← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 60

Sashe 46

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yarima ya gama komai game da course din nasa,wanda zaiyi Beverly Hills ta kasar America zaiyi course din ne akan gyaran fata,wato(plastic surgery)don yaga cewa bamu da wadannan likitocin anan gida,sai dai ya saita tafiyar tasane bayan bikin amininsa wato Magaji. Zaman Yarima da Bily su kansu yana musu dadi,duk da hakuri kawai takeyi da halinsa na saurin fushi da isa da kuma jin kai,sai dai tana kokari taga ta kauce ma duk wani abu da zaisa suyi sabani,tun daga ranar da suka soma kwana guri daya har yau babu wanda ya kuma tunanin kwana shi kadai,domin hakan yana sasu farin ciki.Daren yau saura kwana shida bikinsu Magaji,Yarima babu zama yi nan yi can,yau ita kuma Bily duk bata jin dadi sai dai tana sharewa ne domin ta fahimci tana da shigar ciki,wanda shi kuma Yarima ba ra‘ayinsa kenan ba, in har ya sani zasu yi rigima ne.ta shigo falon Yarima yana zaune yana duba sauran katunan wadanda ba‘a kaisu ga masu su ba,tace sannu da hutawa abokin ango,ya dubeta sai ya ajiye katin, zo kiji,ta isa gurinsa kin kara kyau yau sai dai yaya naji dumin jikinki yafi na kullum?Tace,ko, ya kuma mannata ajikinsa ko kina zazzabi ne? Tace a‘a kalau nake,ya dubi fuskarta muje in sai miki kaya irin na gayu ko?Tace muje to.Wani katon Boutique suka shiga,sam Bily bata ga abinda ya burgeta ba cikin boutique din,shi ko Yarima sai jidar kayan yakeyi yana ayyana yanda zai gansu ajikinta,suka koma gefen takalma nan ma ya diba haka aka biyo su da kayan ledoji cikin mota,takaici ya cikata babu halin ta nuna yanzun nan ya hau fushi sai dai tana ganin an kusa jin kansu indai ita yake nufi tasa kayan nan.bayan sun iso gida da zumudinsa yace ta gwada kayan,duk wanda ta dago sai ta gansa bingil daga siket din har wandunan rigunan kuwa daga mai hannu daya sai mai hannun singileti,sai wadda sam bata ma da hannu Ta dubesa wai kana nufin ni sZan saka wadannan kayan?Ya murtuke fuska bansani ba,tunda ina da wata matar ne bayan ke?Don rainin wayo zakice ina nufin ke zaki sa?Tace tsaya kaji abin bana fada bane, bazan iya sa kayan nan ba,saboda ka duba gidannan gidane na jama‘a haushi ya turnuke sa yace me ya hana ki sanar dani tun a can,sai da nayi asarar kudina, dakin sani tunda mukaje sai kice kai nifa bazan sa ba, sai kika barni na siya sannan don kin raina min wayo yanzu kice bazaki sa ba,ta tausa murya baka fahimceni bane mijina,nifa saboda mutane ne? Yace to gurinmu da akwai mutane ne?Gaya min wanda yake shigowa nan gefen?Tace masu aiki zuwa su jakadiya,kaga bai dace ba,ransa ya sake baci afusace ya dubeta, shin wai ke harma kin isa mu tsaya ja-in-ja dake?To bari in sanar dake,nine wanda ‘yanmata suke son in nuna ina son kaya su sa kudinsu su siya don in gani a jikinsu inji dadi.ya mike tsaye yaci gaba da cewa,amma ke ko baki da burin daya wuce kiga raina na baci,ban san bacin rai ba sai dana hadu dake,please kwashe kayan nan kibar min dakin tun kafin ranki ya kai ga baci,in ma zaki kona ne jeki kona,ke kin gama rainani kin maidani tsaranki,tunda mu sa‘annin junane koba haka kike cewa ba?Zata sake yin magana yace,fita nace banason jin muryarki. haka ta kwashe kayan ta fita jikinta a sanyaye,shi kuma ransa bace ganinsa ta maidashi mara tunani karamin yaro tunda bai aunaba ya sayi kayan.lokacin kwanciya yanayi tayi shiri ta nufi dakinsa tana zuwa cikin dar-dar baya falo ta shiga bedroom tana shiga yana fitowa daga wanka,wani kallo ya watso mata tareda daga murya gurin cewa me kuma ya kawoki dakina? Sai data zabura sannan tace,yi hakuri ta daure ta nufosa kawona goge maka jikink..fita nace,bana bukatarki babu wata mace data isa in saurareta matsawar bazata min yanda nake so ba,matan waje ma suna min biyayya ballatana matar aurena,wallahi nina sani mata da yawa da zasu samu in auresu ko tsirara nace ina son su min yawo cikin gidana sunsan yanda zasuyi,don haka fita kawai kin bata min rai sannan ynzu kin wani debo jiki dan gani jarababbe ko?
[6:39AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 75🏵

To ki sani kwanciyar hankali ce take sawa ayi komai,haka Bily ta koma daki ta fada kan gado lallai ta tsokano,shima Yarima koda ya kwanta sai yaji daban,cikin ‘yan satukan sun shaku da juna musamman gurin kwanciya.Bily ta mirgina ta janyo filo ta dora akan kirjinta,kewar mijinta ce fal aranta,shima daidai wannan lokacin duk da ransa ya baci amma jikinsa yana maraicinta, hakan zuciyarsa zogi takeyi harma ya soma tunanin ko dai ya dauki waya ya kirata ne?Ya tashi ya zauna tsakiyar gado,ba wai sha‘awar tace ta hana masa bacci ba,a‘a zuciyarsa ce daga can kasa take tsananin son ta ganta.ya janyo waya zai kirata sai wata zuciyar ta soma cewa,shin ka yarda ka zubar da ajinka ka kirata?Tayi ma laifi fa?Kuma kaine ka koreta in harka kirata gobe zata iya maka abinda yafi haka tunda tasan ba zaka jure ba zaka sake kiranta.tsaki yayi sannan ya jefar da wayar kan gado,itama duk ta damu sai tana ganin cewa in har biyayyar zatayi me zai hana tayin yanda Yarima ke so, wannan duk laifinta ne yau gata zata kwana ita daya,tana kewar kamshin Yarima ,ranar ko an tafka ruwan sama haka suka kwana jin sanyi duk da bargo da kowannansu ya shiga sannan babu wani bacci sai juye-juye.Oh! Allah shin me yasa suka damu da juna haka?Da safe bayan Bily tayi wanka,nan ta soma daddaga kayan taga wanne ne ya dan fi dama-dama,tasa dan taje bandaki,shi ko Yarima kosawa yayi lokacin zuwa gaida Umma yayi don yaje gaisheta ko zai ga Bilyn,don zuciyarsa ta daina zugi.Bily koda kyar ta samu wani siket gashi dai har kasa dogo sai dai tsagu tun daga kasa har cinya,sannan rigar bata rufe cibiya ba,kuma daga sama duk kirjinta waje,sannan kuma baya ma kusan rabi awaje ta sama,haka dai ta daure ta saka tare da sa takalmi daya daga ciki mara tudu sosai,hijabi ta dora sannan ta fito,amma kafin ta saka hijabin sai data kalli kanta a madubi tace oh,dubeni sai kace ‘yar iska,ko irin ‘yan good evening din nan Tana shigowa falonsa na kasa shi kuma yana sakkowa, zogin da zuciyarsa keyi sai ya tsaya cak,wani sanyi yaji yayinda ya ganta tamkar ya ruga ya rungumeta sai wata zuciyar tace masa yana sai ka nuna mata ka damu?Nan take ya dake sannan yayi nufin fita,da sauri tasha gabansa sannan ta cire hijabin,wani dadi ya rufesa amma sai yasha mur,tace me zaisa ka daure,kalli fa banyi kyau ba ne?Ya kalli kwayar idanunta masu hanasa yayi mata gaddama,yace Beauty kina son ki bani wahala me yasa ko yaushe burinki raina ya baci?In zaki min adalci nima fa dole aka min kamar yanda kema aka miki,amma bana son in matsa miki ke ko kinfi son ki ta bata min.ta dubi fuskarsa na daina duk abinda kake so shi zanyi,yayi ajiyar zuciya sannan yajata zuwa kirjinsa, sai yaji tamkar sun shekara basuga juna bane,harma baisan lokacin da yace I miss you ba,sai dai yaji tace me too Nan suka manne juna,ji suke tamkar su shige cikin juna,ko saboda menene?Oho!Bayaji su kansu sun san dalili.Nan suka nufi falonsa suna manne da juna,sai gashi ranar tare suka karya, har ma Yarima yana tunani aransa cewa dama cin abinci da mace haka yake da birgewa?Duk sanda zaisa abinci a baki sai ya kalli idanun nan nata masu narkar masa da zuciya,tana murmushinta dake kara mishi sanyi cikin zuciya,koda aka jima sai ma ya barcin abincin bai san ya zuba tagumi yana kallonta ba.a zuciyarsa son yake ya gano shinme yasa ita wannan ta fita daban cikin duk matan da yayi harka dasu?Sauran ‘yanmatansa baya damuwa in sun samu matsala ko su zo ko kada su dawo ko ajikinsa, sannan duk lokacin daya gama biyan bukatarsa dasu,sukan fitar masa arai,sai dai ya daure amma wannan tunda ya hadu da ita ta sauya masa wasu abubuwan da dama shi ada baisan damuwa ba,baisan tunani ba, kullum yana samun kansa sayau ne,amma sanadinta duk yasan wannan,ga tunaninta gashi baya son tayi nesa dashi,haka nan duk lokacin daya kusanceta, inya samu nutsuwa wani sabon sha‘awarta ne ke shigarsa, kullum yana son yaji ta manne cikin kirjinsa,yana bala‘in son dumin jikinta.
[6:39AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 76🏵
Chapter 46 · 0% Book details