← Book details Mulki Ko Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Mulki Ko Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hausa Novel
[10:37AM, 1/30/2016] Pherty: [4:16PM,
10/21/2015] Pherty: MULKI KO SARAUTA
Na fertymerh xarah
Ta juya ga bodyguards dinta
tace kushiga dayar motar kuhe gida xan sameku,
ta shige ta ta motar taja ta fuuuuuuuuu
tafiya sunkayi mai nisa batare da sun tankawa
juna ba kafin ta juyo tana kallonsa fuskarta a
daure
tace kayi shiru ashe kai matsoracine ashe duk
mulkinka isarka taqamarka duk na banxane tunda
kake taqama da sarauta
hmmmm kaga naci nasara a tarkona na biyu
haka nake fatan samun nasara a tarkona na biyu
domin in banbance ma tsakanin aya da tsakuwa
murmushi yayi yana kallonta ta madubin motar
alamar ko ajikinsa sam abinda tayimasa baiji
haushiba illah birgeshi da tayi bai taba haduwa
da mace qarama mai taurin xuciya kamar ta ba
yace akowane lokaci nawa tarkon xai iya riskarki
domin kixama acikin shiri nima xan banbance
maki tsakanin affiya da aiman
murmushi tasakeyi akaro na biyu ta juyo tana
kallonsa kafin ta maida hankalinta kan tuqin da
take
tace kasan shi kudi ba abibda basayi duk da
matsayin mahaifina a qasar nan, ni mace dayace
daya mallaka a rayuwarsa a kaina xai iya rasa
komai nasa dan ganin farincikina
kanagani akwai wani tarko naka da xai sanyani
fargaba gudan ni jinin mulki wacce ke ji da kanta
fagen kyau ilimi kudi da kuma MULKI, kaga kuwa
affiya ta xarce tunaninka
ya kyalkyace da dariyar da bai taba yi ba koda
kuwa agaban ummansa ne aransa yana son sanin
wane irin mulki ne take taqama dashi amma
girman kansa da ajinsa ya hana ya tambaya
domin gani yake idan yayi hakan tamkar
girmansa ya fadi ne agareta
@)
yace kina gani kudi na iya magance ko wace irin
matsala a rayuwa,
kin manta akwai abinda kudi baxasu iya
maganinsaba,kamar yanda kike taqamar k mace
dayace agun mahaifinki
[4:32PM, 10/21/2015] Pherty: haka nima namiji
dayane agun abbana,saboda tsananin son da
yake min dayanada iko ko numfashi baxai barni
nayiba sai dai yamin, kada kibari xuciyarki ta
yaudareki gun jayayya da dan jinin SARAUTA
maiji da qasaita
qasaitaccen murmushi tayi dai dai lokacin datayi
parking harabar wani danqareren gida mai kyau
da tsada wanda mahaifinta ya bata domin ta riqa
hutawa kawai aciki
ta duba taga yanda securitis suke tasan xasu
tambayeta inda tasamo yarima saboda kariyar
lfyta
shikuma yana kishingide hankalinsa a kwance
taxo ta bude masa qofar mota
ya dauki kusan minti talatin bai motsa ba bai
kuma kalletaba harta soma tsarguwa da gajiya da
tsayuwa sai taga ya xiro qafafuwansa waje ya
fito yana gyara alkyabbarsa, ta nuna masu dan
uwantane kafin subarshi ya shiga
tfy suke cikin hadaddun falon masu ktau da tsari
har suka iso wani bedroom ta bashi ixinin ya
xauna saanan ta dubeshi tana murmushi
tace 2 days kawai xakayi anan kafin na maidaka
inda na dauko ka, ba komai xanyimaba kawai
hankali xn koyama yanda xaka riqa respecting din
mutane musamman irina, karkuma ka damu da
motarka nasa a ajiye ma ita, ba abinda xai
sameta
19
ya tashi yayivtaku ahankali daga inda yake xaune
hr inda take tsaye yaxo dab da ita
yace well gsky kinyi qoqarin sato dan sarki ki
buya ta hanyar amfani da basirarki da wayonki,
mace bata taba birgeniba sai ke domin kece mace
ta farko dana soma haduwa da ita fitsararriyar
mace irinki mace marar tsoro (i lyk d game) sai
dai abinda xan miki nan gaba baxakiji dadinsaba
tace ba'anan gixo ke saqa ba wayarka nakeso
kabani domin ban amince da ka kira kowa ba
[4:52PM, 10/21/2015] Pherty: batare da yayi mgn
ba ya juya ya kwanta a luntsumemen gadon
yace kinsan dan jinin sarauta baisan komai akan
wahalaba bai iya komai ba da fatan kin shirya
hakan
ta juya ta fice batare da tayi magana
yabi dakin da kallo yanayinsa ya birgeshi bai cika
hayaniyar kayaba komai a natse
ya tashi ya nufi inda yake tsammanin nan ne
toilet ya shiga yayi wanka
kusan minti hamsin da shigarsa kafin ya fito dai
dai lokacin ta shigo dauke da qaton tire cike da
kayan marmari ta dire akan wani qaramin dianing
ta juyo tana kallonsa yana tsane jikinsa da towel
faffadan qirjinsa ta tsurawa ido tana kallo mai
cike da yalwar gashi ya kwanta lub a qirjinsa
akan tsantsinsa sai sheqi yake, tayi saurin dauke
idanuwanta akansa
tace waya baka ixini kayi wanka? batare da
yabata amsa ba yaje ya rufe qofar dakin ya juyo
yana kallonta
yace au kinga kin manta baki sanardani karnayi
wanka ba kuma nayi, taja dogon tsaki ta dauke
kanta daga garesa
yace kinga ko yanxu am d winner an u ar d
looser, saboda kin daukoni kin kawoni gidanki
kinamin hidima tabbas bakida banbanci da
kuyanga agareni ke baiwatace
ta juyo idanunta jajir saboda bacin rai ga
kalamanda yayi mata ba'a taba wulaqantata ba
kaar yau wai itace baiwa kuma kuyanga
ya duba kan mirrow kakakaf ba irin man da yake
shafawa ya tabe bakinsa yana kallonta
yace madam wannan kallon fa na menene ko ba
gwarxon namijine a gidanku
20
ta gyara tsayuwarta hannuwanta a qugunta
tace har yanxu banga wanda yakai yayana
haduwa ba domin ya fika a fagen komai
yace shiyasa naga kin nace da kallona kinkasa
dauke idanunki akaina.....bana cire kaya na
maimaita fa.
taje ta bude sirf ta ciro masa wasu hadaddun riga
da wando nasu kyau da tsada ta bashi, na yaya
aliyu ne da baffa ya siya masa a wata tafiya da
yayi canada
shikansa kayan sunyi matuqar birgeshi amma sai
ya yatsina fuskarsa
yace wadannan kayan sai kace mai aikin dako
bata kulashiba bata kuma nuna damuwartaba
amma taji xafin mgnr
ya shiga toilet bai jima ba ya fito kayan sunyi
matuqar karbansa sun qara fito da kyawunsa a
xuciyarta ta yabahakan har batasan sanda ya iso
dab da itaba yasa hannu ya shafi fuskarta tayi
firgigit
yace kallon ya soma isata fa madam
[5:15PM, 10/21/2015] Pherty: taja tsaki saanan
ta sauke farantin data shigo dashi qasa
duk suka xauna a lokaci daya ta soma gyara
fruits din tana ajiye masa a gabansa amma ga
mamakinta ko kallonsu baiyiba
yace baa sabamin da hakaba ban taso da
wannan halayya ba
an sabamin a duk lokacin danake cin abinci ko
kuma ake bani ana min hira da labarai masu
sanya nishadi kuma ko wace rana da labarin da
xaa min
ta jinjina kanta a ranta tana qiyasata irin
sarautarsa da qasaita ita a xahirin gsky batada
wani lbr da xata bashi.... kafin tayi mgn tuni
wayarsa ta soma qara
ya dauki wayar ya duba ganin maimartaba ne
yasa yadanvtaso daga kishingiden da yake ya
kara wayar a kunnensa
yace abba, daga can bangaren anka soma mgn
21
yarima kana inane, yaxaka fita ba securities
yayi shiru kafin
yace abba gani hanyar xuwa kaduna gurin...... ya
katse sa cikin tsawa
da izinin wa? meyasa xaka fita kaikadai kabar
matakan tsaronka, tor ka juyo da motar kadawo
duk kasa hankalina ya tashi ya tsinke wayar
yayi shiru yana kallon wayar kafin ya dubeta
yace sai kitashi ki maidani inda kika daukoni
ta kyalkyace da dariya
tace ai ba inda xakaje sai kayi kwanakin dana
dibar ma
batare da yayi magana ba ya tashi ya fita daga
dakin
tayi murmushi
tace ko kaje aikin banxane dan baxasu barka
fitaba sai da ixinina
baifi minti biyar ba yadawo ya dubeta karo na
farko a tsayin rayuwarsa da yasan ya dubi mace
da kalar tausayi
yace inason mahaifina bana son bata masa kamar
yanda bayason bata mini, mahaifina yanada
daraja agareni
tayi banxa kamar batajinsa
ya xuba hannayensa a aljihunsa yana kallonta
yana furxar da iska a bakinsa
yace amma kinsa xamana dake gida daya ya
haramta ni ai ba.muharraminki bane daxaki
tsareni a gida
Allah ya hana mace da namiji su kebe guri daya
idan ba muharraman juna bane so koba danni ba
ki tashi muje kodan fadar Allah
ta tashi ta fice yabi bayanta a ransa yana
sonvtuna irin abinda xai mata ya rama dan baxai
kyaletaba sai ya rama.

WANNAN KENAN?
Chapter 3 · 0% Book details