← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 60

Sashe 58

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hankula sun tashi ana ta nemanta,ita ko tana can tana zamanta gidan Mansu na Kaduna,ta kashe wayarta,bata bukatar ji daga kowa kuma ba wanda hankalin sa yaje gurin.mai martaba daya samu labari ranar Yarima yaga bacin rai irin wanda bai taba gani ba,sannan mai martaba ya bashi kwana uku rak mazamaza ya nemo inda Bily ta shiga inko ba haka ba zaisa a tsare sa har sai an ganta.al‘amarin ya wuce duk yanda Yrm ya zata,domin wai don ma basu ji dayan ba.Waziri da Magaji sune suka roki mai martaba kan batun tsare Yarima,amma fa yayi fushi dashi sosai daidai da magana ta daina hadasu, ko Yrm ya gaisheshi baya amsawa.ranar data cika kwana goma cikin dare ta kunna wayarta,sakwanni tayi ta gani suna shigowa na Yrm ne,tayi ta delete bata karanta ba,amma nasu Mansu,Magaji,su Sakina da Maryam harda auta,kowa dai rokonta yakeyi ta dawo,hankula sun tashi Magaji har abinda mai martaba da Umma suke ma Yrm sai daya shaida mata sai taji dan sanyi cikin ranta damuwarta iyayanta,don haka sai ta tura ma Mansu text cewa tace suma su kwantar da hankalinsu tana nan lafia,sai dai bata Kaduna in lokaci yayi wato in Yrm ya saketa zata dawo ta tura sannan ta tura ma Yrm cewa,tana fa jiran sakon sakinta,tana tura masa ta kashe wayar. Lokacin da sakon ya shigo yana zaune kan sallaya ya idar da nafilfilun da suka zamar masa a madadin bacci yanzu,yana ta addu‘o‘i gani yake tunda iyayansa suna fushi dashi bama zai ganta ba,shi dama zasu barshi da zafi gami da radadin rashin ganinta domin yanzun da baya ganinta dinnan yafi kowa tashin hankali,ya yarda sonta ne ya kamashi tuntuni bai gane ba sai yanzun.ganin sako ya shigo da sauri ya dauki wayar yana dubawa,jiki na bari ya soma kiran layin a kashe.haka yayi ta kira har ya gaji,yanzun yama daina zuwa asibiti,kuma sai yanzun yayi kukan rashin Modibbo,yasan da yana nan da iyayansa ba zasuyi fushi dashi ba,yaji da batan masoyiyar tasa. Mansu sun wuce Gombe bayan Bily ta shaida mata cewa tana nan lafia lau,sai dai bazata sanarda ita inda take ba,wasa-wasa shiru har sai da aka kai dasa rokon Allah ko ta wane gefen,gurinsu Umma ne gurinsu Mamanmu ne Allah ya bayyanata,su Umma yanzun sun sassauta ma Yrm saboda ganin halin da yake ciki,duk ya sukurkuce jin cewa su Mansu sunzo Gombe ya nufi Gombe ko zai samu wani labari.Yrm da kansa ya zauna gaban Mansu yana shaida mata cewa alhakin Bily ne yake binsa,Allah ya jarabce sa da sonta,yace kalleni kiga yanda na dawo shin baki sami wani labari daga beauty ba? Tausayinsa ya cika Mansu,tace tayi min text cewa tana nan lafia,yace to ni dazan san inda take wallahi ko ina ne zanje kome zata min indai zata huce zan yarda,tana da hakuri,Mansu tace,ai tasha a nonon hakuri ne haka mahaifiyarta take ya gyara zama don Allah bani labarin beauty mana? Nan ko Mansu ta zauna ta zayyane masa komai,sai kawai taga hawaye yana bin kumatunsa,dama cikin mafarki Bily ta soma saninsa?Lallai aurensu hadin Allah ne,dama tasha wuya agidansu?Yanzunne ya gane taki zuwa gida ne saboda kada kishiyoyin Mamanta suyi mata dariya.lallai bai dace ya wulakanta Bily ba tun farko lallai ya mata laifi dayawa.Mansu tasha mamakin ganin Yrm yana kuka,mai saka mata kuka yau gashi yanayin kuka don mace lallai gara da Bily ta tafi gashi sanadin haka ansamu cigaba, domin su anty Salma ma mai martaba ya saba musu yace dasa hannunsu Bily ta bace,kuma yana fushi dasu bazai gushe ba sai sun roketa gafara.Faruk yazo kuma sun lallashi Yrm, daya dawo hankalinsa yace yana so ya taimaki iyayan Bily amma kada suce sai da ‘yarsu ta bata,Mansu tace bazasu ce ba,shida Faruk da Magaji suka je zaria inda suka samu shahararren mai gini ya tsara musu yanda za‘a maida kafdin gidan kirar zamani ba tare da an shiga hakkin kowa ba,nan ya yarda da aikin yace kuma yana bukata cikin gaggawa Abu indai da kudi yanzun ne sai gashi cikin sati biyu an tsara guri,matan gida kuma duk sai kowa ta koma neman shiga gurin Mama,gefen su Mama yafi kyau ga kayan alatu daya zuba musu,ya saiwa malam wanda yanzun ya koma Alhaji Mamman tun shekarar da suka je makkah,katon shago yasa akayi daga waje ya cika masa da kayan masarufi na saidawa,sito kuma cike da abinci,lokacin Yrm gani yake koda zai karar da dukiyarsa bazaiji komai ba.su Ladiyo anga babu sarki sai Allah an hakura, domin dai nagaba yayi gaba wadda suka tsana yanzun arzikinta suke ci.hassadar da sukeyi baya suke ci ba gaba ba.Yau watansu Mansu guda da kwana goma tuni sun soma shirin komawa gida,don ma sun tsaya ne sunsha sunan Sumayya,ta haifi ‘yarta mace,inda Yrm ya rada mata Bilkisu.sai da suka bita zaria sannan suka wuce,abinda Mansu ta rinka tunawa tana dariya a mota,lokacin da suka je yiwa Mama sallama,sai ta samu su Goggo amarya(kakarsu Bily)zaune a falon Mamanmu suna kallon TV.Ladiyo kuma an leko cikin falon tana cewa yaya gashi na fere miki doyar ai Goggo kuna kallo ne?Nima bari inzo in kallata. shima Faruk sai daya dara da Mansu ke bashi labari.abin al‘ajabi suna shiga farfajiyar gidansu sai taga motar Bily ta fito da sauri tana cewa abban dady ko dai nan gidan Bily tazo?San da suka shiga tana bacci kan kujera, gabanta kwalbar maltina ce da plate din farfesun kaji.duka Mansu ta dada mata tare da cewa,‘yar iskar nan dama kina nan?Bily ta tashi tana dariya tace,kash!Da nasan yau zaku dawo dana cigaba kafin kuzo,Mansu tace wannan ‘yar duniya ce dama nan kike?Kin shammace mu kina nan kici goma ki tsoma biyar,lallai ‘yar duniya kin wahalar da Yarima kuma sai Allah ya saka masa.ta daure fuska wane abu ne kuma Yarima ?Don Allah kadaki sani nayi amai, Faruk kuwa mamaki ne ya hanasa magana,sai dai kallon Bily yakeyi,Mansu tace dole ka rasa bakin magana.Mansu tana shiga daki ta kira Yrm tace yazo ga Bily agidansu, sannan ta sanar dasu Mama.yarima jin abin yayi tamkar mafarki,a gurguje ya nufi toilet yayo wanka yana fitowa ya kira Magaji awaya cewa ya shirya suje Kaduna anga Bily,suna mota ne Magaji ke cewa da munje kayi aski gami da gyaran fuska,yace muje zanyi acan.cikin dare suka iso,Mansu lokacin ta soma bacci,Bily kuma tuni tayi baccinta,suna shiga Mansu ta nufi kiran Bily,tace wallahi bazata fito ba dole aka kyaleta Faruk yakaisu masauki.b bacci ranar Yarima baiyi ba gani yake inya kwanta zai farka yaga cewa cikin mafarki ne.babu yanda Mansu batayi ba ta fito su hada abin karyawa takai musu,tace Allah ya tsareta. Koda Mansu ta gabatar musu da kari,sai Yarima ya debe tsammanin ganin Bily,harma yace Mansu ban taba zaton zaki tsokane niba,zolayata kikeyi ashe.tace kai dai kugama tana zuwa,sam ko sha‘awar karyawar baiyi ba,ya koma ya zauna can kuma harda kuka Bily wai ita bata ko son ganin Yrm.Faruk shida kansa ya shigo yace dan Allah tazo,tana kuka tace kayi hakuri baban dady bazan iya kaffara ba kan cewa bazanje ba.ya mike ya fita kai tsaye gefen bakin ya nufa yace suzo ta hada kai da gwiwa suka shigo da tasan zasu shigo data shige toilet,Yrm yana yin arba da ita da sauri ya nufi gurinta kusa da ita ya zauna tare da cewa, beauty!Da sauri ta dago idanu jajir ta zabga masa harara.yayi murmushi tare da yin ajiyar zuciya, sannan ya mike ya kalli gabas ya tsugunna yayi sujjada,yana daga zaune agabanta yana kallonta shi duk tausayinta yake ji tunda yaji tarihinta agurin Mansu.yace beauty ki min duk abinda kike so nidai bukatata ki yafeni bazan kara ba,na dauki alkawari tsakanina da Allah.ta dubesa kabani takardata cikin mutunci kafin mukaiga kotu,yace kin manta ne beauty aure gidanmu ba‘a saki,har sai mace tazo da alfasha, keko saliha ce.ya dubi Magaji sa baki abokina, Magaji yayi gyaran murya sannan yace kiyi hakuri Bily kiyafe masa komai ya wuce,tace Magaji ina ganin mutuncinka kayi shiru kawai cikin wannan maganar,yace to nayi shiru Allah ya huci zuciyarki.
[8:43AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 92🏵
Chapter 58 · 0% Book details