← Book details Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Kari da Jummai cikin motar Hajiya Kari, ita da kanta take jan motar suna hirar yanda zasu tsara mutuwar Amaryar ta Alhaji Saddiƙ,waton A'isha. Hajiya Jummai ta ce "kin san Allah Hajiya Kari, (ta cigaba) wannan karon sati ɗaya nake son a aika yarinyar nan barzahu, domin duk cikin matan da ya yi,yayin auren ban taɓa jin kishin wata ba kamar wannan". Kari ta dube ta "menene na ɗaga hankali,yarinyar da ƴan ƙwanaki za ta yi ta sheƙa barzahu, har ki ke damun kanki." Jummai ta yamutsa baki,"ina mugun jin takaicin yanda ya damu da yarinyar, duk abokansa ya bi ya sanar da su alhalin da a ɓoye yake aurensa, sai in amaryar ta mutu sannan su ji, amma wannan fa shi da kanshi yake buga musu waya yana cewa,zai yi aure su taya shi da addu'a,ke wani takaici ma sai suna waya da yarinyar in kin ji yanda yake ƙara saisaita murya zaki sha mamaki." Hajiya Kari ta ce, "dama ga muryarshi kamar ta mata,anya ma ba salabane yake yi kuwa?" Jummai ta ce,"shi dai ya sani,ni yanzun damuwata ba ta wuce ya Boka na kan Dutse ya ganni ba. Kari ta ce "a'a kada ki damu,zai ganki ɗan iska nufin shi zai rama wulaƙancin da mukayi mishi na aikin ƙarshe da ya mana na ƙin sai mishi motar da ki kayi?" Jummai ta ce "shiyasa yanzun na taho mishi da makullin motar su Suby,don ba zan sai mishi sabuwa ba,yana kan tsauni ban da iskanci me zai yi da wata mota?" Kari ta ce "saka ai mata penti ki bashi ya ƙarata da ita". Jummai ta ja tsaki,"Ni tunanina me zan ce ma Alaramman nawa in ya ce ina motar su Suby?" Kari ta ja tsaki, "Jummai kina bani haushi,mu da muka nufi gurin masu biyan buƙata cikin gaggawa shakkar me zakiyi,ai ki sa a rufe mishi baki yanda ba zai tuna motar ba,su kuma shegun yaran masu ɗan iskan rawar kan tsiya sai kurum ki ringa haɗa su da na Mashinko direba ya dinga kai su."

https://hikaya.bakandamiya.com/muazzam-babi-na-daya/

*💃💃💃💃💃Wata garabasa sai tsarin bakandamiya ki sayi littafi daya ki samu damar karanta littafai sama da arba'in,akwai litattafan manyan marubuta kamar su RUFAIDA UMAR,LUBNA SUFYAN,MAIMUNA IDRIS SANI BELI,FATIMA DAN BARNO da sauran su,yi kokari kada wannan garabasa ta wuce ki akan naira 500 kacal,wacce take bukata ta yi magana ta wannan number 09068032427*

____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*ÆŠandano page 9*

Jummai ta ce, "sun raina Tinau direba, kullum rigima shi yasa fa Alhaji ya sai musu ta su", Kari ta ce "ƴan iska to su fito da miji mana ki musu aure,ki huta can sa ƙarasa karatun a ɗakunan su" Jummai ta ce "yaushe suka nutsu har zasu samu mazan ƙwarai? Sai dai masu rarake su kuma ƙanana sa'o'insu.

Kari ta ce,"nima gidana matsalar kenan,Safina tamkar ƴar Akuya ko ince karya maza wannan ya aje wannan ya ɗauka". Jummai tasa dariya, sannan ta ce bata yar ba,kin tuna lokacin muna school?" Kari ta ce "kema ai Allah ne yaso ki gurin cire cikin da Mr.Joseph ya yi miki,mahaifarki ta nakasa,da ba don haka ba ƴarki ko ɗanki ba ƙaramin tataccen ɗan iska ko ƴar iska za'ayi ba."

Jummai taja tsaki "bar tuna min ɗan iska Mr.Joseph, shi ne ya yi min sanadi da ko ƴan iskan na samu ai da ban Yi wahalar ɗaukar rayukan jama'a ba,tun da nasan don rashin ƴaƴa ne yake ta wannan aure-auren." Kari ta ce, haka ne. Suna ta ƴan hirarrakinsu, har suka isa ƙauyen da zasu je, hanya ce mara ƙyau mai cike da ƙwazazzabai tare da dutsina.

Suna isa suka fito suka rufe motar, sannan suka soma hawa dutsen wata Æ´ar bukka ce a saman dutsen nan suka nufa ashar suka zunduma ita ce sallamar shiga gurin Bokan dutse,shima daga ciki ya ce maraba da Æ´an tselan uwa,ku shigo dan abu takazar ubanku.

Suka samu guri gefe suka zauna. Ya dubi Jummai da jajayen idanunshi,kafin ki ce komai ki fara cika min alƙawarina,don tsakaninmu babu ƴar ɗaga ƙafa yanzun ga wuri ga waina zamu dinga yi, tunda ke na lura ƴar rainin hankali ce. Dodo ya ce in kin sake kuskure alƙawarinsa za ki sha mamaki."

Ta buɗe jakarta tana cewa,"kai ko gashi ka cika gajen haƙuri, gashi" ta miƙa mishi makullin motar, ya ce "riƙe tukunna ina motar?" Ta ce "a'a tana can ni ba zan iya jan zuwa gurin nan ba, kuma bana son in ce direba ya jawo asirina ya tonu,ko ba haka ba ne? Yace don wannan babu ji ko su Ifiritu sai su ɗauko, amma sabuwa ce ko?" Suka dubi juna ita da Kari, har suna haɗa baki gurin cewa dal ma kuwa,ya ce shi kenan. Ya shiga haɗa wasu abubuwa yana surkullenshi har ya gama ya ce,to ke ma fa kina da aiki a gabanki, domin wannan aikin ya banbanta da na baya.saboda ita wannan yarinyar tana yawaita ambaton Ubangijin musulunci, saboda haka sai mun dage."

Jummai ta ce,gara kam a dage Boka, saboda wannan in son raina ne ta mutu a ranar da aka kawo ta.

Hajiya Karima ta ce "in ma ta mutu ranar ya kiyaye aure," Boka ya ce "ba zata mutu sanda ku ke so ba, domin Aljani ba zai samu aiwatar da aikinsa ba, sai lokacin da take fashin sallah, saboda tana tsananta ambaton Ubangiji.

Tana yawan kusanta kanta da Ubangiji, sannan ke kuma zaki daina sallah daga yau har sai lokacin da Dodo ya ce kici gaba da yi. Ya miƙa mata wani ruwa gashi nan ki yayyafa cikin ɗakin da za'a saka amaryar, kullum sau uku a rana har tsawon kwana baƙwai. Ya bata wani ɗan gwangwani,ki binne shi a ƙofar ɗakin amaryar in ana sauran sati ɗaya bikin," ta ce "Boka ko'ina tiles,ya ya zan yi in saka? Ya ce "ruwan ki in kin matsu ki sa a fasa, sannan zaki dawo in ana sauran ƙwana tara bikin" ta ce "to sai batun mijina ya ya zanyi na sameshi a hannuna? Ya ce"wannan ba zan gaji da gaya miki ba,ba zaki taɓa samun shi yanda kike so ba, kasancewarshi mai tsayuwa akan duk dokokin Ubangijinshi, sannan tun yana ƙarami iyayanshi suna matuƙar tsaye kan shi, duk bokan da ya ce zai kama miki shi to ƙarya yake yi ba zai iya ba, sai dai ki haɗa da kissarku ta mata,to zuciyarshi tana da tausayin mace, amma ba dai asiri ba,in ma ya kamashi ba za aje ko'ina ba, zai karye.

Jummai ta ce, "shikenan zan ga me zanyi. Suka tashi suka fita yana me ƙara tuna mata ban da Sallah ban da Sallah. Wa'iyazu billa,kaji mushirikan mata.

Alhaji Saddiƙ ya dubi Fatima, "Sister ki duba dai ko za'a ƙara wani abu" cikin dariya ta ce, "sun yi fa Brother,sai dai in kana son ka ƙara zaka iya." Nafisa ta ɗaga wani takalmi mai igiya ta baya ta ce, "haba Brother wallahi wannan takalmin ya yi ma A'isha kaɗan na yara ne fa?" Ya dube ta kaji ki to ai itama yariyar ce,she is fourteen or fifteen,sa'ar ƴarki ce fa sister" ya dubi Fatima. Nafisa ta ce "amma ai tafi Nana tsawo," ya ce "to ai Kuma Nana ta fita ƙiba ma," ya miƙe yana cewa, "kisa direbanku ya ƙwasa ku kaima Hajiyarmu,in ta ce komai ya yi shikenan,sai kusa ranar tafiya tunda gaba ɗaya yau sauran kwana sha shida bikin. Suka ce "To" bayan ya fita suka soma dariya Fatima ta ce "ni nama rasa me zan ce ma Brother babu fa brezia ko ɗaya,ya dai saka pants da skat zuwa su bess, amma babu bra. Nafisa ta ce "nufin shi bata da nonon sakawa ne ko?" Suka sa dariya, Fatima ta ce "kin san shi da kanshi ya siyo undes ɗin, zannuwa da sauran kayan duk ni ya ba zaɓi amma ko takalma sai gashi da su" Nafisa ta ce "shikenan in ta zo gidan ya siya," suka soma shirin ƙwasar kaya don zuwa gidan Hajiyarmu.

A'isha tana ƙwance kan katifa, zuwa yanzu ta gama sadaƙarwa ta dangana ta kuma ɗauki ƙaddara, sannan ta amince ƙwananta ne ya ƙare. Don haka ko yaushe zaka same ta da casbaha tana ja. Istingifari ta ke yi, domin Allah ya yafe mata zunubanta.

Wayarta da ke gefanta ce take ruri, bayan ta ɗauka tare da sallama, ya amsa, sannan ta ce, "ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby, baƙin sun taso na san yanzun ma sun sauka a Kano, saboda jirgin Kano suka hau, ta ce "Allah ya kawo su lafiya," ya ce "Amin" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Beby duk abinda be yi ba cikin lefen ki gaya min kin ji ko? Saboda bata son dogon bayani sai kurum ta ce "To" ya ce "shikenan sai na kira ko? Ta ce,to na gode, ya ce nima haka.

Gidan cike yake da ƴan'uwa ta gefen Umma da kuma gefen Abba. Shi yasa yawancin baƙin duk ƴan Gumel ne, sai ƴan Garki, sun zo ne don karɓar lefe kamar yarda akayi waya aka sanar da su. Anyi girke-girke don tarbar baƙin Katsina. Su kan yiwa amarya tsiya da cewa duk gudun auren ne ta ƙara ramewa, ita dai tana kallon su tana kuma jin su,nata addu'a ne a zuci, Umma ma dai tana ƙarfin hali ne domin kada ta karya ma A'isha guiwa.

Sun iso cikin motoci guda uku fararen Acadami su uku motar farko matan abokanshi ne na Kano,ta tsakiya kuma kaya ne a ciki, sai direba ta bayan mata huɗu ne Fatima a gaba, sai Nafisa sai kuma ƙanwar Hajiyarmu, da ƴaƴarta Talatu.
Chapter 10 · 0% Book details