← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 60

Sashe 14

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yammatan gidan su hudu ne kannan farooq, sumayya ce kurum suke ciki daya dashi,sauran duk uban su daya amma kansu hade yake.Suna girmama mansura sun shiga dakin su suna labarin kyan Bilkisu.Da dare suna zaune dakin hajiyar farooq wadda take matukar jin nauyin mansura,da Bilkisu kadai take hira itama jefi jefi tace,yar nan na zata kin yi aure?Bilkisu tayi murmushi tace Allah bai kawo lokacin ba,ta dube ta cike da kulawa,to Allah ya kawo na alkairi kada ki yi ruwan ido ko ki ce sai wane kin ji ko?Bilkisu tace to hajiya,ni dai ma ban samu bane in na samu mai so yaushe ma zan tsaya cewa sai wane? Haka kawai ta ji hajiyan farooq ta kwanta mata a rai har ma tana sha'awar ta gaya mata matsalarta,hajiya ta gyara zama,me ke faruwa ne da ke 'yar nan? Bilkisu tace wlh ban sani ba hajiya,ni dai tunda na taso da sunan wasa ban taba àsamun wanda yace ina sonki Bilkisu ba. Al'ajabi ne ya cika hajiya tare da tausayinta,tace ke ko da za ku jima ne ai da kun je bauchi in kai ki gurin mahaifinmu,shi malami ne waliyin Allah,
In'sha Allah matsalarki tazo karshe, mansura dake gefe tana jin su,da farko har ta ji haushin Bily menene na tona ma kanta asiri? Amma jin haka sai tace hajiya zamu je don batun aiki kiyi waya ki ce baki jin dadi, nima farooq yasha gaya min ko zamu je gurin kakansu a bauchi, in na gaya mata sai tace mu bar komai hannun Allah hajiya tace to sai ya kai ku in'sha Allah za'a warware matsalar kada ki damu,godiya suka yi sannan suka ci gaba da dan tattaunawa, ran jajibari suka zo gombe washe gari ranar idi suka dauki hanyar bauchi, gidan Modibbo Al'amin Dattijo mai ran karfe nan suka sauka, gida ne na alfarma ginin zamani da 'ya'yanshi suka tsara mishi,farkon gidan,shi ne a sasan farko mai dauke da tafkeken falo da dakunan bacci guda biyu,daga ciki dan autan shi ne jafar tare da iyalinshi tsohon yana da yara kusan guda 16, shidanne maza yayin da goman suke mata, ya'yanshi duk suna da rufin asiri matan kuma duk suna auran masu rufin asiri. Farooq ne yayi musu jagora zuwa falon Modibbo yana zaune kan wata lallausar darduma kan kafet, tsohon mai yawan shekaru ba yada rudu sam tuni matanshi sun jima da rasuwa,farooq ya zauna kusa dashi yana cewa,barka da war haka Akaramakallahu,ka ko shaida mu?Su mansura duk suka zauna gefe,ya dago ido ya kalle shi sannan ya kalle su?Yayi dan murmushi,Ummmarul faruku duk da baka zuwa gaishe ni ai ba zan manta ka ba,wadannan dai su ne ban san su ba, kila iyalinka ne,cikin yar dariya suka gaishe shi, farooq yakara shige mishi sannan yace ka min uzuri saboda nisan garin da nake aiki, amma ai ina yo maka aike ko?Aiken ka baya damuna nafi son kazo ka gaishe ni fiye da sakon ka,yace to zan kula,ni kaina ina son zuwa ka dinga sa min albarka,yanuna mansura ga mai dakin na nan,ya tashi yadauko dady,yana bacci ma yadora mishi akan cinya,ga kuma danka nan tsohon ya rungume shi masha Allah,yayi girma to ka kai su ciki gurin kawun naka,ya mike ko mu shiga ciki mace mai kirki da son mutane ta sauke su cikin farin ciki
da la'asar Farooq yana son ganawa da tsohon amma mutane sun mishi yawa,da yawa 'yan gaisuwar sallah ne, manyan attajirai ne tare da malamai,farooq ya shiga cikin gidan yace ku shirya muje mu gaida umman gidan mai martaba,hajiya fati tace gaskiya ne suma dai nasan gidan yau yan gaisuwar sallah sun yi yawa, amma gara yau akan gobe,tunda gobe hawa gaban bilkisu ya fadi tace a ranta dama farooq suna da dangantaka da gidan sarki?gidan su yarima kenan,sun shirya bilkisu cikin jallabiyya baka ta zagaya dan gyale tamkar yanda larabwa suke yi,takalmin ma baki ne.Hajiya fati ta yi ta yabon kyan bilkisu da tsarinta, mansura cikin shadda galila suka sha anko ita da farooq suka nufi kofar fada. Tsararran gida ne ginin zamani duk da girman gidan harabar cike da motoci na alfarma suka yi parking sannan suka fito me yasa gaban bilkisu yake faduwa? Sun shiga kofafi faluka kashi-kashi, kafin su ka shiga wani tafkeken falo, yana shimfide da carpet kirar china me shegen laushi,
[8:46AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 24🏵

Ga kujeru na alfarma kusan gefe uku kowacce da kalarta kuma ta dace da gefen da aka jera su, wata Dattijuwa ta nufo su da fara'a tana cewa Aa umar farooq kune a gidan ina gajiya?yace babu gajiya hajjo umma tana ciki kuwa?Tana nan bari ayi muku iso,ta fito tace gata nan zuwa, sai nan ta shiga gyara mata inda zata zauna,ma'ana ta shiga kakakabe kujerar duk da ba ko kura akanta,kyakkyawar mace ta fito sanye cikin wani leshi na alfarma, gwala-gwalai ne suke kyalli a yatsunta a hannun da na kafa, zuwa wuyanta. Tunda ta fito take kallon bilkisu a zuciyarta kuwa fadi take masha Allah, ta zauna kan kujerar ta dubi farooq da suka zube kan carpet tace idonka kenan ko farooq?Yayi murmushi yace ayimin afuwa umma, ta dubi su mansura tabe to wace ce matar taka cikinsu ko dukansu ne?Yana 'yar dariya ya nuna mansura sannan ya mika mata dady,kiyi hakuri umma ko gombe ma ina dadewa ban zo ba,saboda yanayin aiki wannan karon ma dan hutu ne muka samu,shi ne muka zo gaishe ku, tace to mungode Allah yayi albarka,
.ta nuna Bikisu wadda kanta ke sunkuye tace wannan fa?Bata san me yasa yarinyar ta tsaya mata a zuciya ba,farooq ne yayi magana,kawar mansura ce itama ta biyo mune tayi gaisuwa,umma tace mungode kwarai amma tana da aure ne?Yace tukunna dai tace to Allah yabaki miji na gari,shi da mansu suka ce amin, tace umman taka fa? Tana gaishe ki su sumayya ma ina ga yau za su zo,yaya gurin su anty salma su Aisha?Ta ce duk suna lfy sai gobe zasu zo gaida mai martaba,yace sai dai a gaishe su dan gobe zamu juya Modibbo ma mutane sun mishi yawa bai san ma munzo nan ba,tace yau kam Modibbo ai har dare amsar gaisuwa zai dinga yi.yanzun nan ma nake ma takwaranshi magana yazo yaje ya gaida shi tunda kwana uku zuwa hudu zai yi ya tafi farooq yace Al'amin yazo ne? Tace jiya me martaba yace mishi yazo gida yayi salla farooq yace ya fito ne?Yaushe rabon da mu hadu anfi shekara7,Umma tace kai dashi duk ba masu son zumunci bane bari in kira muku shi ku gaisa,
Dai dai nan wasu 'yanmata su biyu suka soma jere kayan ciye-ciye da shaye-shaye a gaban su mansura da farooq. Bilkisu gabanta ya tsananta faduwa kanta kuma yana kasa wasa take da zoben dake karamin yatsanta, umma ta kira layin Yarima tace babana ga yayanka ummar faruk kazo ku gaisa yace to su dan jira shi zai yi wanka, tace babana kayi sauri na sanka fa,yace to su ka ci gaba da hira tare da 'yan ciye-ciye, bilkisu kam kasa cin komai tayi kuma sai ta samu kanta da matsanancin jin nauyin umma,kula da hakan da umman tayi na kin ki cin komai da bilkisun tayi ne yasa tace ke kin ki cin komai saboda me?Ta dubi umman cikin jin kunya tare da dan murmushi,ta ce na koshi ne.Umma tace ka'idar gidan nan in ka shigo sai kaci abincin gidan,tasa hannu ta dauki yankakken apple ta saka abaki,tana taunawa a hankali idanun umma na kanta yarinyar sha'awa take bata,ta dubi mansura, yaya sunan kawar taki ne?Mansura tace sunanta bilkisu a ranta tace ta ci sunanta,Bilkisu maigadon zinari..

Kamshin data ji ne yasa gabanta ya tsananta faduwa menene take jine kodai mafarkin tane na yau da kullum?Muryar nan ta Yarima ta jiyo mai cike da kasaita da son girma, ya dubi farooq cike da sakin fuska yace,yayana sannu da zuwa,ashe da rabon zamu gaisa ne, farooq ya mike tare da mika mishi hannu,suka yi musabaha yana tambayar farooq iyali ya nuna mansura yace gata nan,ya dubi dady dake wasa kusa da umma, yaronka ne wannan? Yace eh Yarima ya tsugunna kusa da daddy yace Hello handsome, mansura tace ina yini, ya zuba manyan idanunshi kan fuskarta, yace lafiya yaya boy da yayana tace lfy,Bilkisu kam ta kasa dago ido ta kalli Yarima ganinta irin mafarkin da ta saba yi ne,mansu ta tabata tare da yi mata alama da ido wai su gaisa da Yarima, ta dago ta dube shi dai dai sanda ya zubo nashi idon kanta miyan bakinta ya kafe,ta kasa motsa lebanta ma bare ta iya furta wani abu,shi dai ya kauda kanshi amma zuciyarshi cike da mamaki,kyawunta tafi kama da larabawan gabas ta tsakiya,
Fiye da yan nigeria ta kuma kallonshi tana son ta tabbatar da cewa ba mafarki take yi ba,don haka tace Yarima! Ya kalle ta da sauri tayi dan murmushi har yanzun baka huce ba kenan?Cikin mamaki ya dube ta,a ina ki ka sanni ni?Ta dubi mansura sai kuma tayi shiru. Farooq yace cikin mamaki,kin san shi ne Bily?Tace tunda bai gane ni ba bar shi kawai,shiru Yariman yayi yana son tuna inda ya santa,umma cikin dan murmushi tace babana baka santa ba? Ya mike tare da fadin ban taba ganinta bafa, cike da rainin wayo ya fada,har ma su mansura da umma basu ji dadin yanda yayi ba,musamman mansura da tasan cewa Bilkisu ba ta da son magana da maza to ko shi ne Yariman mafarkinta?Shi ko ciki ya koma bilkisu ta bishi da kallo,Yariman mafarkinta ne tabbas, meyasa bai gane taba? Shin ko shi ba ya mafarkinta ne?Abokin wasanta tun suna yara? Suyi fada suyi wasa.
[8:46AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 25🏵
Chapter 14 · 0% Book details