← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 60

Sashe 26

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Amarya hijabi har kasa da nikabi tasa ta rufe fuskarta don tunda ta fito daga inda aka killaceta sai ta ringa ganin haske yana haske mata idanu,don ta jima bata ga rana ba.Motocin daukar amarya sun kai ishirin zuwa gidan sarkin zazzau,sauran dangi sun wuce Bauchi a mota amarya ko jirgi zasu biyo su Ladiyo dasu Karime suma sun taho don su danyi ‘yan binne-binne nan da bokayensu suka basu. Haka nan yanda Mansu ta tubure sai da Faruk yayi ma Bily kaya haka Bily itama ta tubure sai an raba musu nata.Lallabata akayi Mansu ta diba,don Umma cewa tayi baza‘a raba ba tunda tsadar kayan ma ba daya bane, tunda babu kasa da aura duk cikin kayan Mamanmu ma cewa tayi sai sun raba Mansu taki.Amarya ta isa gidan iyayan mijinta daf da magariba nan zasu fara zama agefensa tunda Malesia zasu wuce,gefen yasha gyara da kayan alatu,sannan ga dakin da aka basu suma su Mama sunyi kokari,sannan ga kuma gara shake da mota,duk fa hidimar nan malam Mamman ba ko taronsa,sai dai fa diyarsa ta auri dan sarkin Bauchi.Dinner daya da daya aka shirya a kayataccen Hotel kusan mutum shida ne akan amarya suna shiryata.Ni kaina muna hada ido nace subhanallahi,to ina ga ango.Yana zaune cikin shiga ta alfarma,wata alkyabba ce karshen tsada cikin motarsa limousine Ya kashingida yana kallon TV kuyangi da sauran dangi suka rakota har gurin motar suka bude mata ta shiga kamshin turarenta ne wanda tun tsawon zamanta agidan da aka killaceta tsohuwar take turareta dashi ya bugesa ga kuma na musamman domin shi Mansu tayi mata wanka dashi,ta shigo ta zauna tayi sallama,ba tare da ya kalleta ba ya amsa,sai dai yana kallonta da wutsiyar manyan idanunsa kyan da tayi tare da kamshin turarukan jikinta sun rikita sa kuma take sha‘awarta daya jima yanayi ta motsa masa,sai dai ya dake ya kuma shareta, amma zuciyarsa tana ta fadin she is beautiful.Ita ko Bily kasa kurum take kallo tare da yin wasa da yatsunta, xuciyarta kuwa tana kambama kyan halitta irinta Yarima. Guri yayi guri,dama ango da amarya ake jira shigowarsu cikin hall din zuka tana jama‘a sun tsumu ‘yayan Gwamnonin da ‘yayan sarakuna sun jinjina ma zaban Yarima.Kai wani dan sarki daya kasa daurewa sai daya iska Yarima har mazauninsa ya bashi hannu,bayan sun gaisa sannan yace Prince Al‘amin ka dauki ta karshe acikin mata,Yarima yayi dan yake tare da godiya. Mansu ta dafa Bily sannan ta rusuno bayanta tace aminiyata kunyi kyau da yawa kun dace sosai tsaki Bily tayi tare da cewa ni duk kunya ma ta isheni, don abin kunya ne in auri dan wannan yaron.Mansu tace yanzun dai ya zama miji sai adaina ce masa yaro,Bily ta dan dubesa ‘yan jarida suna ta hira dashi tace bazan daina kiransa yaro ba,tunda ba girmata yayi ba.Dinner tayi kyau,gurin ya tara duk wani mai ji da kansa,� yanmata da yawa sun kira Bily da mai tsananin sa‘a,domin cewarsu samun Yarima sai an tona.Bily takai kunnanta lokacin da wani dan jarida yake tana bayan Yarima wane irin farin ciki yake ciki yau kasancewar yayi aure da abar sonsa kuma mai tsananin kyau budar bakin Yarima sai cewa yayi shi wannan rana itace rana mafi muni cikin ranakun da yayi aduniya saboda me?Inji dan jarida cikin mamaki nan take Magaji ya katse dan jaridan da cewa tsabar murna ce tasasa baya iya saita maganarsa please ka tafi sannan na roke ka daka goge wannan bayanin da yayi.Bily bata ji komai ba don yace haka, dama tana tsammanin zance abinda yafi haka ma.Magaji da Faruk sunyi kokarin ganin Yarima baiyi wata tabargaza gaban jama'a ba gurin yanka cake nan ne suka danyi fama dashi yace bazai tashi zuwa ko ina ba don haka suka dauko cake din zuwa gabansa tare da baiwa jama‘a uzurin cewa kunsan Yarima namu dan gata ne sannan shaukin mulki yana dibansa don haka bazai iya zuwa gaban cake ba sai dai mu kawo masa,haka an sha fama kafin yayanka sannan yasa mata abaki itama bayan Mansu tasha fama gurin lallashinta dan haka hoton ba da cake din nasu duk ransu bace yake,sai dai haka ni bai hanasu yin kyauba,haka dangi sukayi ta rawa suna zuwa suna zuba ma ango da amarya kudi, kasancewa duk sunki rawa Bily kam abin bai birgeta ba,ta tuna ‘yan watannin baya kafin ta gamu da Yarima bata da wani buri daya wuce ta samu miji,burinta shine aure farin cikinta taga wanda zai ce wance ina sonki,amma hakan ya gagara,har zuwa wannan lokacin da take aure.Ta dubi Yarima cikin zuciyarta tace,gadai mijin kuma mijin nunawa tsara,ta kalli dinbin mutanen dake gurin wadanda ada sai dai ta gansu cikin TV ko jarida ta dubi kayan jikinta zuwa gwala-gwalan hannunta duk wadannan abubuwan sun kasa sakata cikin farin ciki saboda rasa wannan kalmar ta so.To wai ita MEKE FARUWA da ita ne maza basa sonta?Sai ko ga hawaye shar daidai sanda wani dan jarida yake cewa,wane irin farin ciki kike ciki yau ranar aurenki?Ta bude baki zata ce tana bakin ciki ne ita aranar yau sai muryarta ta hau rawa,nan da nan Mansu tace da ‘yan jaridan bazata iya cewa komai ba farin ciki yayi mata yawa gashi har kuka ma takeyi.Bily tanaji bata tanka ba,ita damuwarta tasha mata kai,haka akayi ta shagali dangi suna ta bada kyautukan zannuwa, agoguna,masu dauke da hotunansu,wani iya shege da Magaji yayi shine,duk maroki ko mawaki daya zo gabansu Yarima yayi roko sai Magaji yace, yarima ya baka kujerar makka,ko mota kamar sau hudu ana haka,Yarima yana jinsa da yaga Magaji watan bai san zuri ba,kuma kyautar gidan sarauta babu karya ta bada,don haka sai yace Magaji ya isheka haka, inko ba haka ba duk wanda ka sake yiwa kyauta kaine zaka basa,don ni ban dauki yau ranar farin ciki bare har nayi wata kyauta,dariya kawai Magaji yayi yasan dai ya kunna Yarima. Bayan tashi daga gurin dinner haka akayi jerin gwano zuwa gidan mai martaba inda su Bily suka shige gefensu,sai da tayi wanka sannan tazo tayi alwala ta samu su Sakina duk sun kwanta da sauran jama‘a.Bily ce kawai take sallah,nan itama tayi sallarta sannan suka soma hira gurin dinner.Bily dai korafi takeyi akan yanda Mansu ta ringa bada ita gurin ‘yan jarida ita ko Mansu zakewa tayi tana ta fadin yanda sukayi yau cewarta bata taba ganin mata da miji da suka dace kamar ita da Yarima ba.
[4:09AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 46 🏵
Chapter 26 · 0% Book details