Sashe 6
Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko mace'yar uwarta kan shagala gurin kallonta, gefen kumatunta ya kan lotsa ko da magana zata yi shi yasa duk sanda ta fita sai taga jama'a na kallon ta sai dai abin mamaki bata taba samun ko da wasa wani da namiji Yazo yace yana sonta ba, hakan bai dame taba nata ganin rashin sakin fuskar da take yi ne in zata fita da kuma tsoron da ta kema mazan, dama bata bukatarsu tunda ana ta ganin sun cika zalunci tare da dan nema mata hakkinsu shi yasa basu ne a gabanta ba, amma ga mamanmu tana son taga cewa Bilkisu tana da tsayayye kafin ta kare secondary in yaso taci gaba a dakinta, sai ga shi mansura samari sun mata Caa! Haka Sakina da Maryam kannan Bilkisu wadanda ke j.s 2 yanzun haka, sannan'ya'yan su ladiyo duk ba Sufi sha biyu sha uku ba amma duk suna da samari yan cikin gidan yayaran yayin mahaifinsu.
Malam mamman ya shiga dakin mama tana zaune kan dardumar da ta idar da sallar isha'i, ta amsa sallamar da yayi tare da fadin sannu da zuwa, yace yauwa. Ya zauna " Dama nazo ne kan batun Bilkisu , don na kula yarinyar bata da mutunci shi ne ma dalilin da yasa ban taba ganin saurayi yayi kiranta ba, sai dai kannanta, kila tana nufin sai me mota ne ko? To ba zan yarda da zamanta ba, ba ruwana da wata bokon baza can, ke da ki ke daure mata to ki gaya mata na ce aure zan mata, mama ta sanyaya murya sannan tace to kayi hakuri amma ma yarinya take da za ka daga hankalinka?
Yace ke Fatima ban San zancan wofi su suwaiba ba kannanta ba ne? Tani da Amina duk sun sasanta dasu Jibrin, don haka ba ruwana da wani lokaci , su ladiyo sun Fiki tunani, tunda suka sa 'ya'yansu suka fito da miji sai kece oho na fahimci gaskiyar su ladiyo ne da suka ce kin ce ke'yarki sai mai kudi ko?
Zaku ga kudin in nayi sada ka da ita kuma almajiri zan ba sadaka, ya fita yana mai ci gaba da fada har zuwa gurin mahaifiyar shi wato goggo amarya nan ya shaida mata nufinshi na sadakar da Bilkisu ta ce jeka ba da ta in ma mahaukaci zaka ba shi, uwarsu ta ci dogon buri akan su bari ka ji in shaida maka in har ka sakar ma wannan matar taka fuska to zaka yi da ka sani , tunda ta daure ma ya'yan ta mata suna wannan bokon na san cewa tana da mugun kuduri nufinta ta tarasa suyi mana gandan- gandan a cikin gidanka, ya zama kai ba da kayi bata karba saboda ka jibge balagaggu cikin gidanka, tashi kaje duk nufinta ni na sani burinta kenan sai mai kudi....
Yan rigingimu sun faru cikin yan kwanaki in da su ladiyo tare da sauran dangin na maigidan suka yi ta zuga shi yana zuba wa mama da ya'yanta wulakanc. Bilkisu tana zune ta ma kasa cin abinci,saboda hankalinta yana tashe ne, yan kwanakin mansura tana zaune gefenta tana lallashinta, can cikin daki kuma mamanmu ta tasa su Sakina tana musu nasiha kan cewa ba su isa kula samari ba, shekarunsu ko sha biyar basu kai ba sakina tana sha hudu maryam sha uku maigidan ya shigo da fada yana cewa ina Bilkin ne? Da sauri ta mike tana matukar jin tsoro shi, yace fita maza ga bakon ki can waje shi ne mijinki shi na baki, saboda bakin jininmu,na idar da sallar la'asar na tashi ina cewa ina da 'ya duk mai bukata na bashi amma na rasa mai so sai da na toho hanya sannanna ci karo da wannan dan garuwan shima sai da na roke shi arziki da kyar ya yarda sauran ki mishi wulakanci, cikin kuka ta fita yana tsaye jikin gidansu riga daban wando ma haka, kuma duk na shadda, kodaddu sun jike, ta isa gurinshi tace sannu da zuwa.
Baki ya saki yana kallonta,cikin in-ina yace ke ce kece babanki ya bani?Ta daga kai yace,tab gaskiya kin fi karfina,wannan rike ki ai sai gwamnatin tarayayya,karamar hukuma ma kam ba zata iya ba.Ya tafi yana waiwayanta yana cewa kaga mutum zai cuce ni? gida ta koma cikin jin dadi tana gaya masu mansura da su mamanmu abin da ke faruwa.Muryar babansu taji ya kwala mata kira, da sauri ta fita.Ya dube ta kun gama magana ko?Tace ya dai tafi ne.Yace kina nufin baku daidaita ba?Ta daga kai alamar eh.Yace ki dai ce kin koreshi,yau ko kyaci ubank.Ya ciro igiyar guga ya shiga dukanta,mama sarkin hakuri tana jiyo su kuma zuciyarta na zafi amma haka ta daure bata fito ba,sauran matan sai dariya suke ba wadda tace ai hakuri,jina-jina yayi mata ya fita yana zage-zage,ru mansura suka kamata suna kuka suka shige daki.Tun daga nan kullum cikin turo mata maza yake,amma kamar hadin baki duk wanda yazo sai yace tafi karfinshi hakan nan shima bai fasa dukanta ba,har bikin su suwaiba yazo aka yi biki aka watse Sannan Bilki ta dan sama sauki sai dai sun sha habaici ranar bikin, wannan bai dame su Bilkisu ba. Maryam zo ki jawo min ruwan wanke wanke. Cewar Bilkisu, tace Allah sarki Anty Bilkisu dazun fa nice na ja miki na wanki ga Sakina can Allah bata komai. Sakina ta fito tana cewa, sannu da cewa bana komai wa ke gyaran daki? Bilki tace maryam ja min ruwa sakina je ki karasa gyaran dakin, ladiyo ta dubi karima tace. Allah mun huta su tani ana can dakin kai, salame ta cafe ai yafi musu ni in bar 'yata gwansame duk wanda ya shigo ya kasa gane waye uwa wacece yar. Karima ta kalli Bilkisu, sannan ta kalli su Salame, Ya'yan namu sun da farin jini ne, amma wasu zaki ga ga dai kyau sai a rasa ma shinshini. Ladiyo tace kin kaita da nisa, kin manta da wadda uwar ke fita yawo boyi gidan masu dashi, ya'yan na gantalin boko, amma babu mashinshini. Karima tace babu ya babbar kullum sai uban ya kima, su kasa dariya,daidai sanda Sakina tazo tana ce ma Bilkisu.Anti Bilki ina abin kwashe shararmu
[8:46AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 12ðŸµ
Kafin ta bata amsa sai ta ji karima tana cewa don tsabar bakin jini irin na o'o sadaka ma an rasa mai so, duk yanda maza ke son mata amma an rasa mai sonta.Sakina tace,aikin banza sa'idawa.Salame ta mike ke mara kunya waye mai saka idon? Bilki tace ke sakina kin hauka ne? Su karima suka soma masifa amma sakina bata yi shiru ba,fadi take toni da ku nake? Kuna maganarku,nima tawa nake yi. Bilki tace wuce daki bana son rashin kunya.Ladiyo tace yi min shiru munafuka ke kike sata bata son hayaniya don haka sai ta mike ta nufi dakinsu.Cikin haka har suka shiga ss3. Lokacin 'yammatan duk sun kawo,hatta Asma'u auta an soma girma, ga malam mamman kullun cikin fada yake kan cewa ya gaji da ganinsu sannan duk cikin dangin su ya cigita koda wanda yake so amma sun ce sam saboda tsana, cikin haka suka soma jarabawar sauka mansura da bilkisu sunfito daga gidan su mansura zasu zo gidansu Bilkisu a kofar ghda suka ga Sakina tare da wane dan yaro suna hira....
Mansura tace Bily gaskiya ki masu sakina magana su daina kula kananan yarannan ba fa aure za su yi ba, sai dai bata yara. Bilkisu tace kin san sakina da shegen musu in na musu magana sai suce wallahi ba samarin su bane 'yan makarantar sune bari zanyi maganin su yau sun samu mama tana cin abinci suka zauna mansura tace mamanmu zan ci tuwon nima, ta turo mata kular gashi nan ki saka gamiyar can cikin tukunya wata nayi kin san yau ladiyo ce ta yi girkin mansu tace. A'a mamanmu ba an raba girkin ba? Bilkisu tace kin san matan gidan sai dai shirin Allah sun kuma cewa sai dai a hada,Mansura ta ture kular tare da cewa ba zan ci tuwon wannan kazamar ladiyon ba. Bilkisu tace yauwa. Mamanmu, gaskiya kima su sakina magana su daina kula kananan yaran nan, ga masu sonsu 'yan mutunci, ai gara ma su fitar da mazan saboda fadan baba ko yaya ki ka gani tunda suna j.s.s3 ne sun ci gaba can dan fadan baba yana daga min hankali ta soma hawaye duk dana tsani maza da ace na samu mai sona ko yaya yake Allah zan yi aure ne..
Ko dan ke ma ki huta da gorin'yan gidan nan, mansura tace haka ne tunda suna da manema, cikin tausayi mamanmu tace maigado kena ke tunani bana son su riga ki aure,gashi naso suma suyi karatu mai dan zurfi.Bilki tace kada ki damu aure da mutuwa duka na Allah ne,kema zaki samu saukin fadan baba in kin rage biyun,suna cikin tattaunawa ne maryam ta shigo mama tace mamina daga ina?Tace banace miki Ibrahim ya iko kirana ba?Tace yauwa dama ina son in ji shin da gaske ne auran ki zai yi?Maryam ta sunkuyar da kai kasa tace tun tuni fa yake cewa zai turo na ce mishi a'a saboda ga antinmu nan bata yi ba. Bilkisu tace kin ji shirme,to dama in yazo kice mishi ya turo tunda ba boyayye ba ne,kowa yasan gidansu akwai mutunci,mansura ta duki kafadar bilki tace kai su Bily akwai shegen manyace,suka sa dariya bily tace Allah kuwa na sakina ne wannan Abdul din nake ganin sai an dan yi bincke kanshi,saboda don kano ne Mansura tace shin kece za ki bincika?Bilkisu tace,to hakkin baba ne kema kuma kin san ba zai yi ba amma a san yanda za'ayi ko Mamanmu? Ta ce dole kam.