Sashe 59
Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya tashi ya fita Yrm ko sai gashi y zube gwiwa biyu gaban mace,macen ma ‘yar Nigeria ‘yar Arewa wadanda ada yake kira kauyawa.yana cewa ta yafe masa ki yarda dani wallahi ina sonki da sauri ta dubesa gami da bude idanuwanta sosai,ina tsananin sonki beauty ban farga da tsananin sonki daya kamani ba sai da baki tare dani,na azabtu na wahalu,kalli yanda sonki ya maidani.hawaye ya soma gangaro mata tace yaya ka gane cewa kana sona?Ban yarda ba zaka yaudareni ne zaka cuceni ne,ya matso ya rungumeta duk da ta game jikinta guri guda, yana cewa I love you my beauty,I love u so much,I miss u a lot.turesa tayi tare da cewa ni bana sonka don Allah kabarni a takaice duk yanda suka zaci shawo kan Bily cikin sauki sai abin ya faskara, har Umman Mansu ta shigo ciki amma Bily ta kekashe nan ta tasa ta suka nufi zaria tace da Yarima yaje yayi hakuri zasu kawo ta ya dubi Umma yace don Allah kada ku mata fada laifina ne.bari in sanar dake laifukan dana mata.Bily ta dubesa da sauri an tambayeka ne?Yace a‘a zan dai fada musu ne don kada suyi miki fada suga laifinki bada hakkinki ba,tace suma kasheni ina ruwanka ba‘ace dai kafada ba,harma abin yaba Umma dariya tace to kai tunda bata son aji laifin naka ba sai ka barsa ba?Ku koma zamu maida ta insha Allah. A zaria idanu Bily ta zare tana kallon yanda aka fitar da titi cikin layinsu ga kwalbati layin yayi kyau bata gama tsinkewa ba sai data ga gidansu taga gefen mahaifyarta nan tayi sororo,Umma tace duk aikin Yrm ne,kuma yace shi don Allah yayi bawai saboda yana aurenki ba,ni kaina mota ya sai min wai in dinga zuwa aiki,baki kurum Bily ta taba ita abin bai burgeta ba.washegari sai gasu anty Saliha dasu Salma mai martaba yace suje su bada hakuri harda son suka zo yayi lakur jikin mamansa suka ce ta yafesu,tace insha Allah ya wuce.amma ita sai jibi zata dawo,Yrm yana samun labari sai yahau gyaran gidan aka sake fenti ya kwashe komai ya zuba sababbi don da tuni ya kammala nasu to hankalinsa ba kwance ba. Kafin ta dawo sai da Mansu tazo sukaje aka yimata gyaran gashi da lalle sai kace sabuwar amarya,ga kuma ainahin gyaran duk anyi suka nufi Bauchi.hutawa kawai Umma da Goggon sasa suka yi mata nasiha suka tafi.tana kwance kan sabon gadonta tana kallon kudin da Yarima ya kashe acikin dakin kawai sai kace baza‘a mutu ba,son yana bacci a gefenta,Yrm ya shigo cikin kayan bacci,zo muje mu kwanta beauty ko nan zamu kwana?Tayi masa shiru,ya matsa jikin gadon daidai fuskarta ya tsugunna cikin kunnenta yace baki huce bane?Tace,subhanallah don girman Allah ka barni nace ya mike na barki sai da safe.komawa Bily tayi tamkar bakuwa agidan, kowa na gidan tana dari-dari dashi har Umma sai datayi mata magana tace wai shin ‘yar nan kin kasa sakewa kodai baki yafe bane? Tace,a‘a Umma aini dama ban riki kowa cikin zuciyata ba,ko Yrm da yayi sanadin komai tun kafin ya ganni ma na yafe masa,Umma tace Allah sarki,ai haka ake son bawa na kwarai,me saurin yafiya.Ubangiji yana yafe ma mai yafe laifin dan uwansa,Allah ka yafe mana zunubanmu wanda muka sani da kuma wanda bamu sani ba.Bily sai da ta dan kara gyara Yrm na sati daya sannan ta dauri aniyar karbarsa ranar juma‘a ta shiga cikin kitchen ta tsara girki sai ranar ta shiga gefensa tunda ta dawo,yanda ya tsara gurin ya burgeta sosai ta jere masa abinci,sannan taje tayo gayunta cikin riga da wando na yan ubansun gurin Umma ta tura son ita kanta data dubi madubi tasan tayi ne.Yrm suka shigo da Dr. Salihu duk da yana dar-dar din kada ta bada shi ga mamakin Yarima sai ya ganta cikin gayun da yaji dama bai shigo da Dr. Salihu ba,domin zai kalle masa ado.tace abinci yana samansa,ai fa Yrm sai doki nan suka hau ta zuba musu,Dr. Salihu yace yana son abincin gargajiya ita matarsa tafi son na nasara,zai kawota su saba ta koya don ta rika masa,Bily tace sai sunzo.Yrm ya rakasa ya dawo. Ya zauna yana dubanta gaskia kinyi kyau,ta dubesa da fara‘a ko?Yace sosai ma,har fa sai naji haushin shigowa da Salihu,tayi ‘yar dariya ka kara abincin naga kamar baka koshi ba,yace ai kallonki ya kosar dani beauty,dan dawo kusa dani in dan ji kamshinki,da dan dumin jikinki.ba musu ta dawo,wayyo yau Yarima jinsa yake tamkar yau ne ya cire beauty dinsa daga leda,surkulle dai kala- kala ta jisa har sai daya bata tausayi kalaman so kuwa har sai da tayi hawaye don dadi ashe za‘a gaya mata wannan kalmar a rayuwarta? Fahimtar da Yarima yayi beauty tana son a so ta sai ya shiga nuna mata so a baki a aikace,fili a boye a waya,nan fa ya tsumata itama ta shiga fiddo masa da nata son filla-filla.tuni Yarima ya sallami Tina duk da sai da yayi mata jan ido ta tafi.zama suke na tsantsan so babu algus a cikinsa suna kaf-kaf da juna,in yana gida suna like da juna in ko yana office suna nane da waya,wai wayaga sabon shiga?Abin zallar sha‘awa ko aiki yake cikin laptop zaki samesa ya tada kai ne da cinyarta ita kuma tayi wasa da sumar kansa,wanka tare cin abinci tare,in yana gida zatayi musu abinci shima sai ya shige kitchen din.tafia suke cikin mota zasuje ganin sabon gidansu shida ita suna gaba abayan kuma son ne da Bilkisu ‘yar gidan Magaji,ta kwanto kanta akan kafadarsa yayi dan murmushi tare da sa hannunsa ya shafi cikinta.yarona yana damunki ko?Tace yaya zanyi cikin shagwaba,yayi fakin gefen titi bari na gani sauran kwana nawa yazo ne ma?Cike da shagwaba tace,in Dr. acikin mota?ya kwantar da kujerar sannan ya kwantar da ita ya daga rigar yana aunawa,son yana dariya yace lah!Dady kana duba bebyn ne?Yace eh yayi kusa yazo son yace dady kullum sai kace ya kusa yazo ni nafi so in gansa.Bily tace don Allah nidai daga min kujera in tashi kun cika zumudi kaida yaronka,nina fiku kosawa in haihu in huta. Makeken gidane tsarin ginin abin sha‘awa,an gama komai anata fenti.Bily tace nawan wannan gida sai kace mai mata hudu?Gaskia yayi mana girma,yace to shikenan zan sake aure,sai mu zau.....ta banko masa harara yace,ai subutar baki ne,tace yanda kayi subutar baki kace kai nawa ne ni kadai haka zaka hakura,ya kalli inda yaransu suna ta guje-guje cikin dakuna,ya jawota jikinsa ya tsotsi lebenta na kasa,yace ke dayace matata nan duniyar baki da kishiya,ta kalli idanunsa cikin ido tace inna mutu fa?Ya rumtse idanu ya kara matseta jikinsa,insha Allah bazaki rigani mutuwa ba,domin inkin mutu beauty nizan lalace ne na sani zan koma useless rayuwata zata daina amfani ko yaushe ina addu‘a ki rayu ki rike min yarana ni kuma in mutuwar tazo ta daukeni,Bily tace baka min adalci ba nawa inka mutu nima binka zanyi,yace to yaran fa?Tace ga su Umma,yace su Umma sun tsufa,tace bazamu mutu bama yanzun duka-duka shekarunmu nawa ne?Yace beauty bata nan ake daukar jariri ma? Tace to ya isa muje gida.Yrm yanzun ne yake tashensa,shekarunsa talatin da hudu in bakin sani ba baki cewa yana da aure,duk inda ya shiga mata suna kallonsa,sai dai duk wata mace gani yake ta biyo bayan beauty.arziki yanata bunkasa yanzun ya gina asibitin(surgery)daban sunan Yrm ya zagaya ko‘ina cikin kasa,ko‘ina kaji ana kwararren likitan mata Dr. Yrm,jaridu,gidan talabishan,da kuma radio,sunsha hira dashi maza da mata Yrm birgesu yakeyi,ga kyau ga kudi ga kuma aji.Bily ta fara nakuda misalin karfe daya na rana lokacin Yrm yana asibiti amma bini-bini zakiga ya bugo waya,dama yana sa ran haihuwar tata gobe ne,ko kuma cikin dare ita kuma taki sanar dashi cewa tana nakuda,yana cikin duba marasa lafia sai kuma ya sake kiranta,matar dake zaune gabansa ya dubata yace yi hakuri madam,ya daga wayar da kyar yace beauty are you ok?Muryarta na rawa tace eh,yace ke ban yarda ba,meke damunki?Sai kawai yaji tace Innalillahi wa‘inna ilaihir raji‘un da sauri ya mike ya dubi matar don Allah ki jirani ya fita da matsiyacin gudu ya figi mota
[8:44AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 93ðŸµ
[8:44AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 93ðŸµ