita ina zuwa bari in yi magana Alhaji ne ya kira ni ku gaisa ina zuwa,tana fita Karima ta matso kusa da A'isha, "yarinya ni dai zan miki nasiha ne ki riƙe mijinki ki mishi biyayya, kada ki zama cikin irin matan nan masu gudun miji,kin ga haihuwa yake so kiyi maza ki cika mishi gidan da ƴaƴa kin ji?" Zancan ya yi ma A'isha nauyi,don haka ta kasa ɗago kai, sai dai ta kaɗa kai alamun to. Ta ƙara ƙasa da murya,kin ga dai kishiyarki aminiyatace ko? To wannan ba zai sa in kasa gaya miki gaskiya ba, ita bata so kowace mace ta haihu tunda ita bata haihu ba,don haka zatayi ta zuga mijinku kan cewa kada ya kusance ki,ke yarinya ce in kin ji tana haka ki mata shiru, amma da lokacin ƙwanciya ya yi ki tafi gurin mijinki kin ji? Sai Hajiya Jummai ta turo ƙofa tare da sallama, sai Karima ta ja baya alamun bata son Jummai ta ji, amma yanda A'isha taga sanda suka haɗa ido suka yi wata alama da gira sai jikinta ya bata cewa ƙila sun shirya wani abu ne.
Yinin ranar ta amsa wayar Uncle kusan sau taƙwas, duk dai dan yaji halin da take ciki. Ta kira Umma da Abba da kuma Yaya Abdulrahman, shida saura ya shiga ɗakinta amma daga gani ya fara zuwa ɗakinshi, domin ya canza kayan shi daga suit zuwa jallabiya fara kar. Ta ce sannu da dawowa,an dawo lafiya? Ya ce lafiya lau Beby,ba dai wata damuwa ko? Ta ce eh,ya ce to bari muyi sallah, ta ce to. Wanka tayi tasa riga da siket na atamfa,bata damu da yin wata ƙwalliya ba, domin shafa wannan shafa wancan ba damuwar ta bane. Ta yi sallah tare da nafila raka'a biyu,ta zauna tana yin azkar ɗin yamma. Ayatul kursiyu ake fara karantawa, sannan falaƙi da Nasi da ƙulhuwallahu, sannan ta ce "am saina wa amsalmulkulilahi Rabbana as aluka khairan mafiy hazihil lailati wa khaira ma ba a daha,wa'a uzubika min sharri mafi hazihillailati wa sharri ma ba a daha, sannan ta ce:-
Allahumma bika amsaina wa bika asbahna,wabika nahya wa bika na mutu,wa ilaikal masir.
Allahumma anta rabbii laa ilahaaha illa anta kalaƙatani,wa'ana abduka wa anna ala ahdika wawa'aduka mastaɗa'atu a'uzubika min sharri ma sana'atu abu'u laka bi ni'imatika alayya wa abuu'ubi zanbi fagfirlii fa innahu la yagfiruz zunuba illa anta.
Haka ta yi ta kawo addu'o'i har zuwa isha'i ta yi sallah tare da yin shafa'i da wuturi,tana zaune tana tasbihi, Uncle ya shigo da sallama. Ta amsa, sannan ta yi mishi sannu da shigowa, ya amsa ya ce in kin gama zo muje,dama ta gama ta yi addu'o'inta ta shafa shima ya shafa tare da cewa Allah ya karɓa ta yi ɗan murmushi sannan ta ce Amin. Ya ce me kika roƙar mana? Ta dube shi, sannan ta sunkuyar da kai ta ce alkhairi, ya ce kin sani a ciki? Ta dube shi, "na manta" ya ce "to daga yau in kin yi sallah ki dinga saka ni cikin addu'arki, Allah yana saurin amsar addu'ar mace a kan mijinta, haka nan ta mijin akan matarsa. Ta ce to, ya juya zo muje, ta bishi suka ratsa falon shiga cikin wani labule, sai ga gurin cin abinci,dinning ne na glass mai kujeru shida,can gefe ga wani mai kujeru taƙwas,gurin ya tsaru gwanin sha'awa.
Hajiya Jummai ta shigo ta wata ƙofa bata hanyar da suka biyo ba, ashe kitchen ne, da fara'a ta shigo,ta dafa A'isha wadda tunda ta shigo ta soma jin wata muguwar faɗuwar gaba,ta rasa dalili duk lokacin da Hajiya Jummai ta zo inda take sai gabanta ya dinga wata muguwar faɗuwa.
Hajiya Jummai ta ce, ƴar ƙanwata kin fito? Cikin in-ina A'isha ta ce, in in ina yini? Jummai ta zauna tana cewa, lafiya lau, Alhaji Saddiƙ ya yi murmushi sannan ya ce,gata nan sai kunya da tsoro,dubi yanda duk ta rikice daga shigowar ki.