← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 60

Sashe 32

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Taja tsaki ai dama ita ba wai tana son sai ta burgesa bane kawai tana son ceto shine daga halakar daya shiga,amma akasan zuciyarta sai tana jin kamar ta canza shiga, amma sai wata zuciyar ta kwabe ta da cewa kinma damu sai kin burgesa kenan,don haka sai ta fasa ta fita zuwa kitchen dai dai lokacin ne taji bakon yana cewa,gaske kanwarka ce?Yarima yace,um hum! Bakon yace don Allah ina sonta she is very beautiful.Yarima ya mika masa littafin hannunsa tare da cewa amsa Saddik,kula min da littafina kasan ba‘a samunsa anan nima sai a England aka samo min duk da cewa muna dasu a library amma ba‘a son a fito dashi.Saddik yace, kada ka damu,yanzu muyi maganar sister dinka,I love her.Ga mamakin Bily, sai taji yace jeka gaya mata mana ni kazo ka dame ni kana sonta. Bily Sai data kusan faduwa don mamaki,shi wanan wato ko kishinta ma bayayi? Koda baya sonta ai ya dace yayi kishinta amatsayinsa na mijinta. Shin me hakan yake nufi? Guri ta samu acikin kitchen din ta zauna ta zabga tagumi,mijinta ne ke turo mata wani daya ce yana sonta,shin ko dai gaske ne Yarima bai san addini ba?Haka ta mike ta nufi daki bata ko ganin hanya sosai,dolenta ne tayi duk yanda zata ceto Yarima,amma duk da haka wata zuciyar tana ce mata Yarima ya wuce da tunaninta,amma sai tana karfafa ma kanta gwiwa da cewa,ai mata yake so kuma su yake nema,haka nan itama mace ce duk abinda wadancan matan suke dashi itama tana dashi,shin me zai hana itama ta bishi yanda sauran ke binsa?Ai itace ma ya dace ta bishi tunda mijinta ne,zata gwada irin nata salon,Allah yasa adace. Ta sani duk inda Yarima zaije baya wuce sha biyu.Wata rana ma baya kaiwa zaka ga ya shigo ko shi kadai ko shida ‘yanmatansa,ko sai in yazo sannan su biyo shi,yayi ta ja musu aji.Don haka kafin ya shigo tayi wanka ta gyara jikinta da turaruka,don turare yana motsa sha‘awa musamman irin masu sanyin kamshin nan,rigar bacci tasa kalar pink mai yala-yala,wato mai bin jiki tana da gidan nono kuma shi les ne mai shara-shara, ta gyara gashinta ta daure da ribon pink,ta kalli kanta a madubi tayi kyau ta zauna jiran Yarima Sha biyu saura ya shigo anci sa‘a shi kadai ne ya shigo,sai daya jima da shiga dakinsa sannan ta nufi dakin tana turawa kofar ta bude,ta shiga da sallama baya dakin amma da alamar yana wanka ne, ta kalli ko ina a dakin,lallai Yarima bashi da matsalar komai arayuwarsa,shiyasa yake yin yanda yaso.Zama tayi kan durowar gefen gadon tana cike da fargabar yanda zasu kwashe,kusan mintina goma sannan ya shigo dakin,waton ya fito daga bayin.Ya kalleta fuskarsa da alamar tambaya.Bily dai tana kallonsa bata ce kala ba,shima yaci gaba da harkokinsa.Shafa wannan matso wannan sa a hanci,sa a hammata, mamaki ma yake bata sai kace karuwan namiji,rigar bacci mai wando ya saka,sannan ya nufi wani dan fridge kwalbar jus ya ciro ya dauki kofi asaman fridge ya zauna gefen gado yana tsiyaya,ta gane nufinsa waton kala bazai ce mata ba,tasan zai iya abinda yafi haka ma,don haka sai tace,ina yini?Sai daya kurbi jus din sannan yace menene dalilin shigo min daki ba tare da izinina ba?Ta mike ta nufo shi yanda take tafiyar duk komai na jikinta girgiza yakeyi,kusa dashi ta duka,nazo ne in sauke nauyin da Allah ya dora min a matsayina na matarka.Ya dubi fuskarta idanunsa ya sauke akan lebunanta ‘yan yala-yala masu laushi jajaye tamkar ta saka janbaki,sannan ya kauda kai wane irin nauyi?Tayi jim don nauyin kalmar da zata fada.Hakkinka dake kaina.Ya sake kallon saitin kirjinta,sannan ya kauda kai yace, bana bukata,in kina nufin bani kanki ne,wancan lokacin ma nayi ne domin in banbance miki tsakanin yaro da babba,wato aikin da namiji zai iya da kuma wanda mace ba zata iya ba koda ‘yar shekara sittin ce shi kuma dan talatin duk da kince kashina baiyi kwari ba,nasan zaki shaida cewa ni ba raggo bane,don haka yanzun kama kanki bana bukatarki ko da zan ganki tsirara. Kash! Mu hadu a littafi na uku (3) don jin yadda zata kasance,shin yanayin hakurin ko ko,ita tana yin zuciya koko batayi.
[4:42AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵 MEKE FARUWA 57🏵
Chapter 32 · 0% Book details