Sashe 57
Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Na baka guri ka shakata sannan kasani bazan iya zama dakai ba, ka kasa tsaya wa akan halalin ka alhalin ban rage ka duk wani jin dadi ba. Baka sona baka son karuwa dani, burinka in mutu gurin cire min ciki ta hanyar da kai ka sani ni bansani ba, amma naje gurin likita ta min bayanin komai dama ance duk mutumin da baya kaunarka zai iya yi maka komai ciki harda neman rayuwarka. Da fatan daka samu sakona zaka rubuto min sakina koda ta waya ne sai ‘yan uwanka su aura maka wadda suke so ‘yar masu kudi kuma wadda zata tara musu ‘yaya kamar yarda suka ce,tana turawa ta kashe wayar gaba daya.shiko Yarima yana ganin sako ya shigo ya duba ai a rikice ya nufi gida, ta tabbata nan kuma babu motarta yaje yace ma Umma ina Bily? Umma tace ni ban sani ba bata nan ne?Yace a'a na zaci tazo ne ya fita,gidan Umma ya nufa yana tafe yana neman layinta amma a kashe,bayan sun gaisa sai yace shin ko Bily ta iso?Umma tace ta nufo nan ne?Yace dana ce tazo ne ina zuwa kila tana gida ya fita duk inda yasan Bily tasansu sai da yaje har magariba ta shigo ya dawo gida ta gurinsu Umma ya shigo tana sallah son ma yana ta binta sallar.ya fita ya nufi sasansu,ya daure ya watsa ruwa sannan yayi sallah ya ci gaba da neman layinta shiru sannan ya kira Magaji bai boye ma Magaji komai ba,Magaji yace shikenan gaskiyarta ne tunda ta tafi ba sai ka huta ba? Haushi ya kama sa yace haba Magaji na kiraka ne fa don ka taimaka min yanda zan bulloma al‘amarin ka kuma dauko wata caftar, Magaji yace to in ba haka ba me zance?Yarima yayi shiru can yace da zan iya dana ce tayi tafiyarta amma na kasa ba zan iya ba, cewa fa tayi wai in sake ta? Magaji yace ka saketan mana to yaja tsaki,sannan ya nuna ma Magaji kofar fita,fita baka da amfani,Magaji ya mike ya fita Yarima yabi shi da kallo. Bacci ranar sai dai barawo amma kasa bacci Yarima yayi,baya son su Umma susani amma dole ne suji,sai dai zai ce musu taje gaida iyayenta ne,to kuma zasu ce babu ko sallama?Haka yayi tayi ya saka ya kwance,har gari ya waye.Magaji daya koma gida sai ya kira layinta yaji sa akashe, washegari ya fito ya shiga gidan sasan Yarima ya shiga lokacin Yarima shima ya gama tunanin cewa dole ya koma gurin Magaji,domin shine yasan zaria, kai shi abin kunyar nasa ma yana da yawa shekara nawa shida matarsa bai san kowa nata ba sai wanda ya kawo kansa yanzu gashi zai je dalilin yana bukatar ta dawo?Magaji ne ya katse sa da cewa abokina yaya ne? Yarima ya dubesa mun tashi lafia?Lafia lau inji Magaji sukayi shiru can Yrm yace ko can gidan iyayanta zamuje? Magaji yace to sai muje,kaga kaima tunda yanzun tayi dalili sun san kai Yarima yace to sarkin sheri naji yanzun yaushe zamu tafi?Magaji yace ko yaushe,Yarima ya mike yace jeka shirya mu tafi.sun iso zaria misalin karfe biyun rana,unguwar suka shiga kai tsaye, kallon unguwar yakeyi yana mamakin dama beauty a irin wannan unguwar take?Duk da an ce iyayanta talakawa ne da za‘abarsa inya iso(G.R.A)zai nufa nemanta,bai kara tsinkewa ba sai da suka tsaya akofar gidan,yace Magaji don Allah nan ne gidan iyayan beauty?Magaji yace tabbas Yarima yace,amma baka kyauta min ba da ka kasa sanar dani kamar ni ace surukaina suna cikin wannan gidan, ai samuna yazama na banza.Magaji yace lokacin gyaran ne baiyi ba shiyasa Allah bai horeni da sanar dakai ba amma yanzu ai kaga lokacin yayi tunda ance gani ya kori ji.suna fitowa daga mota Asma‘u tana fitowa daga gida,tace a‘a yaya Yrm sannunku da zuwa,Yrm cikin zumudi yace Asma‘u beauty tana ciki ko?Asma‘u tace wace antynmu?Yace eh,tace bata zo ba.Magaji yace babanku yana nan?Tace yana ciki,yace to shaida masa ga baki. Da sauri ta koma tace Mama ga yaya Yrm mijin anty,ta mike da sauri tace,to ina malam kirasa dakin Salame ta sanar dashi da sauri ya fito sai daya canza ‘yar riga mai haske sannan ya fita wajen yayinda Umma ta shiga gyara gurin. malam ya shigo dasu Asma‘u ta fita siyo musu lemu mai sanyi.Yrm cikin tausayi yake kallon gidan hakama dakin,bayan sun gaisa Asma‘u ta kawo musu swan water mai sanyi da lemu,Yrm dai ruwan kawai yasha.Magaji ne ya gabatar da Yrm, sannan yace sun zo ne su duba ko Bily tazo gida,s saboda wata ‘yar matsala da suka samu.Mama ta kalli malam shima ya kalleta sannan yace ikon Allah,amma ko daya ban zaci haka daga gurin Bily ba,domin yarinya ce mai hakuri,amma kunga bata zo nan ba,tun yaushe ne?Magaji yace jiya ne. Yarima ya cire hula saboda wata zufa data feso masa,a hankali ya furzar da wani huci mai zafi.sannan yace,ni babbar damuwata bata da isasshiyar lafia,to amma baba ba kuji anan din akwai inda zata?Malam yace kun duba cikin gidan Umman Bauchin kakarta?Magaji yace duk bata can,Mama ta nisa tace kun tuntubi Mansura?Duk da dai Mansu ma tana nan zaria,kila gidan Mansu taje.tunda kunce jiya ne ni kuma shekaranjiya Mansu tazo nan,nan aka hada su da Asma‘u zuwa gidan Mansu,sun samesu har Faruk dinma yasha mamakin ganin Yarima a gidansa.Mansu ta musu kyakkyawar tarba sai dai Yrm ya kasa cin komai domin baiga beautynsa a gidan ba,sannan bai tsaya kwauron baki ba ya shaida ma Faruk dalilin zuwansu.cikin mamaki Mansu tace,Bily tabar gidanka?Yace wallahi tun jiya babu inda banje ba,Mansu tace shiyasa na dinga neman layinta shiru?To ina Bily zata?Wai ma meya faru haka da zafi ne har ta saka kafa ta fita?Yrm yace gaskia laifina ne,na sani kedai kawai abar zancan sai in Allah yasa anganta.wasa-wasa har kwana uku,su Yarima sun koma gida,Magaji shine ya sanarda Umma komai, amma ya boye kama shi da wata da Bily tayi, ya dai ce Yarima ne ke cire mata ciki shine ta gaji ta gudu gashi kuma su anty Salma suna ganin laifinta. Hankalin Umma ya tashi ta shiga cewa dama nayi tunanin yarinyar nan bazata aikata wannan aikin ba.
[8:43AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 91ðŸµ
[8:43AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 91ðŸµ