Sashe 11
Mummunan Zato Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƴan unguwa da suka taru da kuma ƴan'uwa sun sha mamakin ganin kayan da aka kawo, suma sun sha tarba kuma sun ga karamci sun kuma yaba. Nafisa kuwa ɗakin A'isha ta shige lokacin A'isha tana wanka. A'isha tana fitowa taga Nafisa zuciyarta tana son Nafisa. Ta saki murmushi tare da cewa "dama har da ke aka zo? Ta ce,eh mana aini Brother ya yi ma ƙawance. A'isha ta zauna tana shafa mai, Nafisa na kallonta, lallai kam yanzun nononta suke fita ashe ya kula ne. Ta ce, Nafisa ya ya Hajiya fa dasu Aunty Fatima?" Nafisa ta ce, "ai tare da Anty Fatima, muka zo Hajiyarmu kam tana gaishe ki ba ki ce ina Uncle ba? A'isha ta ɗan yi murmushi kawai.
Nafisa ta ce, "Naga kin rame ne" A'isha ta ɗan yi murmushi, sannan ta ce "Na sha jinya fa tun a school har yanzu." Nafisa ta ce Allah sarki, to Allah ya ƙara lafiya. Amin inji A'isha, tare da zura wata duguwar riga, sannan ta soma ɗaura ɗan ƙwali. Nafisa ta ce Allah yasa ki haifa mana Beby mai irin gashin nan naki. A'isha dai ta sunkuyar da kai, Nafisa tayi-tayi ta zo su gaisa da su Anty Fatima, amma ta ƙi,Fatiman ce ma tace ai nima ƙanwar ta ce, bari naje mu gaisa,Talatu ma tabi Fatima dan su ga A'isha.
A'isha ko rufe fuskarta ta yi, har dai suka gaji suka tafi, Nafisa ma nan ɗakin ta ci abincinta, Abba yayi-yayi su ƙwana amma suka ce a'a, Kano zasu ƙwana don zasu shiga kasuwa goben da safe,sai su wuce. Da zasu tafi an basu tukuici suma yanda ya kamata. Nafisa ta raɗa ma A'isha a kunne, cewa ki rage bacci,ki tsaya kan addu'a.tsayuwar dare zaki dinga yi kina roƙon Allah alkhairin da ke cikin auren ya kuma kare ku da duk masu sherri da hassada kin ji ko? A'isha ta ce, na gode Nafisa zan kiyaye insha Allah.
Ya fito daga wanka,wankan da ya zama mishi ƙa'ida, duk dare koda da ya yi shi ne zai kusanci matarshi ya fi gane yayin in yaso ya sake. Matsawar bai yi wankan nan ba,to ko ba zai samu bacci ba, kasancewar yanayi ne na zafi shiyasa. Yana fitowa ya warware (AC) turarukan shi na ƙwanciya ya faffesa, sannan ya saka kayan baccin shi riga da wando.
Ya zauna bakin gado yana son jin muryar A'isha ne kawai,yau ƙwana biyu kenan ba su yi waya ba,bai san mene ne yasa yake son Yarinyar ba,yana tsoron fa kada Yarinyar ta mutu tamkar sauran matanshi. Ya soma neman layin yarinyar,yana yi yana kallon agogo goma ta gota a ranshi, ya ce ko kin yi bacci zaki tashi. Dai-dai lokacin ko ita tana kan darduma, nafila take yi sanda ta sallame sannan ya sake kira.
Ta ɗauko wayar ta ɗaga tare da sallama, ya ce "oh sorry Bebyna, na tashe ki kina bacci ko?" Ta ce, "a'a bana bacci, ya ce me ya hana ki? Ta yi shiru, ya ce to ko abinda ya hana ni bacci ne kema ya hana ki? Ta ce um,ya yi ƴar dariya kin san abinda ya hana ni ne? Ta ce a'a, ya ce in gaya miki? Ta ce eh,ya ce ni tunanin kine ya hanani ke fa? Ta yi shiru ya ce Beby kina ji na kuwa? Ta ce,ina jin ka,ya ce oh gaya min, ta ce ni ina sallah ne, ya ce good,me kike roƙo? Da sauri ta bashi amsa da cewa cikawa da imani da rahamar kabari, tare da samun Aljanna maɗaukakiya." Ya ce "Umhum? Yana son jin ƙarin bayani, ta ce "Shikenan nake roƙo," ya ce "batun aure fa baƙya yi mana addu'a? Shiru ta yi jikin shi ya yi sanyi ya ce A'isha in tambaye ki wani abu? Ta ce eh, ya ce zaki sanar dani gaskiyar maganar? Ta ce,in har na sani ba, ya ce "kin ji wasu maganganu ne a kaina?" Ta ce kamar me? Ya yi ɗan jim sannan ya ce koma na me? Ko kirkina ko akasin haka?.
Ta rasa me zata ce ya ce ina jinki nasan duk mai irin sunanki in dai ta ci sunan bata ƙarya. Sanar da ni. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Uncle duka biyun na ji da kirkin da kuma akasin hakan. Ya ƙwanta rigingine jikinshi ya yi matuƙar sanyi sannan ya ce "Beby tsorona ki ke yi ko? Kin tsane ni ko? Kina zargina kema ko? Na sani na dai na burge ki ko? Muryarshi ta soma rawa, shi kenan ba zan matsa miki ba Beby zan barki kema kina tsoron haka bana son ki mutu domin kin shiga raina sosai" ya kashe wayar ya jefar da ita a kan gado sannan ya ɗauko filo ya rufa akan fuskar shi tare da matsewa yana jin wani pain a cikin ranshi.
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇ðŸ»*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account É—in namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*ÆŠandano page 10*
A ɓangaren A'isha kuwa duk sai ta ji babu daɗi har ma ta yi da ta sanin amsa shi, sai ma duk ta ji tausayin shi ya kamata,ta ji kamar yana kuka. Abbanta zai ji daɗi in yaji labarin nan kuwa? Ƙila ma ya ce ba zai yafe mata ba. Da sauri ta tashi ta duba agogo,sha ɗaya saura, ta ɗauki ɗari biyu ta fita, da sanɗanta ta fice bakin titi ta siyo kati ta dawo ta shige. Sai da ta kulle ƙofarta ta hau katifarta ta loda katin, gabanta yana ɗar-ɗar ta soma kiran layin shi kasancewar wannan ne karo na farko da ta taɓa kiran shi.
Dai-dai lokacin shi kuma yana ta neman layin Abba don ya shaida masa ya haƙura da auran, amma wai layin is switch off,sai ga call ɗin A'isha Beby kamar yanda ya rubuta a cikin wayar tashi. Ya tsura ma sunan ido, kada dai idanunshi ne suke mishi gizo? Ya dai ɗauka ba tare da yin magana ba,ta ce "Uncle" ya ce "Na'am" ta ce "nifa ban zarginka,don Allah kada kayi fushi dani ko da na samu labarin tun a school ne na san dai an confuse amma ba dai na yarda bane,don Allah in nayi laifi kayi min afuwa." Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "ba ki da laifi Beby, domin nima sai da nace a'a Abbanki ya ce babu damuwa, amma bari kiji wani abu,kin ga ke yarinya ce ko? Amma zan rantse miki da wallahi-wallahi ban taɓa shan jini ba, duk wani laifi game da sicret cold zargi ne,ban san shi ba, batun mutuwar matana ƙarar ƙwana ce kurum,kin yarda da haka? Jikinta a sanyaye ta ce na yarda,ya ce "to Beby ki ƙwantar da hankalinki, addu'a za ki dage da yi Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi kin ji ko?" Ta ce "to,kaima ka daina fushin? Ta ci gaba kada fa ka sanar da Abbana," ya yi ƴar dariya bana fushi da ke, kuma insha Allah ba zan taɓa yi ba, itama ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "to sai da safe,ka kwanta. Ya ji daɗin kalmarta, sannan ya ce "to zan yi yanda ki ka ce,kema ki ƙwanta tare da mafarki mai daɗi na twins ma su kama da face ɗin ki,ta kashe wayar da sauri.
Hajiya Jummai ta kalli kayan, sannan ta kalle shi.
"Me ka ke nufi da waɗannan kayan?" Ya dube ta "Na ki ne mana" ta taɓe baki, "Ni fa gaskiya duk zannuwan nan ba suyi min ba,babu kala ta, maimakon ka bani kuɗin na saya da kaina? Kuma ina son canza kayan ɗakina, sannan ga su Suby." Ya ce, "Jummai, gaskiya ni dai ba zan bada kuɗin wasu kaya ba,kin san nawa na siya waɗannan kayan? Game da gyaran ɗaki dai zan baki dubu ɗari,su Suwaiba kuwa dubu hamsin zan bada kada a kuma damuna,cefanen gida kuwa mun gama magana da Uche,ya rubuta komai." Ta sake fusata, domin ta kula ma ƙwangilar da take so ta yi bazata samu ba kenan, komai ƙit da ƙit? Ta dube shi "don kurum zakayi aure, sai ka dinga komai faɗa-, faɗa? Ga wani maƙo da ka koya,da Uche ne yake faɗin abinda ake so?" Ya ce,"to ke ko yaushe baki gida kin ma fi ƙarfin ki ce min zaki guri kaza,koda a waya ne sai dai na dawo baƙya nan, lokaci ya ƙure min dole na sauke abubuwan dake gabana, Uche kuwa shi ne yake girkin nan,don haka shi ne yasan abinda za'a nema.
Ta ce, "Kana lokaci ya ƙure,ba saura sati uku bane bikin? Ta ce, "batun lefe fa? Sai ka kawo a haɗa" ya ce ai lefe ya daɗe a gidan su amarya." Ta miƙe cike da masifa.
"Lallai Alhaji Saddiƙ aurenka na wannan karon ya banbanta da na baya, wannan karon aƙwai ƴar zargi." Ta soma kuka, "maƙiyana sun samu galaba,wato lefen ma ban isa ko gani inyi ba, na gode." Ta fita tana cewa gara daka nuna min babu ruwana abinda babu ruwan mutum ai daɗin ji ne da shi. Ya bita da kallo,wato ita bata san ma ta mishi laifi ba,bare ta bashi haƙuri ko ta mishi bayani shi ne ta zo tana tuhumar shi,ya samu labarin ta saida motar da ya siya ma su Safiya da Suwaiba, domin wanda ya gyara motar ne yake sanar dashi lokacin da ya je ɗaukar tashi motar. Da be ga ta su Suwaibar ba yace sun zo sun ɗauka ne? Sai yaron mai gyaran motar ya ce, a'a wani ne yazo ya ɗauka, kuma ya gaya mishi cewa Babanshi ne ya sayi motar. Alhaji Saddiƙ shi dai alwashi ya sha ba zai ƙara sai wa yaran koda mashin ba.
Hajiya Jummai ta kalli Hajiya Kari.