← Book details Mulki Ko Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Mulki Ko Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hausa Novel
[5:35PM, 2/2/2016] Pherty: [5:26PM, 10/22/2015]
Pherty: MULKI KO SARAUTA
Na fertymerh xarah
Ya fito a gurguje yana gyara alkyabarsa sauri
yake yaje partyn kafin lokacin dagawar jirginsa
yayi
in banda partyn amininsa ne kuma yaxama dole
agaresa da baxai jeba
ta fito sanye da doguwar riga mai kyau da tsada,
fararen duwatsu ne a gaban rigar tayi matuqar
fito da kyawunta
a hankali take jan motarta cikin isa da qasaita
harta iso wani qaton harabar hotel inda yake cike
da mutane
tayi parking din motarta ta suri jakarta qarama ta
fito, tun daga nesa akayo mata caaaaa..... da
idanu ana kallonta
da sauri na'imatu tavqaraso gareta wadda itace
amaryar, rumaisa na bayanta
na'ima tace nayi fushi bida angona sai yanxu
xaki xo tor ki koma
sorry naima kinsan halin baffana musamman ma
idan yana gari
[5:47PM, 10/22/2015] Pherty: tayi murmushi taja
hannunta ita kuma ta riqo hannun rumaisa suka
isa cikin qayatavcen wuri da aka qayatashi yayi
kyau kamar a wurin turawa
ta gaisa da ango suka danyi barkwancinsu da
suka saba kafin su xauna, dayake an jima da fara
events sai bata sami ganin komai da yawa ba ta
dubi rumaisa
tace ni xakima wulaqanci ko, da kikasan baxaki
xo ba dan me xakisa na xauna jiranki,
rumaisa ta tabe bakinta idan da sabo ta saba
kullum suka hadu ko a gida ko a waje sai sunyi
fada
tace yanxuma har cikin mutane sai kin nuna
halinki, inbanda iskanci jiya miss call nawa kika
gani meyasa baki dauka ba ko kuma kika kirani
affiya tace baxan dauka ba kin batamin rai xaki
wani kirana tor idan ma na dauka mecakice
danine?
rumaisa tace kinsan ni kurmace ba abinda xance
dake amma wlhy sai kinsan kinyi da rumaisa
taja dogon tsaki tace ba abinda xakiyi dani amma
kibari agama event din yau hr wurin maimartaba
xamuje, ke kima tashi daga kusa dani
ta kawar da kanta gefe tana kallon yarima da ya
shigo yanxu
ta tabbata aranta hr ga Allah aiman baisan affiya
ba kamar yanda affiya bata san aiman ba,
tana mamakin yanda suke jini daya, family daya,
amma basu san junaba saboda basu taso tare ba
kuma rabon aiman da affiya tun suna j.s1,tun da
yaje pheonix bai dawo ba har shekara uku kuma
tun da yadawo basu taba haduwa ba saboda
kullum yana dakinsa idan baya karatu yana kallon
ball ko kuma game
sai taji tana son ta hadasu tunda daman aure xaa
hadasu amma tanason susan juna su fahimci
juna tun yanxu
Ta xunguri affiya tana son ta nuna matashi a
matsayin yayansu aiman da basu taba haduwa
ba
tace affiya kinga wani abokin yaya maina he is
handsome an beauty nasan xaku dace sosai
ta dago daniyar taga ko waye rumaisa ke yabawa
haka caraf suka hada ido dashi, sai da xuciyarta
na buga tayi saurin dauke dubanta garesa tana
yatsina fuskarta
[11:25PM, 10/24/2015] Pherty: bata ankaraba sai
ganinsa tayi agabanta hannunsa dauke da
loudspeaker ya nunata da yatsa
yace naji kina mgnr xaki xubarmin da ciki idan
bakyaso ni inaso karki kuskura ki soma idan ba
hakaba kotu xata rabani dake
jikinta na rawa ta tashi dafe da qirjinta ga jamaa
duk an xuba mata ido,shikuma yana tsaye ya
xuba hannayensa a aljihunsa yana murmushi
tace ciki....ni
ya gyada kansa yana kallonta da hannunsa yayi
mata alamar 3-2ya juya ya fice yana murmushi
sum tayi ta fadi sumammiya ajikin rumaisa data
riqeta cike da mamakin aiman
tor daman sun san junane yaushe hakan ta faru
ina suke haduwa,tabbas baxata sanar a gidaba
harsai ta tabbatar
tace na'ima dan Allah ku kama akaita gida
ahaka taro ya watse aka sanyata mota suka nufi
gida da ita
shi kuwa gogan ko ajikinsa yana jingine a
motarsa sai faman fusgar da iska yake a bakinsa
yana wani dauke kansa hr suka wuce da ita.
abinda na bashi mamaki bai wuce ganin hrda
rumaisa cikin masu kaita gidaba koda yake tare
ma yagansu axaune, may be sunsan junane
kokuma su qawayene,dama haka mata suke da
shisshigi ya shigar motarsa yajata da qarfi kamar
xai tashi sama fuuuuuuu...

Yana isa gida trolley dinsa ya dauka da laptop da
manyan wayoyinsa da duk wani abu da yake
buqata yabar gidan ganin lokacin tashin jirginsu
ya kusa bai ko nemi sarkiba saboda hr ynxu yana
fushi dashi
kai tsaye airport ya nufa cikin qanqani lokaci
jirginsu na daga
Tunda ya.iso pheonix ya soma kiran layin
ummansa, tana dauka yake gayamata shi har ya
iso skul kuma ta gayawa tsoho karma ya
nemeshi, bai jira cewartaba ya tsinke wayarsa.
[12:04AM, 10/25/2015] Pherty: yaya mamakin
samun nabila gidansa dakuma yanda akayi hrta
sami shiga ta tare masa a gida alhali security
nagidan
har yaje xai tara security ya tambayi dalilinsu
nabari mace ta xauna masa a gida sai kuma ya
fasa acewar bayason hayaniya ko dogon turancin
daxasu tsaya yimasa sannan ma idan ya
tambayesu dalili tamkar ya xubar da ajinsa ne
qasaitarsa ta xama ta bnxa itada ta kawo kanta
idan ta gaji xata fita
tana ganinsa ya shigo ta taso da karairayarta
xata rungumesa,yasa hannu ya tureta ta fada a
saman center table sai da qugunta ya bugu
tace wash
yaja tsaki ya fice fuskarsa a murtuqe
shiru tayi bata damu ba amma tasa aranta sai ya
sota kuma ya aureta ta dauki aniyar biyarsa gida
nigeria domin ta cimma burinta kuma xata
shanye duk wani wulaqanci daxai biyo baya daga
garesa
bayan qugunta yadaina xogi ta tashi tabishi har
dakinsa yana qoqarin cire kayan jikinsa,ya dubeta
cike damamaki karo na biyu a rayuwarsa da ya
kebe da mace a daki bayan affiya
ya gyara tsayuwarsa bayan ya maida rigar ya
kafeta da narkakkun idanunsa dake rikitata
yace ashe ke marar hankalice bansaniba ke
wacece daxaki shigomin daki ba ixini ba komai
angayamiki ko ummana na shigomin daki kasafai
ballantana ke banxa bullshit
hannunta a qugunta take kallonsa
tace laifine prince dan na nuna qaun..........tas
kakeji ya dauke fuskarta da mari kusan sau uku
ina magana kina magana,ina baki umarni kina
gardama dan kin rainani,fuskarsa a daure ya
nuna mata hanyar waje
yace get out of my room,kika sake gigin shigomin
daki sai na karyamiki qafafu stupid
a tsorace ta fice daga dakin jikinta na rawa
hannunta dafe a kuncinta,
ya soma safa da marwa yana yayyafe hannunsa
da ya mareta gani yake ma taci amanarsa da
hannunsa yakai a jikinta hr shikemata Allah ya
isa
yaja numfashi ya furxarda isaka daga bakinsa shi
ala dole ransa bai baciba bai yarda da bacin raiba
wai haushi tabashi
yana mamakin yanda mata k bibiyar maxa,tor shi
mema xaiyi dasu meye nashi da mata da suke
matsar da kansu akansa....

Sunayin parking a harabar gidan suka fito da ita
securities hankalinsu na tashi ganin yanda suka
fito da ita
a falo suka tadda president da ammi da aliyu
duk suka tashi lokaci daya suna tambayar meya
faru
na'ima tayi masu bayanin komai dan rumaisa
bata shigoba tanadaga waje tana tsoron su ammi
su tambayeta, dai dai lokacin ta farfado
nan da nan ran maxa na baci,ya rasa meke masa
dadi a duniya ya riqa safa da marwa acikin
katafaren falonsa kafin ya juyo idanu jawur yake
kallonta dai dai lokacin qawayenta na fice da
sauri
yace ciki ciki affiya,waya maki cikin,menene
dangantakarki dashi,waye ubansa a duk fadin
garinnan dame kuma yake taqama?
hawaye na xubo mata tasoma girgixa kanta cike
da tashin hankali
tace Allah baffa bansaniba.......ji kake gau ya
dauketa da mari
aliyu ya riqota cikin tashin hankali abinda bai
taba gani.ba baffa yasa hannu akan autarsa
jikin ammi nayi sanyi sosai
kuka take kamar ranta tunda taxo duniyabata
taba tsintar kanta cikin irin wannan yanayinba
kin mantane kin manta duk gatandana ke baki bn
manta tarbiyar dana baku ba meyasa kikaci
amanata auta, meyasa kika nemi toxarta ni a idon
duniya
tana kuka tasanardashi komai sai dai bata fadi
dan sarki bane gudun baffanta yaje bincike aje
ahanasu bata rama ba
waye mahaifinsa
tace nima bansaniba
tor meyasa kuke haka ynxu me gari ya waya
tana kuka tace wlhh sai na rama baxan kyaleshi
ba ta tashi ta haura step ta nufi dakinta tana
kuka sosai
[12:10AM, 10/25/2015] Pherty: Tun daga ranar
take nemansa ruwa a jallo ta baxa securities
dinta ako ina suka gansa su xomata dashi
duk inda takesa ran ganinsa ta duba bata
ganshiba babu sa babu alamarsa batasan daliliba
hakan ya qara qufular da ita sai take ganin kamar
da gangan yanemi toxarta ta a idon duniya tunda
gashi an nemesa ansa kamar walqiya
tayi kuka kamar ranta hrta gode Allah ta tabbata
baa taba cin xarafintaba irin wannan ta qudirava
ranta baxata barshiba sai ta rama aduk lokacin
da suka hadu sai ta nuna masa qarfin MULKI
yafina SARAUTA.

Hausa novel
2 February at 22:16 路 fertymerh xarah n...
Chapter 6 · 0% Book details