← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 60

Sashe 30

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya shigo pallon umman shi rai bace Bily yana ta fadin shi gaskiya an takura mashi tare da nuna billy wai umma da wannan abun zan tafi ai kau umman ta hau shi da fada sosai ita ko billy kanta na kallon kasa tana ta sharar da hawaye, Yarima ya mike ya fita Bily ta daure ta dubi Umma tace Umma nima nafi son abarni anan.Umma tace a‘a Bily banaso kice komai kinji ko,ke dai kiyi ta hakuri sannan kici gaba da addu‘a,share hawayenki kinji ko?Nan take tace to Umma,Yarima ya rasa yanda zaiyi dole shi suka je shi da Magaji suka kammala mata komai,yana ta zafin rai,ai ko suna dawowa har daki ya same ta yayi mata tatas,yace in har kika bini dama kisan kin nemi maganin hawan jini dana ciwon zuciya,don kam kaken dana miki yanzun ne zaki gane dalili,sannan in har kika sake, kika tafi da wata kuyanga bana ji ana wani cewa ai musu biza ba tun cikin jirgin zan turo ki in huta,kinsan zan iya banza wawuya ‘yar matsiyata ya fita,kukan da Bily tasha ranar babu iyaka daga karshe dai ta hakura ta kira Mansu ta gaya mata komai,Mansu ma hakuri dai ta bata,Bily cikin kuka tace,Mansu yaushe zanji dadi ne irin na kowa?Wai ni MEKE FARUWA dani ne?Haka zan dawwama Mansu,wallahi dana so aure saboda kuncin rayuwar gidanmu amma yanzu ga aure ga daula amma gara zamana na gidanmu gara ina gaban Mama su Gwoggo Ladiyo suyi ta min gorin yafi min yanzun.Mansu ma ta soma kuka tana cewa kiyi hakuri wata rana sai labari,haka suka yi sallama zukata abace.Sai da tayi kokari ta natsu sannan ta sake kiran Mansu tace mata ki kula min da Mamanmu.Mansu tace,kinsan wannan dole nane,ko baki ce ba,ni dai fatana ki kwantar da hankalinki duk me ya miki ki daure ki sama ranki cewa kina ibada ne,kinsan kuma bautar Allah sai da hakuri na sani kin sani no condition is permanent. Allah ma ya fada cikin Alkur‘ani kowane tsanani yana tare da sauki,lokaci yana zuwa da zakiyi dariya aminiyata cike da jin dadi Bily tace na gode Mansu,naji dadi insha Allah maganganunki zasu zamar min abin tunanina, duk lokacin dana shiga kunci,sukayi sallama katan guda biyu cike da begen juna. Yanda taga rana haka taga dare, tunani ne ya cika zuciyarta MEKE FARUWA da ita?Me yasa bata da sa‘a ne ita arayuwarta?Duk yanda Mamanta tasha wahala kanta ta kyautata rayuwarta taso kwarai ta samu mijin da zai kula da ita da mahaifiyarta,amma sai gashi wani can wanda bai san kimarta ba marar tausayi mara imani wanda in aka tsare sa koda bindiga ba zai nuna mahaifiyarta ba ya aureta ya kuma sameta abudurwa bai ko kula da hakan ba,wanda ada ita taci buri sosai akan budurcinta,domin tasan abin alfahari ne sai gashi amma shi ya keta ta ba tare da yako juya ba.Shin wane zama zasuyi a Malesia?Tasan sai tayi hakuri tasan zai bi mata,tasan sai dare zai dinga dawowa,tasan yana zuwa club,kila ma wata rana yazo mata a buge, tunani dai barkatai,lallai ta bakin nasa ta nemi maganin ciwon xuciya. Tun shigowarta gidan yau ce rana ta farko da taga ainahin gidan,mutane tankam an fitar musu da kaya,Umma dai tana ta nanata mata cewa,lallai in taji yaya ne ta kirata ta shaida mata,shi kuma taja masa kunne cewa ya kula da ita don ita din amana ce agaresa,kuma ta yabesa da cewa dama kai mai alheri ne,don haka ka lura da ita ka wadatata nan ya tuno da batun Modibbo jiya da yaje masa sallama,yace takwarana don Allah ka lura da matarka sosai,ka sani yanzu ka shiga wata rayuwa ce mai daraja kuma kaima ka zama cikakken mutum,yanzun ka kula da karatunka banda shirme.Yarima yace,insha Allah na kuma gode,an raka su zuwa filin jirgin sama inda Bily ta kara yarda Yarima dan gata ne,saboda ‘yan rakiyazuwa jami‘an tsaro ne,suka shiga jirgi zuciyarta cike da addu‘ar hawa abin hawa,inda Yarima ya zauna kusa da wani tana ta hangen inda zata zauna kusa da mace ‘yar uwarta tunda shi bai damu su zauna tare ba,don haka sai ta zauna ita daya akujerarta,wani kuwa yana shigowa ya zauna kusa da ita tare da gaishe ta,ta amsa tana satar kallon Yarima,don suna gabansa ne shi kam ko kallo bata isheshi ba,haka nan da jirgi ya tashi mutumin nan ya dameta da surutu har dai ta gaji ta soma baccin karya.
[4:31AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 53🏵

Kai jama‘a!Anya mutane ana cewa babu kudi babu kudi,shin gaske ne?Gidansu take kallo tana fadin haka cikin zuciyarta tana tsaye tsakiyar falon gidan Yarima tana kallon tsarin falon irin dai gidajan da take gani cikin fina-finan turawa ko mujallarsu. Yarima ya nuna mata dakinta yana kusa dana sa ne,ta shiga gado ne madaidaici sai durowoyi wordrop da dai dan sauran abubuwa,ta kintsa daki duk da dai bashi da datti,ta shiga bayin karami ne ta tsaftacesa sannan tayi wanka da alwala wata tsohuwar baturiya ta shigo tana dauke da tire,tarkace ne ita jus din kawai tasha sam bata san wannan tarkacen ba,har wayewar gari bata fito ba,tunda tana da bayi kuma tazo da dambun nama dana kifi wanda Umma tasa akayi musu don haka bata da matsala,dama bata yi zaton Yarima zai nemeta ba,kuma hakance ta faru.Da safe ta lalubi kitchen taje shima ya tsaru,madam Dora tana ta ‘yan aikace-aikacenta suka gaisa,Bily ta soma hakilon neman abin karyawa,tea ta hada ta soya kwai babu ko bread taci kayanta ta koshi anan kitchen din take suna hira da madam Dora inda madam din take shaida mata cewa tana da kyau,shin ita ‘yar wace kasa ce?Tace mata ‘yar Nigeria ce,sai tace oh,ta manta dama Prince ya gaya mata cewa ita kanwarsa ce.Bily batayi mamaki ba tace,eh hakane.Madam Dora tace dan uwanki yana da kirki sosai,tun farkon zuwansa nan kasar nake masa aiki ni da sauran ma‘aikatan yasan darajarmu yana mana adalci.Bily ta danyi yake tace ai hakane halinsa yake,tace koya sunanki? Bilkisu inji Bilyn ta shaida mata madam ta kasa sai dai Bikis haka ko taci gaba da kiranta.Da dare tana zaune afalo tana kallon wani fim,zuciyarta ko tana tunanin cewa tunda suka zo bata ko saka Yarima cikin idanunta ba,sai gashi ya shigo kamar ta share shi,sai dai ta daure tace masa sannu da zuwa tamkar baiji ba kuma tasan yaji don haka ta share shi kusan awa daya ya fito cikin ‘yar T-shart fara da 3 kwatan wando ya nufi kitchen mai hade da dinning room.Can dai tana zaune sai taji wani abu yana kara,ashe intercom ne sai taga madam Dora tazo ta bude.Wata mace ce ta shigo tana sanye da siket da iyakar cinya,sai ‘yar bes kana ganinta kaga chanis,suka gaisa da madam sannan ta nufo ciki tana tambayar madam ko prince na nan?Madam tace yana dining room can ta nufa,madam tazo tayi ma Bily sallama da cewa zata gidanta don basu da nisa,Bily tace to mu kwana lafia sai dai tanayi zancen ne kawai amma zuciyarta na gurin su Yarima,shin wacece wannan?Jim kadan suka jero ita da Yarima suna ‘yan hirarrakinsu,suka zube nan falon.Tamkar a fim ko cikin mafarki sai ganin Yarima tayi yana wasanni da wannan macen,sam tamkar basu san da mutum agurin ba.Kasa jurewa tayi ta mike ta shige dakinta kan gado ta fada,har yanzun bakin Yarima take gani cikin na wannan matar, tasan bata son Yarima amma dole ne tayi kishin mijinta.Kai ko ba mijinta ba ba zata so taga wani musulmi yana kusanta kansa da zina ba,bare har ya aikata.Tasha kuka daga baya tayo alwala ta soma nafila tana kaima Allah kukanta.Washegari ko da safe misalin goma tayi yo kwalliyarta cikin super riga da zani tayi kyau,tana zaune kan dining tana karyawa ya shigo cikin shirin makaranta.Madam dora ta mika masa dan kofi da plate coffee ne aciki yana sha,suna gaisawa tana masa korafin sister shi tafi son tayi girki da kanta,yace eh ko gida ma haka take.Madam tayi ‘yar dariya sannan tace kuma Bikis tana da kyau,sai ya fita daga kitchen din yana cewa,chelen tana jiransa bari yaje.Can hanyar fita ya nufa,sannan ya aje kofin da plate din ya tafi abin tsoro mata gidan Yarima wasu suna shigowa wasu suna fita,kuma karka ga yanda yake wani shassha musu kamshi,abinda kullum ke bata mamaki har yau da take satinta daya agidan bai taba mata koda magana ba kuma koda ta gaishe shi baya amsawa, haka nan baya damuwa ko agabanta ne yayi yanda yake so da ‘yanmatansa hakan nan in sun nemi sanin ko ita wacece agabanta zaice kanwarsa ce.
[4:35AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 54🏵

Hankalin Bily bai gama tashi ba,sai daran ranar data cika kwana goma a kasar.Ta fito zata kitchen saboda tana son tashi da azumin alhamis,me zata gani?Yarima ne da mata guda biyu tamkar zasu cinyesa,kowace tana son nuna masa karshen soyayyarta,kuma tana son burgesa har ya juyo gurinta,cikin tsananin tsoro tace, A'uzubillahi minash shaidani rajim.Suka dubeta su biyun banda Yarima wanda ya rungumo su duk da ya ganta juyawa daki tayi ko ganin hanya batayi don tashin hankali cikin sanyin jiki ta zauna tama rasa wane tunanin zatayi ne?Kodai don bata kai kanta garesa ne yake kawo su gida don ya bata mata rai?Inko haka ne ai gara ta kai kanta gurin nasa koda zai riga mata fyaden ne in dai zai daina kawo wadannan matan masu kama da bebyn roba ta sani ba sun fita kyau bane ta sani ba wai tana son Yarima bane sai dai tasan in don rashin zuwa gurin Yarima ne yake zuwa ya kawo mata,to tabbas tana da kamashon zunubi,kila ma nata yafi nasa.Tabbas Yarima baiyi kuskure ba daya ce ta nemi maganin ciwon zuciya dana hawan jin,har gari ya waye tana tufkawa tana warwarewa.
Chapter 30 · 0% Book details