← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zauna kusa da Umma ,kuma ganin Abban nasu ba da alamun wasa ba,yasa ta nutsu ta san magana ce mai mahimmanci zai mata,kila batun komawarta makaranta ne nan da kwana hudu,ya katse mata tunaninta da fadin "Aisha" ta amsa "na'am Abba." Ya ci gaba "ina son zan miki wata magana,sai dai ina shakka." Cikin mamaki ta dube shi,sannan ta ce "Shakka Abba?" Ta ci gaba "bazan so in zama 'yar da iyayenta za su rinka shakka a kanta ba,domin bani da burin bijire ma umarnin ku,ko haninku,ka fadi ko ma me ka keson fada ba tare da shakka ba." Ya numfasa tare da jin dadin maganar ta,sannan ya furta zancan zan miki aure ne." A tsorace ta dube shi,domin batayi zaton faruwar haka ba,amma sai ta dake ta kuma hadiye wani abu da ke taso mata ,ta ce "to Abba." Ya ci gaba "kuma Alhaji Sadiq wanda yazo daga katsina,shi na zaba miki." Kanta na kasa ta ce "to" Ta dube shi kamar zata yi magana,amma tana jin da ta bude baki hawaye zai zubo mata,don haka sai ta yi shiru.

"Ki yi magana mana." In ji Abba,don ya fahimci tana son ta yi magana ne ta fasa.Sai ta yi dan murmushi sannan hawayen data ke makalewa suka zubo,ba ta share ba,ta ce "dama zancan karatu ne zan yi sai kuma na tuna cewa ai babu sauran karatu."

Tausayinta iyayan suka ji,Abba ya ce " insha Allahu za ki ci gaba,yanzun ma zaki koma kafin mu tsaida lokaci,ina so ne dai ki sani,ta ce "to" ya ce " tashi kije,Allah yayi miki albarka."

Wanka ta shiga,amma zama ta yi a bayi ta kasa wankan,tunaninta shin mene ne dalilin Abba na aurar da ita bayan ya yi mata alkawarin zama Doctor? Kuka ta yi sosai cikin bayin,tana tausayin kanta, Ta sani duk yanda aka yi Abba yana da dalili mai karfi na yin hakan gare ta,sai dai ta sani ba yana nufin cutar da ita ba ne,ba ta taba soyayya ba,ballantana ta ce bata son shi,ta sani dole ne ta girmama shi musamman in ta tuna taimakon da ya yi ma mahaifinsu,gashi mai kyau da kuma tsafta,ma'abocin kamshin turaruka,ta tuna san da yazo suke falo kamshinsa ya cika gidan ko ina,sam bai yi kama da shekarunsa ba tamkar wani matashi dan shekara talatin,daga karshe dai tayo wankanta ta fito,ko a daki lallashinta Umma ta kara yi,kan cewa kada ta damu.

___________________________
Hajiya Jummai tana zaune bakin gadonta kafarta daya kan daya,tunanin ta yana can Jigawa ita kam sam ba ta so ba,Alhaji ya yanke hukuncin bawa abokin shi Manajan wannan kamfanin ba,bayan ta jima tana mishi maganar kaninta,bataso ta ga wani kusa da dukiyar mijinta domin duk abinda ya tara nata ne,tunda ba d'a gareshi ba,don haka dole ta kula da dukiyar ta,ta san kuma tunda shine gaba da ita zai rigata mutuwa,dole ma ta san matakin dauka kan wannan kamfanin bari dai ta bari a gama gyaran.

Dai dai yayi parking wayarshi ta soma tsuwa,ya duba Friend ya furta,sannan ya dauka.

"Assalamu alaikum,Friend mun wuni lafiya?"

"Lafiya lau Friend.Alhaji Saddik ya fada.

"Yarana suna lafiya?"

"Lafiya qalau,batun aiki ne nake son ce maka an kusa kammalawa,sannan sai batun taimakon da na ce maka zan nemo game da matsalarka. Da fatan kana da lokaci zan maka bayani." Alhaji Saddik ya ce " ina jinka,ni kadai ne." Abba ya ci gaba...

[11/30, 07:51] Ummi Tandama😇: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*ÆŠandano page 4*

"Bayan Istihara mun ga alkhairin aurenka da wata yarinya,zan so ka samu lokaci ka zo," Shiru Alhaji Sadiƙ ya yi,can ya ce, "Friend na haƙura da duk wani aure yanzun, mutane sun camfani da yawa,ba na son ƴaƴan mutane su yi ta mutuwa a hannuna....." Abba ya katse shi "kai dai in ka samu lokaci kazo." Yace,"shikenan,na gode."

Sai da ya sauka masauki ya huta sannan ya yi ma Friend ɗin shi waya cewa yana nan a Dutse fa, Abba yace "ka min bazata fa,to bari inzo in same ka inda ka sauka wancan karon ne?" "Eh,nan ne" inji Alhaji Sadiƙ. Ya idar da sallar la'asar yana jan carbi, Abba yayi sallama ya shigo, Alhaji Saddiƙ ya tare shi cike da fara'a tare da yi wa juna musabaha, suka zauna. Sun gaisa Alhaji Saddiƙ yace "Friend ina yaran nawa,sun koma karatu hutu ya ƙare ko?" Abba yace, "Sun koma,ya ya Madam?" "Tana lafiya" inji Saddiƙ, tace in gaishe ku,(ya ari bakinta ya ci mata albasa). Ya ci gaba,"Naso ince ka zo min da zoɓon nan da nasha a gidan ka"Abba ya yi ƴar dariya,"ai na zata gidan ma zamu je yanzun," inji Abba, "Na fi son mu gama magana a nan shi yasa na sauka,yi man bayani Friend danni fa bana son yanda ƴan garinmu suka shiga tsorona,nan ma in shiga wannan halin" Abba yace "bari dai in baka labarin komai ."nan ya koro mishi bayanin yanda suka yi da Malam Dari, Alhaji Saddiƙ bai ji mamaki sosai ba, saboda ya san ita ce shima ya sha ganin ta cikin mafarkinshi.

Ya dubi Abba, "Friend ban sha mamaki ba, saboda ran da naga yarinyar nan na san cewa ita ce nake gani cikin mafarkina, amma hakan ba zai sa in aureta ba,sam ba zan zama sanadin mutuwar ƴarka ba,bayan haka ma da kunya in auri ƴarka,ai ƴata ce, kuma da kunya sa......." Abba ya ɗaga mishi hannu alamar yayi shiru, sannan ya ce "amma ka san cewa bai saɓa ma Shari'a ba ko? Hasali ma wata sunna ce mai ƙyau ta Manzon Allah (S.A.W) muka yi koyi ko? Ka manta Sayyidina Abubakar (A.S) babban abokin Manzon mu ne, sannan ya aura mishi ƴarsa Nana A'isha, Allah ya yarda da ita,Tana da ƙarancin shekaru, shi kuma ya soma manyantaka,sam wannan ba abin kunya ba ne kamar yanda wasu ke faɗi."

Alhaji Saddiƙ ya ce "Friend yariyar nan ƙarama ce, bayan haka mu duba irin yanda mata suke mutuwa a gidana...." Abba ya sake katse shi da cewa "kai ne ka ke kashe su?" Alhaji Saddiƙ ya girgiza kai, "To!" Inji Abba,"ƙwanansu ne ya ƙare itama in nata ƙwanakin suka ƙare ko ba a gidanka ba dole ta tafi, batun ƙanƙanta kuwa wannan ba wani uzuri ba ne, iyayenmu ko shekarunta ba su kai ba,me ya same su? In dai baka sonta ne shi kenan."

Alhaji Saddiƙ ya dafa kafaɗar Abba "ba za ka taɓa haihuwar ƴa in ce bana sonta ba,na amsa kuma ban san bakin da zan iya maka godiya ba, saboda kai masoyina ne, cikin kowanne hali,in ba mai sonka ba,wanene zai yarda ya kai ɗansa mahalaka,don ni da kaina sai in rinƙa ganin tamkar gidan nawa mahalaka ce, Allah ya yi maka sakamako ya sa itace sanadiyyar warwarewar al'amurana."

"Amin" inji Abba. "To yanzun yaushe ka ke son matarka?"

Alhaji Saddiƙ sai ya samu kan shi da jin nauyin Abokin nashi,ya yi shiru, Abba ya dube shi "Don Allah Friend kada ka ji komai,ba wata kunya" Alhaji Saddiƙ ya ce "abin ne sai yana ba ni mamaki, ashe zaka haifi ƴa ni kuma in aura?" "To ai abin Allah ne," inji Abba,"yanzu dai yaushe ne za ka turo sai a saka rana in ta dawo hutu ayi bikin in ya so zan roƙi alfarma koda je ka ka dawo ce don Allah ka yarje mata,don tana son karatu,burinta shine ta zama Doctor."

"Don wannan kada ka damu Friend, insha Allahu ba tun turowa daga naje zan masu Alhajinmu bayani." Daga nan suka ci gaba da hirar aikin gyaran kamfani, bayan sun gama tare da cewa su zo su je gidan nashi, Alhaji Saddiƙ yace"an ya sai nake ganin yanzu kamar gidan zai min wuyar zuwa" Abba ya miƙe "to tashi muje ku gaisa da yarinyar,don tuni na yi mata bayani" Alhaji Saddiƙ ya dubeshi da sauri "Ta amince?" Abba ya yi murmushi "A'isha ba ta musu ko gardama,ƙwarai zaka ji daɗin zama da ita,ko dana sanar da ita ba ta yi musu ba, amma ta yi zancen karatunta,in kaje yanzun ka ga sai ka shaida mata karatun nata yana nan, insha Allahu" "to na gode,sai dai in har bata so dole ne mu bar wannan maganar," murmushi kawai Abba ya yi, sannan ya miƙe tare da faɗin "shiryo mu je, bari na yi waya" ya fita. Umma ya kira ya ce mata ga su nan zuwa su da Alhaji Saddiƙ, kuma yana buƙatar zoɓo mai ɗan sanyi.

Falon Abba suka shiga Umma ta leƙo sun gaisa tare da tambayar Iyalan nashi da kuma su Hajiyarshi,ya ce duk suna lafiya,ta koma kicin inda A'isha ke harhaɗa abinci kan babban tire. Umma ta ɗauka tare da faɗin "Shiryo musu zoɓon bari na kai wannan." Tana direwa Abba ya dube ta, "Ni fa dake zaki haɗa min,Ummansu shi Friend sa mishi nashi shi ɗaya, wannan zuwan ba nawa bane,na ƙawallinki ne." Murmushi Umma ta yi,ba ta ce komai ba ta fita. Ta isko A'isha kicin tana ƙoƙarin fitowa,ƙasa-ƙasa ta yi mata magana.

"Ki natsu ban da wauta, Alhaji SaddiÆ™ zai yi magana da ke,kada ki ba Abbanku kunya." Ta ce "to" dama tsaf take. Ta nufi falon Abba,ta yi sallama ta shiga.

Daddaɗan ƙamshin sa ya gauraye falon, ta ɗan saci kallon inda yake yana sanye da wani farin shara-sharan yadi wanda har ana iya ganin bes ɗin shi ta ciki. Ƙyan yadin ne ya bayyana tsadar shi,hular shi ƙube ce wadda aka yi ta da farin zare. Ta dire tire sannan ta zauna ƙasa,kanta sunkuye ta ce, "Ina yini Uncle?" Tun shigowarta ya ke kallonta, duk da cewa sanye take cikin hijabi bai hana shi ganin rashin jikinta ba, shi kanshi tausayinta ya ji ya amsa da cewa, "lafiya lau ƴar Abbanta." Ta miƙe ta soma ɗauko plate don zuba mishi cous-cous, ya ce "bar shi Nana A'isha,ba ni zoɓon nan nasha bana jin yunwa," ta ce "to" ta soma zuba mishi cikin kofi ta rage tsawo ta bashi,hakan ya burge shi, sannan ta koma mazaunin ta ya dube ta,ke ce kikayi wannan zoɓon?" Ta ɗaga kai alamar "Eh" ya kuma kafa kofin a bakin shi ya shanye ragowar na cikin kofin.
Chapter 4 · 0% Book details