← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 60

Sashe 18

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wayar ta katse ba‘a dauka ba yaja tsaki sannan ya sake neman layin,ringing na uku Magaji ya daga wayar.Yarima yace,haba Magaji adinga rage bacci ana nafila mana,wannan bacci kamar ka mutu?Magaji yace,gara ma ni bacci nake,shima ibada ne wani ma ba‘asan ko shi da mata nawa yake ba,Yarima yace,na gode.Yanzu dai duk ba wannan ba,me kasani game da wannan yarinyar?Magaji yace,wacce kenan?Yarima yace,yarinyar da muka hadu gidansu Modibbo kawar matar Faruk din Umman Gombe?Magaji yayi ‘yar dariya tare da cewa,nasan dama wata rana sai ka min zancan yarinyar,domin irin taku ce.Ya dan saurara kafin ya cigaba,gaskiya bansan komai kanta ba,ni da farko ma na zata kun hada iri can cikin dangi.Tsaki Yarima yaja,sannan yace kada ka bani haushi fa Magaji?Tunda kace baka san komai kanta ba,na baka awa sittin da shida daga yanzun,ina son sanin who is she?Ya kashe wayar ba tare da ya jira jin me Magaji zai ce masa ba.Tun misalin goma na safe Magaji ya soma neman sanin Bily,da farko gidan Modibbo ya nufa gurin Hajiya Fati don son sanin wacece Bily?Don nan ya soma ganinta gurin Modibbo ya soma shiga suka gaisa,baice ma Modibbo komai ba game da bukatar Yarima na son sanin Bilyn ba.Sun dan taba hira har ma Modibbo yake cewa,ina labarin abokinka ne?Magaji yace,yana lafiya sannan yace,bari ya shiga su gaisa da kawu.Modibbo yace,kawunku yana Yola,na aikesa sai dai mai dakin tana nan ciki,yace to bari mu gaisa dama nazo gaisheku ne.Sun gaisa da Hajiya,sannan yace dama Hajia ina so in tambayeki ne shin ko kin san Bily kawar matar Faruk din Gombe?Haj.Fati tace,ikon Allah nifa nayi mamakin ganinka da safe tunda kuka zo Yarima na nan ba wani zuwa kuke ba sai sa‘a.Tayi ‘yar dariya sannna tace,wallahi ni ban santa ba,daga ita har matar Faruk din.Nima karo na farko kenan da fara ganinsu.Nan dai sukayi sallama ya fito,cikin mota ya soma tunanin wazai tunkara da wannan bukata?Yana ganin abinda sauki ashe duk ya wuce nan.Yayi tunanin to ko Faruk zai kira?Sai kuma yace,kai da Yarima yana son Faruk ya sani da shine mutum na farko da zai fara nema.
Nan Sumayya ta fado masa yarinyar da yake mutuwar so,yace bari ya kirata yau dai yaji muryarta tunda ya shiga ya fita da kyar ya samu number din ta gurin yaya Salma ya kasa kiranta,amma yanzu zai kira kila ma ya samu labarin daya fito nema.Dafda zata yanke Sumayya ta daga wayar duk da cewa wayar tana hannunta,haka nan bata gane ko number din wanene ba.Cike da yanga tace,hello! Ya lumshe ido don jin muryar da yake matukar so,sannan yace,Assalamu alaikum,Sumayya tace ,Wa‘alaikassalam,wanene please?Yace au baki gane ni ba?Tace,a‘a.Yace,to Magaji ne daga Bauchi,tayi ‘yar dariya.Oh,Magaji ban gane kaba,koda yake bamu taba waya ba,yaya Bauchi? Yace,Bauchi lafiya duk suna gaisheki tace,ina amsawa,yaya Yaya Modibbo?Yace lafiya,dama wani taimako nake so ko zan samu?Tace in baifi karfi na ba,ai bazai gagara ba,yace kin san kawar matar Faruk dinku?Tace anty Bily kenan,nasanta jiyannan muka dawo daga gurinsu.Yace,yauwa don Allah menene labarinta?Kamar ya?Ta bukata,yace,ina nufin kinsan tarihinta?Ta girgiza kai tamkar tana gabansa bansan komai kanta ba,face nasan ita ‘yar Zaria ce kuma ta gama karatu bansan me ta karanta ba,amma yanzu tana bautar kasa ne,yace to na gode,kina da number dinta ne?Tace,eh,amma sabuwar number dinta ne nace ta bani don ina sonta,kai ne zaka shiga?Yace ni wane ni,wani abokina ne.Da sauri tace,Yarima?Yace,a‘a.Tayi ajiyar zuciya har abin ya bashi mamaki,yace shikenan kiyi min text din number dinta,tace to.Da taso ta rokesa ya shigar da ita gurin Yarima,sai dai ta fasa,shiko zuciyarsa ta shiga rudu,kada dai Sumayya tana son yarima ne. Zuwa washegari,Magaji duk ya gama bige-bigensa shi dai bai gano komai ba game da Bilkisu,dole sai ya hada da zuwa Zariya.

Kwance agaban gidansa,cikin wani dan gado Yarima ne,daga gefensa Chelen ce tana sanye da Bra da pant,wasa takeyi da gashin kirjnshi,idanunsa lumshe zuciyarsa tana masa nacin me yasa yaba Magaji kwana uku?Ya matsu yasan ita wannan yarinyar ‘yar uban wanene

Ita ko Bily daidai wannan lokacin hankalinta kwance,tunda ta cire(mtn)ta saka(zain)sai dai bata yarda ba kamar yanda tasoyi da,saboda numbers din dake kan(sim)din,tana son ta ba Mansu labari sai sun zauna tukunna.Magaji ya shigo Zaria kai tsaye unguwar T/wada ya nufa gurin wani abokinsa da sukayi karatu a (University)nan Bauchi.Ibrahim dan Zaria ne,a unguwar T/wada.Da kwatance ya iso T/ wadan,nan kuma ya shiga kiran number din Ibrahim amma is switch off.Tun safe yake neman wayar taki shiga,nan ya shiga nemansa ta hanyar tambaya duk ba sa‘a,yayi parking nan kusa da wani Masallaci da nufin yayi magriba,zaije ya nemi masauki.Amma cikin yardar Allah yana sahun gaba sai kawai yaga Ibrahim a sahun gabansa.Don haka suna idar da sallah sai yasa hannu ya dafa shi,nan suka fita wajen Masallacin,Ibrahim yana ta mamaki.A dakin matar Ibrahim suna cin abinci,Magaji yana fada masa dalilin zuwansa Zaria,yace na shigo garinku ne don neman labarin wata yarinya Bilkisu.Ibrahim yace,ikon Allah!‘yar wace unguwa ce?Magaji ya kafa kofin ruwa yana sha,sai daya gama sannan yace,nan fa daya,wallahi bansan komai kan yarinyar ba,hasalima sau daya na taba ganinta.Ibrahim yace,to kai batayi maka kwatance bane?Magaji yace,nifa Bauchi muka ganta.Yarima ne ke sonta shine duk ya daga min hankali,yanzu haka gobe yake son jin ko ita wacece.Ibrahim yace,gaskiya ya baka aiki,Zaria tana da yawa,ta ina zaka soma nemanta?Magaji yace,shi yasa na biyo ta kanka tunda kaine dan gari.Babban misalin dazan iya badawa na yarinyar kawai shine,kyawunta nasan saboda tsabar kyanta bazata bata a unguwar da take ba.Ibrahim yace,to kafin a gano unguwar da take fa?Magaji yace to bari dai in mukayi Isha‘i sai mu soma tun yau.Haka kuwa,suna idar da salla suka shiga gari.Da G.R.A suka soma don zaton Magaji na ko ‘yar wani mai halince,gida-gida suka dinga bi cikin G.R.A sune har sha daya da rabi.Washegari ko suka soma da T/Wada,S/ Gari,haka sukayi ta yawon neman inda zasuji labarin Bily,amma shiru.Bayan sunyi sallar La‘asar,suka shiga Ojo da har zasu wuce amma MGJ yace su shiga.
[8:47AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 31🏵
Chapter 18 · 0% Book details