← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 60

Sashe 49

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakika Yarima yana son mata shi likitansu ne,sannan yanzun cikin course din nan ya gano zasu iya maida tsohuwa yarinya,domin ana iya canza fata suna dasa nono daga zubabbe ya koma tsayayye har yake tunanin na billy inda ba tsayayyu bane da sai yayi mata aiki ya gyara su toh amma yayi sa'a nata masu kyau ne sosai tsaye suke kyam irin wanda ko tsufa baya sawa suyi sharab dinnan sai dai su dan russuna .yana zaune cikin dakin daya zama mallakinsa,wani abu yake son sani cikin laptop game da course dinsa, yarinyar bata fi sati daya itama da zuwa ba,ita ‘yar mutanen Maroco ce,tana da kyau sosai itama tazo yin course ne irin na Yarima tun ranar daya soma ganinta ya shiga rudu,sannan jinkai da sarauta suka motsa.yana dago kai ya ganta tsaye cikin dakin,ya tambayeta shin tana bukatar taimako ne?Bada bata lokaci ba tace,tana son yin magana dashi ne,yace mata babu matsala,amma fa sai dai ba yanzun ba domin yana da abin yi,tace to ta iya jiransa?Yace,inbata da abinyi ta iya yin hakan mana.tace shikenan,ya nuna mata gurin zama yaci gaba da aikinsa.tana kallon Yarima komai nasa yayi mata,tana sonsa tun sanda idanunta suka soma ganinsa yana da kyau sosai,tsawon awa daya da mintina sannan ya gama komai,ya dubi agogo sannan ya dubeta tare da cewa,lokacin sallarsa ya kusa shigowa,amma zata iya yin maganar cikin minti sha biyar?Tace bazai kai ba ma,ita kawai tana son su zama abokai ne kawai,yace me yasa tayi tunanin su zama abokai?Tace haka nan kawai ne taji ya kwanta mata cikin rai,sannan ta lura yana son yayi abinda ya kawosa ne, tana son mutum mai kwazo da ilmi.yayi godiya tare da mika mata hannu,sunnan shi ya sanarda ita wato Prince Al‘amin,cike da jindadi tace,ita kuma sunanta Tina Abraham. Tun daga ranar suka zama aminai duk da cewa basu taba aikata wata masha‘a ba,suna dai sha‘awar juna amma duk sun danne.sai wata ranar lahadi yana waya da Bily ta shigo,zama tayi tana kallonsa tare da sauraron yaren Hausar da yake magana da ita,sai daya gama sannan tace masa tana son ta iya wannan yaren,yace to gaskiya bai alkawarin koya mata ba,amma inya samu lokaci zai dan kwatanta,ta matso kusa dashi tana shafa gefen wuyanta tare da lasar lebunanta tace masa ita in tana kusa dashi sai ta samu kanta cikin wani yanayi,shin zai yarda su dandani juna? Baice kala ba kuma bai mata tsawa ba sai data zo kusa dashi ta rungumesa, wasu abubuwan data soma masa sune suka sa shi kasa daurewa,harma ya fito mata da kwarewarsa awannan harka.Tina ta raina kanta da kwarewarta agurin yarima, ta kuma kara samun kwarewa tare da sonsa mai tsanani, tun daga ranar ta tare a dakinsa suka cigaba da lalacewa,Allah ya kyauta musu.Bily tana zaune cikin kujera bayan ta gama kwara amanta,sanyi ne takeji tana zato na zazzabi ne.Jakadiya ta shigo tace da jakadiya taje ta kawo mata bargo. jakadiya taje gurin Umma tana cewa,ranki ya dade gimbiya Bily fa duk kwanakin nan batajin dadi,ba ko za‘a kira likitar nan ta dubata ba ko mun samu karuwa ne?Ai jin haka da sauri Umma tace,bani wayar can, jakadiya ta miko,Doctor Aisha ta kira tace mata tazo yanzun,kamar minti hamsin ta iso.bayan gwaje-gwaje da ‘yan tambayoyi ta gano cikin wata biyu da ‘yan satittika, nan take ta sanar da Umma, murna gurinsu ba‘a magana,nan dai aka daura mata karin ruwa. mai martaba harda goron albishir ya hadama doctor Aisha dashi.ita dai Bily damuwarta daya,in Yarima ya samu labari yaya za‘a kwashe?A dare ko ya kirata sai tayi tunanin ta sanardashi kuma ta nuna masa ita bata so don in wani ya sanardashi to zasu kwashe ta babu dadi,yanzun ko ta siyasa zata bi.yace beauty yaya ne?Tace,um kai dai bari,muna cikin matsala fa,ya gyara zama tame kenan?Tace banga al‘ada ba gashi har na soma rashin lafia,Umma ta turomin doctor Aisha ta dubani bansan me tace ba naga dai gidan ya cika da murna,nidai gaskiya banason in haihu ka fada min me zanyi? Yarima ya kasa magana ma don takaici can yace gaskiya matsalar ma babbace, ko dai inzo ne acire shi? Gabanta ya fadi,amma sai ta daure tace kada kazo in akwai wata kwaya mai karfi ka min text dinta in aika asiyo min insha,yace yauwa kin kawo shawara, to amma wazaki aika?Tace Atika don batayi karatu ba kuma in gargadeta nasan zataje, yace shikenan zan turo inbai fita ba ki gaya min,tace to amma fa insu Umma sun kiraka sun maka murna kadaka nuna baka so don inmun cire kadasu gane ko su zarge mu. yace, haka ne beauty kada ki damu kin ji? Tace to sai na gani.
Hankalin Yarima ba karamin tashi yayi ba,shin wace kwaya zai ba wa beauty? Nan take ya shiga cikin asibiti gefen magunguna ya bincuko, nan take yazo ya turo mata su in ta samu kuma ga ka'i'dojin su, sannan ya kira ta yace ta gani? Tace, ta gani ta share ta ci gaba da sabgarta, shi ko kullum nacin tambaya ya ya fita? Tace Aa yace to zata iya ganinshi a kowane lokaci. Zai zo ya cire mata shi tace to gara haka din ma, ya ce ai su Umma sun kira ni har da mai martaba na dai nuna musu murnata tace to sai na ganka, ai suna gama waya ta kira magajin Malam a waya tace tana Neman shi yanzun nan, cike da far gaba ya zo don bata taba kiran shi ba.
Bilkisu ta sanar dashi Komai tace in yazo kasan dole ne ya cire cikin nan, ni yanzun ban san ya ya zan yi ba, kuma bana son in fada ma Umma, magajin Malam yace to lallai Yarima, amma kada ki damu ki barni dashi ni nasan yanda zan mishi in hana shi zuwa, nan take ya kira shi. Yarima ya soma mishi tsiya ango kasha kamshi, sai yau aka ga damar kiranmu? Magaji yace kai me ya hana ka kira ni? Yarima yace Aa bana son in takura maka ka samu gurin Hutu gashi kuma abun ya hada maka biyu, wato ga sabon shiga ga ka tuzuru yace ba komai, dama na kira ne in ce maka ina murna da samun baby, yaci gaba sai dai wani abu da bai min dadi ba, shi ne na shiga gaida bilkisu na same ta a galabaice, sai da aka dauko Doctor Aisha nan ta gano tasha wata kwaya ne don zubar da cikin, a tsorace Yarima yace yanzun ya ya ake ciki, su Umma sun sani? Magajin Malam ya kuma dagewa tamkar gaske yace yanzun dai da mun gama waya zan sanar dasu don na hana Doctor Aisha ta sanar dasu, musamman da na fahimci da saninka zata zubar da cikin, magana daya dai yanzun ko Ku janye ra'ayinku kai da matar ka ko kuma wlh zan sanar da su, musamman in har kazo don na sanka sosai zaka iya cewa zaka zo kayi aikin da kanka.
Jikin Yarima ya mutu, sannan yace amma dai magaji kasan haihuwa ba ra'ayina ba ne ko? Tsaki magaji yaja sannan yace, wannan sai ka gaya ma ubangijin da ya baka cikin, ya kashe wayar shi.ya dubi bilkisu bar shi kawai, ba zai zo ba, suka yi ta dariya ita da magaji tayi mashi godiya sannan ya tafi.
[8:38AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 81🏵

Ya kira bilkisu yana cewa, ya ya aka yi ta bari magaji ya sani? Tace ya shigo gaishe ni ne ya same ni cikin wani hali shi ne ya kira likita.... Ta soma kuka cikin kissa ni gaskiya ba zan iya ba, gashi yace zai gaya ma su Umma kuma kasan yanda su Umma suke murna za su dauki mummunnan mataki ne a kanmu, yanzu ya ya zan yi? Yace ya ya zaki yi kuwa in ban da hakuri? Kina nufin zan zabi bacin ran iyayena saboda ranki yayi fari? Ba ki kai wannan matsayin ba, ta soma sabon kuka wato danni baka kaunata in zan mutu ne in mutu ko shi kenan, ta kashe wayar sannan ta soma dariya tana cewa in kasan wata ai baka San wata ba, don ma kada ya dauka fushin wasa take yi sai ma ta kashe wayarta bayan ta kira Mansura ta mata bayanin komai, sannan ta ce zata kashe wayarta don kada ta nema ta ji shiru, Mansura ta kara ma ta wasu dabarun sannan suka yi sallama, hankalin ta kwance ta gode ma Allah tasan bata da matsala ta gefen Yarima, Allah yaga niyyarta Yarima da farko bayan ta kashe wayar cewa ya yi ke dai ki ka sani ko a jikina da bacin ran iyayena ai gara naki.

Amma kuma me?

Kunnuwanshi sun kasa daina jiyo mishi kukan da ta kashe waya tana yi yayin da zuciyar shi ta shiga cewa kamata ya yi ace ka lallashe ta ne, zugin zuciyar ya matsa mishi nuna mishi take yi bai yi mata adalci ba, haka dai ya daure yayi jarumta har zuwa washe gari inda abin ya ishe shi har ya nemi layinta cikin wayarshi amma a kashe, yayi ta kira shiru ya bata awa daya ya sake kira nan ma shiru, jikinshi ya yi sanyi, zuciyar shi ta dame shi yinin ranar babu kuzari duk wadanda suke tare dashi duk sun fahimci yana da damuwa, musamman Tina. Shi kanshi ya rasa dalilin damuwar tashi, akan matar da ya tabbatar ba sonta yake yi ba, wasa- wasa yau kwana hudu yana neman layinta babu dare babu rana, duk da ya kira magaji ya tambaye shi shin bilkisu tana nan? Magaji yace, ban sani ba sai dai ka kira wayarta, Yarima yace yau kwana hudu wayarta tana rufe, magaji yace to ka kira ta cikin gida mana? Yace bari ya yi hakan.

Umma ya kira bayan sun gaisa yace, Umma wai ya ya jikin bilkisu ne? Yaci gaba ina ta neman layinta amma shiru? Umma tace, jikinta da sauki babana, dazun nan ta shigo nan amma zan kirata in ji, yace to suka yi sallama.
Chapter 49 · 0% Book details