Sashe 31
Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yaya batun su Mamanmu? Duk wanda ya auri boka da ‘yan tsibbu lallai yana cikin dimuwa ba kuma zai gane ba,har sai ranar da karya ta kare,ga dai su Ladiyo nan anata fama yanzun ma da suke zaune gaba dayansu acikin dakin Karima suna tattaunawa ne akan duk malaman da suka je gurinsu,Salame tace abin kamar hadin baki malaman nan sunce mana inma an daura auren kwata-kwata ta dade tayi sati daya agidan mijin zai koro ta amma gashi yau mun shiga sati na uku.Ladiyo ta gyara zama ga kuma tsohon ciki tace yanzun ko bacci bana iyawa tunda akayi auren nan kullum ina raba idanu ne inga ta shigo gidan nan wutsiya zage,bani da buri sai na ganin bayan Bily.Karima tace kedai bari Ladiyo wallahi baki kaini ba,Ladiyo tace um um daina cewa ban kaiki ba,ni nan da kika ganni ko wannan cikin na jikina bana tunanin ranar haihuwarsa kamar yanda nake tunanin auren nan na Bily gashi kuma shiru. Salame tace mu koma mu sanar dasu aiki baiyi ba.Ni damuwata ma daya yanda mai adashen nan ke ta min sintiri naci na kasa zubi kudin da sune na bada muka kai gun malaman nan yaya tazo tana neman abin dauka, nace indai bani zaki dauka ba,ko yara ga sunan kwancar bani da wani abu dazan iya baki gaki dai ga dakin,in kinga abin dauka to dauki.Duk suka sa dariya,Ladiyo tace nima gado ne kurum yanzu ya rage min,Karima tace wa ma zai sayi wannan gadon naki,ko‘ina kudin cizo yayi kashi.Ladiyo tace eh,in zan saida ai dama wanke sa zanyi. Salame tace ai ko yaci klin din dari biyu dukkansu suka sa dariya,tace mu bar dariya mu fuskanci matsalarmu fa?Haka ko sukayi,washegarin ranar suka shiga mota suka nausa.kusan duk bokayan sunce musu kada su damu,aikin zaici ahankali. Shiko asalin bokan nasu cewa yayi yana zaton ma fa anyi sakin kila uwar yarinyar taki yarda su sani ne,sannan takai yarinyar gurin ‘yan uwanta.Ya kara musu da cewa haba ku sai kace ba mata ba?Ku kanku ma fa sharri ne mai zaman kansa cikin irin siyasarku ta mata da kissa ai kwaji koda gurin mijinku ne.Kai ita kanta yanayin amsar da zata baku zaku iya ganewa, suka ce hakane.Ladiyo tace malam sai dai fa maigidanmu da kake cewa zamuji gurinsa wallahi yanzun ya juya mana baya tunda yarinyar ta samu dan sarauta shikenan duk ya birkice mana.Malam yace a‘a kuce akwai sabon aiki kenan,to kuna da kudi ko?Suka ce zamu nemo, amma don Allah ai mana aiki mai kyau,yace musu don wannan kada ku damu,an gama kuzo dai da dubu takwas,sannan da kaji biyu.Suka ce to sun gode,sannan suka muke suka dauki hanyar gida.Allah kasa mufi karfin zuciyarmu, amin. Suna shigowa gidan sun samu Mamanmu zaune tana yiwa auta tsifar kai,nan suka kyafta ma juna ido alamar su bigi cikinta,don haka sai suka hada baki gurin yin sallama.Mama ta dubesu ta amsa,sannunku da dawowa suka ce yauwa. Karima tace munje barka ne matar wan Salame,cike da fara‘a Mama tace,Allah sarki to Allah ya raya,ai da kun gaya min da munje. Salame tace umh ni ai gani nayi na gaya musu bikin Bily sunki zuwa, shiyasa nace bazan gaya miki ba tunda abinba tsoro bane,su basa son zuwa
[4:36AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 55ðŸµ
Amma suna son aje musu.Mama tace,kai sai kace bin bashi?Ai lada ne in naje din,to Allah ya raya suka ce amin.Ladiyo tace,auta anata shan tsifa ne?Mama tace eh wallahi kin ganta nan kitson tunna bikin maigado taki tsefe sa,taje tasa anmata kitso yangu-yangu kuma sai da nace kar tayo kanana,amma da yake tana da kunnan kashi sai da tasa aka mata shi.Ladiyo tace ai duk haka suke,itama uwata gashi nan dama ita ba gashi ba yana nan kan duk yayi dugu-dugu ni dai ai bani da lokacin tsifa.Mama tace nifa tunda taki tsefewa ai tasan tawa tsifar sai na fece kai tas ta mun kuka in nade ta.Salame tace da kina can gidan amarya ai da kin huta.Asma‘u tace ba Mama ce tace adawo dani ba.Karima tace,ina ruwan amare,ana can dai.Duk suka kalli Mama suga yaya fuskartata zata nuna?Mama tace,um suna can,sun ma tafi ni wacce kasa ce inda mijin ke karatun likita.Gaba dayansu suka ce me?Cikin Ladiyo ya shiga juyawa,Mama ta kallesu saboda yanda taji sun hada baki,Karima ta wayance tace,a lallai Allah ya bada zaman lafiya. Asma‘u tace Mamanmu sunan kasar wai Malesia inji anty Mansu.Ai tuni suka sulale kowacce ta shige dakinta zuciyarta tana zogi tare da son tuno MEKE FARUWA ne?Abubuwan suke zo musu ahaka?
Sumayya taja tsaki sannan ta kashe wayarta,anty Salma ta dubeta ke kuma dawa kike tsaki? Sumayya tace,wannan Magajin Malam din mana ya dame ni wai ni yake so,ni ko gaskiya be min ba.Anty Salma ta harareta,sannan tace to menene aibun Magaji?Momy ‘yar gidan anty Salma itace ta uku tana da kannai da kuma yayye guda biyu maza,tace Mama ita fa Sumayya wai uncle Yarima take so,lokacin bikinsa duk inda mukaje sai tayi kuka.Anty Salma tace ai da kina sonsa kika yi shiru?Sumayya tace, wallahi Ummanmu ce ta hanani magana.anty Salma tace,to ba gara ke ba,da wannan ‘yar matsiyatan. Momy tace,ni ko ina sonta Mama tana da kyau.Anty Salma tace, ja can sakarya tayi ta kyannata mana,sannan ta dubi Sumayya tace,karki damu bari ya gama karatu ya dawo sai mun hadaku. Ai dama itama wannan ba wani sonta yakeyi ba hadinsu mai martaba ne da Modibbo. Murna Sumayya ta hauyi yayinda Momy ta shiga turo baki itama tsarar Sumayya ce Momyn.Tace to baga Magaji yana sonta ba,Sumayya tace to ni bana sonsa Momy ta taba baki sannan ta tashi ta basu guri.Umma ta kira lambobin gidan nasu Yarima na can Malesia ta hanyar land line har sau uku ana ukunne madam dora ce tazo tana buga ma Bily kofa domin Yarima ya fita,Bily taso taki daukar wayar don ita tun fitowar da tayi daren jiya datayi mugun gani koda ta daga wayar jin muryar Umman Yarima yasa tajin wani sanyi,tace sannu Umma ina yini? Suka gaisa tace ina baban nawa?Bily tace ya tafi makaranta,Umma tace ina fata dai kuna nan lafiya babu wata matsala ko?Ba komai Umma cewar Bily,to kiyi ta hakuri dai kinji ko?Tace to Umma. Umma tace yauwa ‘yata ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari,nasan Yarima sarai ki ta hakuri tace to Umma,to na gaisheku in yazo kice masa na kira ina gaidasa, tace to mun gode,zan gaya masa.Ta lura yana shigowa ne karfe hudu, don haka kafin hudu ta shiga kitchen tayi ‘yan girke-girkensu na hausawa,sannan tayi wanka,kwalliya tayi sosai irin wadda ake mata, sannan ta saka wani leshi mara nauyi kalar sararin samaniya,riga ne da siket tayi kyau ta saka gwala-gwalai kunne da wuya,da kuma yatsunta,tayi kyau sosai.Yau sai biyar ya shigo shida wani abokinsa dan Africa ne mai suna Saddik,tunda tazo sai yau ta gansa da musulmi,ta fito tace masa sannu da zuwa.Ya kalleta wani takaici ya cikasa aransa yace,har abada wannan ba zata waye ba,yace ai ke yafi dacewa ayi miki sannu, ko don wadannan kayan da kika lafta wa jikinki.Taji zafin maganar, amma sai ta daure tace Umma tana gaisheka, daxun tayi waya hanyar dakinsa yake tafiya amma sai ya dan tsaya ba tare da ya juyo ba yace me tace? Bily tace,ta gaishe mune kawai.Ya shige daki, ta dubi bakon sannu da zuwa ta masa cikin harshen turanci,sai taji ya amsa da hausa duk da hausar tasa batayi gargar ba,suka gaisa ta nufi daki.Bako Saddik ya bita da kallo,sanda tare da shiga daki gaban madubi ta tsaya bata ga aibun kwalliyarta ba,amma har yana wani cewa ta lafta ma jikinta kaya
[4:39AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 56ðŸµ