← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 60

Sashe 39

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bily ta yarda da zancan Yarima,da yace shi da daya ne tamkar da dubu,domin yanda taga iyayan suka nuna karara son dan nasu suke,haka nan manyan mutane abokan nasa da wasu da suka samu zuwa daga cikin danginsu sai ina ka saka ake dashi.Umma ko sororo tayi lokacin da suka hada idanu da Bily, tasa rai ta ganta tana daga kafa da kyar sai gata tangaran to ko dai karami ne ko kuma yabi jiki?Duk wannan tunanin Umma ne amma tasha alwashin zata tambaye su taji kar dai suna shan kwayoyi ne?Yin wannan tunanin sai da gaban Umma ya fadi tace,inko haka ne sun cucemu.Bayan shan ruwa sunci sun sha ana zaune ana hira kafin lokacin zuwa masallaci,Umma ta dubi Yarima tace,ubana na zaci zanga matar taka da tsohon ciki?Yarima yace,haba dai Umma tun yanzu?Tace kaji shashanci da sai yaushe mu da kullum addu‘armu muga ‘yayanka,yace dazun ma mai martaba fa cemin yayi wai to kai Modibbo in zamu tafi da matarka zamu wuce inta haihu sai ta dawo,abin ya daure min kai nace ranka ya dade tana da ciki ne?Sai cemin yayi kuji zancan banza, ni zaka tambaya?Suka kwashe da dariya, Umma da Magaji.Yarima murmushi yayi don shi baya kyalkyala dariya.Bily kam sai tayi kasa da kai, Magaji ya mike tare da cewa zo muje masallaci. Yarima yace kwarai muda bamu zo da wuri ba.Suna fita Umma ta dubi Bily wai da gaske ne ‘yar nan baki da komai?Kunya ta rufe Bily,kanta na cikin cinyarta tace,wallahi Umma ba komai,tace ko dai kwaya kike sha ne?Tace Allah bana shan komai,tace ko shine dai ke baki,yace kada ki fada?Don fa karki yarda ki dinga shan kwaya nan gaba ta miki illa,kinga shi namiji ne da zarar yaso ‘yaya zai iya karo aure,ke kuma an cuceki. Bily tace,wallahi Umma bama shan komai,to kun taba ganin likita?Cewar Umma,a‘a inji Bily,bamu taba gani ba,tace to wannan ai shirme ne,kafin mubar garinnan sai munje kunga likita. Gurin kwanciya, Bily ta shige gurin Umma dama su Yarima suna can masallaci suma zuwa sha biyu suka nufi masallacin, haka sukayi ta ibada har ranar sallah.
Bily kam ranar data ganta gata ga Ka‘aba,ai addu‘a sai wadda ta manta. Murna kuwa harda hawaye, domin arayuwarta bata taba tunanin yau rana zata zo da zata ganta agaban Ka‘aba ba.A cikin addu‘o‘in da Bily tayi ta roki Allah game da aurenta da Yarima,kan cewa in mai shiryiwa ne Allah ya shirya shi sannan ya daidaita tsakaninsu in kuma babu daidaitawa,to Allah ya watsa abin ya kawo mata karshen wahalarta,sannan ta roki Allah ya sassauta ma mahaifiyarta,game da abokan zamanta ya kuma sa mahaifinta ya dawo kan hanya.Ranar sallah mai martaba ya nufo gida,Umma dai ta tsaya sai sunga likita.Daran ranar Yarima ya kasa hakuri da jarabarsa ta motsa,dakin Umma ya shigo Ummar tana toilet sai Bily dake zaune,tana neman layin Mamanmu sun gaisa da kowa amma ta kasa samun Mamanmu ya dubeta ransa ya sake biyawa,amma girman kai ya hanasa yayi mata magana.Har zuwa sanda Umma ta fito,tace yaya ne babana?Ya danyi murmushi sannan ya dubi inda Bily take zaune yace ba komai dama nazo ne nace miki sai da safe. Abinka da manya,nan Umma ta gano nufin dan nata,don haka tace,Bily tashi kije gurin mijinki mana, ni sai naga ma kamar gudunsa kike tunda muka zo banga kina bashi wata kulawa ba.Tana wannan maganar ne bayan fitar Yarima,taci gaba da cewa kin san fa su maza ‘yan lallashi ne,suna san kulawa bare irinsu Yarima.Bily tace Umma ba kirana yakeyi ba,Umma tace kaji sokuwa, yanzun yaushe ake jiran kiran miji?Har dai Yarima dan jin kai?To maza tashi ki bishi dama zaman da kukeyi kenan sai yace zo? Tashi-tashi maza-maza kar in sake jin haka.Bily ta mike ranta bace zata tafi,Umma tace,haka zaki je ba ko dan saka turare?Bily kam ta cika ne da mamaki,da bata zata haka Umma take ba,kuma sai tana ganin kamar ko san kai ne Umma take nunawa,don dai Yarima danta ne,duk da ta sani Umma tana sonta.Hoda ta murza sannan tasa turare ta saka kayan bacci sannan tasa hijabi ta fita,yana zaune bakin gado ya rasa me ke masa dadi,kamar ya zama kuda ya dauko Bily yake ji. Ta shigo da sallama fuskarta daure, tamkar an jefa shi cikin gidan aljanna haka yaji,harda yin wata ajiyar zuciya,amma don jan aji irin na Yarima sai ya wani daure fuska tare da cewa, lafiya ?Bata yi magana ba,ta zauna can gefe kan kafet,kin shigo min daki kina ta wani daure-dauren fuska bayan ban kira ki ba.Shiru dai ta masa,yace ok,in baki da magana tashi ki kama gabanki.Ga mamamkinsa sai yaga ta mike zata fita,yasha gabanta, ai bazaki fita ba har sai naji dalilin zuwanki. Bily ta dubesa, Umma tace inzo,oh shine dan kin raina Ummar zaki koma can ko?Tan ki koma din,ya koma gefen gadonsa ya zauna sannan ya dauko laptop dinsa ya soma kunnawa tana dai tsaye.Ta dawo ta zauna inda ta tashi yaci gaba da tura wani assigment ya jima yana turawa har ya gama,lokacin ta soma gyangyadi yace,ke ta farka idanunta fal bacci yace zo ki kwanta ba don halinki ba,tace nan ma ya isa, yace ke komai sai kin min gaddama,harda kice nan ya isa ance miki ina kalanki ne?Kema gulma ta kawo ki ko da Umma tace ki zo nasan kina son zuwan ko don a sosa miki abinda ke miki kaikayi, bani da yanda zanyi tunda an makala min ke.Mikewa kawai tayi taje ta kwanta, sai daya gama mata wulakanci kala-kala sannan ya shiga yin abinda ransa ke so da ita,jikinsa har bari yakeyi duk da dai yau ma kamar kullum,gim ta masa kamar kullum,haka ma da safe gari yayi haske amma ya fake da cewa kada ta kuma dawo masa yau bari ya sallameta gaba daya,bashi ya barta ba sai da Umma ta kwankwasa musu ita dai ta sani arashin ‘yanmatansa ne ya kula ta shiyasa bata jin itama zata sakar masa kanta yanda ta kula yafi bukata, ta aje aranta yanda ta rasa wanda zaice Bily ina sonki,haka ta hakura da jin wannan dadin don a duk lokacin da Yarima yake kusantar ta zuciyarta tana gaya mata cewa makiynki ne ke son hutawa da ni‘imarki,don haka sai taji duk mugayan maganganun da yake gaya mata suna dawo mata,kuma sai taji tana kyamarsa saboda matan da yake hulda dasu, sannan burinsa na taji dashi dadi ba zata ji dashi ba har abada,sai dai yanda suka saba.
[6:28AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 67🏵

Suna zaune gaban likita sun masa dukkan bayanin daya dace,sannan ya shiga dubasu.likitan ya tabbatar da cewa lafiayarsu lau,sannan ya basu wadansu kwayoyi wai su sha bayan sun dawo gida Umma tace,to su zo suje suyi tsaraba don ita gobe jirginsu zai tashi zuwa Nigeria su kuma sai gobe sannan zasu wuce Malesia tace wallahi Umma naso in biku gida nayi missing din Mamana.Umma tace,me zaki je Nigeria kiyi mijinki yana wata duniyar?Ke dai kiyi hakuri ba shekara mai zuwa bace zai gama ko ta sama ce? Kamar yau ne gurin Allah Mamanki ba kuna waya ba?Tace mu kanyi saboda yawanci sai sanda Mansu taje gidan sannan ta kira ni,Umma tace a‘a bata da waya ne?Tana da shi,inji Bily to ni yaushe rabona da wayata taga kati sai zuwanmu nan da Magaji yasa min,Umma ta kalli Yarima, me kenan babana?Yace to Umma yaya zan mata,ita fa tunda taje tafi karfin tace min tana son kaza,ko na ci ko a na sha bare kati, Umma tace to ke kuma ai wannan hauka ne, keda mijinki?Kusan shekara kin kasa sakin jiki dashi to dawa zaki saki jiki?Ki daina haka kinji ko, gaki kamar kanki a waye?Duk abinda kike so ki masa magana tace,to Umma yace kuma da kanta take abinci amma bazata ce tana son abu kaza ba,madam dora ce ma take gaya min cewa, tana cin taliya shine in sun zo shi cefane sai nace ya siyo mata,Umma tace ta daina haka Bily tace to insha Allahu bazata kara ba, azuciyarta sai mamaki takeyi shin Yarima da gaske ne da zata tambayesa abu zai mata?Tasan kila bazai ba don dai yaga mahaifiyarsa ne kurum.Sun shiga siyayya shagunan larabawa,nan taga mamaki Umma cewa tayi duk me take so ta diba na tsaraba nasu Mamanta ma ta dauka sai ta wuce dasu ta bada akai musu,amma ta kasa daukar komai sai Umma ce ke cewa, dau wannan dau wancan daga karshe ta daukar ma Asma‘u auta dankunne da sarka na gold ita da yarinyar Mansu,sannan ta yiwa Dady tasa haka suka yi ta shiga shaguna suna kashe kudi,Yarima dai ya jidi kananan kaya harda ‘yanmatansa yayi ma tsaraba,da Umma tace na Bily ne kai tsaye yace a‘a ya sayawa abokan karatunsa ne,kuma ga mamakin Bily Umma ba tace komai ba.
[6:30AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 68🏵
Chapter 39 · 0% Book details