← Book details Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 60

Sashe 54

Meke Faruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nan Yarima ya yiwa mahaifin bayanin cewa matsalar ta kayan aiki ne,cewa yayi shi zai bada kudin kayan aikin ko nawa ne. Yarima cikin satin yayi aike kayan suka iso, ya bukaci hoton yarinyar lokacin da take lafia,Allah cikin ikonsa sai gashi aiki ya kammalu zuwa wasu kwanaki ya bude aikin,an sha mamaki ganin fuskar yarinyar ta samu,shi kansa sam bai zaci aikin zaiyi kyau haka ba,sai dai kamanninta sun dan canza kadan,sai tafi da kyau ma,wannan aikin ya jawo daukakar sunan Yarima a fadin kasar nan inda asibitoci masu zaman kansu dana gwamnati suka yi ta gayyatar Yarima ire-iren wadannan aikin har ya kasance baya samun isasshen lokacin zama a gida,wani lokacin kuma cikin dare ne zaki ga anyo masa waya ana nemansa Emergency. Tiyata da makamantansu,abin yana cin ran Bily,domin aikinsa yanzu yasa bata samun kulawa sosai zata tsaya tayi gayun da kananan kaya ne da shaddodin ne zuwa lesuka,atamfofi amma wani lokacin ma har ta cire tasa kayan bacci bai dawo ba,yana dawowa kuma duk a gajiye da yayi wanka shikenan zai kwanta sai bacci.yau ma kusan kwana tara kenan haka na faruwa,domin wannan karon har asibitin Ibadan yaje yayi kwana biyu.yau tana sa ran sati ne da Lahadi dole yana gida,tunda yayi sallar asubahi ya koma ya kwanta,tara daidai ta tashi ta shi ta koma dakinsa ta zauna kusa da fuskarsa tace,abban son bazakayi wanka ba?Yayi mika barni inyi bacci beauty jiya nayi aiki sosai,mutum shidda na fede,tace shikenan mu kuma yanzu aiki yafi mu, ya tashi zaune yana kallonta,kamar yaya?Ta dubesa to yanzun fa bakada lokacinmu,yau kana aiki nan gobe kana aiki can.ya matso kusa da ita ya jawota jikinsa wannan aikin fa in kinyi tunani beauty dalilinsa ne na bata shekaru ina karatu,kuma an samu Allah ya taimakeni inda zaki lura aikin taimako ne,kin sani na fiki son hutu tunda kika ga sai mu kwanta mu tashi ban lalubeki ba kin san wani aikin yasha gaban wani Amma kiyi hakuri ko wane dan adam yanacin zamaninsa ne,yanzun lkcina ne akan aikina wata rana sai kiga an sami wanda ya doke ni,to ba kya ganin gara nayi amfani da damata da lokacina in samu aljannata, nasan dama ke ba makawa in dai miji ke daga kafa a shiga tawa dama a dage take shikenan sai ki jagoranci sauran matana na gidan aljanna,tayi driya to kwanta ka huta,yace a‘a na fasa yanzun ‘yar hira zamuyi irin wadda muka kwana biyu bamuyi ba, tace yau ai kana gida harda irin wadda bamu taba yi ba duk zamuyi. Yanzun dai kwnta kurum kayi baccinka,kuma matseta yayi sai sukaji kiran waya,ya kalleta fuskarta daure ya dauki wayar yana yi mata dariya,bataji kome aka ce masa ba ta daiji yace zanzo to nan da 10.ya fada tare da kallon agogo,ta mike zata fita yace zo nan gimbiya bana fushi bane maigadon zinari,marasa lafia na zan duba ance biyu daga cikin wadanda nayiwa fida basu farfado ba,amma ina ganin ba wata matsala bace,kafin goma zasu farka,tace um ai kai nasan in kaje sai kuma na ganka,yace shirya muje tare ta dubesa da gaske? Yace na taba cewa ki shirya muje?Tace a‘a ta fita ta zuwa dakinta cikin doguwar rigar shadda ta fito aslin soly ja,takalmi da jaka da gyale farare,hatta abin hannunta fari ne, shi ko farin yadi ne mai shara-shara wnda kana gani kaga yadin manya,salon daurin dankwalin Bily ya burgesa yace kai beauty dafa naso inyiwa kaina asara tayi fari tareda cewa ko?Yace ina son? Dashi zamu dakkosa in kina cigaba da min wannan farin tafiyar tamu zata iya fasuwa,tace yana hannun Asabe,yace amsosa mukadai zamu baki so muyi ‘yar hira irinta sirri?Tace to muje in amshesa sai muyi ma Umma sallama.Son yayi kyau cikin wandon jeans,pink da fara kar din shirt, takalminsa pink da ‘yar safa fara,shine ya dauki son din suka yiwa Umma sallama da cewa sunje asibiti,hakan yayi matukar birge Umma,suka nufi katuwar jeep dinsa tace tunda nazo gidannan yau ne rana ta farko da na shiga unguwar nan da rana kamar yanzun,ya dubeta yanzun ma shahada nayi don fa ni bana son ana kallemin ke,tace um wata rana inna kallemu sai inga tamkar masoya? Ya dubeta yaya ake gane mutum ya kamu da so?Tace kaine fa doctor nawa, zaka fini sani yayi murmushi ni ba likitan zuciya bane,kuma ban karanci so ba,kuma bai taba kamani ba,don haka ban san shi ba,tayi shiru yace kin taba so?Ko kuma sanin yanda yake?Tace ban taba so ba,sai dai ina sha‘awar aso ni,ina so in sanshi inyishi,da sauri ya dubeta kiyi ma wa? Tace kai mana nawan. Ta cigaba na taba karantawa wani littafi, marubuciyar cewa tayi shi so wani halitta ne wanda da zaran mutum yaga abinda yake so zai shige shi nan take,da zaran ka kamu da son wata baka da sauran nutsuwa,zaka kasance cikin tunanin abin sonka tare da kasancewa da abin son naka duk rintsi duk wuya,Yarima yayi dariya tare da cewa,malamar so kice kinsan so kenan?Tace a‘a naji dai labarinsa amma banyi saba ban kuma sansa ba.suna isowa asibitin shine ya dauki son suka jero duk da cewa Asabar ne asibitin yana cike da mutane,sai kallonsu akeyi ballantana nurse din da suke nan sai kallon Bily sukeyi,a cikin zukatansu suna cewa lallai dole ne Dr. Yrm ya dinga yiwa mata kallon baku yi ba,daf da zasu shiga office dinsa wata Dr. Jamila ta iso tana cewa a‘a Dr. kai da madam ne?Ta amshi son suka shiga office din ta bisu,tamkar ba asibiti ba office din domin ya tsaru(AC)ma kusan guda uku ne tace dama shi dan sanyi ne,gadon dake gefe ne irin wanda marasa lafia kan kwanta kawai zai nuna maka cewa nan office din likita ne.kujerar da aka tanada domin likitan itace ya nuna Bily tare da cewa beauty please sit down,ta zauna tana kallonsa tare da cewa,yau nima nazama doctor. Dr. Jamila ta dubi Bily yaya gajiya madam ya kike? Lafia,inji Bily fuskarta ba walwala tace Dr. Familyn ka masu kyau,yace na gode me kika zoyi asibiti yau Sunday?Tace ina da mara lafia,maman kawata ce ba lafia,yanzun sukayi min waya wai jikinta din ya tashi shine nazo in duba,Allah ya sauwake.
Yace zaki zauna anan ne in dawo?Ta mike muje nima na samu ladan gaishe da marasa lafia.yasa hannu ya dauki jakarta mu gani kina da kudin da zaki basu sadaka ko,tace duba ka gani ni na jima rabon da nasa jakar nan kila kuma asamu koba yawa,ya dago daga kallon cikin jakar da dan murmushi,yace Haj. Bily ai jakar taki tam take,ai na sani ke din babba ce,indai kudi ne,tace oh zagina zakayi,me nake saidawa?Yace au bakya sai da komai fa shine kike da kudi haka? Cikin tsokana yake mata maganar,ta warce jakarta nidai muje,Jamila itama dariya takeyi a xuciyarta tana mamkin dama ashe Dr. Yarima yana wasa haka?Ya mika hannu zai amshi son tace muje in rakaku. Bily ko yanda Jamila keta iyayi da salo shine yake bata haushi,kodai mijinta yana kula ta?Suna shiga dakin da marasa lafiar suke sai da ya fara shiga inda nurse din dake kula dasu suke zaune daga ganinsa duk suka tashi, Bily ma suka shigo suka gaida Bily tare da cewa madam din Dr. ce,Bily tayi murmushi suka amshi son suna cewa fine boy dayar tace Dr. dukansu sun farfado yace Alhamdulillah, bari mu duba su suka tafi dukansu,daga kansu Bily ta soma rabon kudin sannan tabi sauran marasa lafian,suna godia,nan taga da sauran kudin tasa sister guda daya ta rakata sauran dakuna don basu taimakon dubu daddayan,sannan taxo taba wadannan nurses din guda biyu ta samu ya gama rubuta ma mara lafian maganin daza a siyo,sannan suka fito har gurin mota sukayi musu rakiya harda Dr. Jamila ya amshi son yana cewa,to mun gode,sai Monday suka ce Allah ya kaimu,ta zauna agurin zamanta shi kuma ya shiga gurin tuki,ta kai hannu tare da cewa,zo nan son baba yayi driving ko?Ya rike baban gam, Yarima yace bazai zo ba,da kin iya da kin ja mu,tace to ka koya min yace sai kin gama fushin,tace fushin me?Yayi dan murmushi sannan yace haba beauty ni yanzun ko ido kika kifta nasan me hakan yake nufi bare fushinki,tace to wai fushin me zanyi ne? Yace kin fini sani kila ganin Jamila ne, tace umh wannan sarkin shisshigin nifa batayi min ba sai wani kaudi takeyi maka, yace to banda ke beauty kema mace bata miki ba bare ni?
[8:42AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 88🏵
Chapter 54 · 0% Book details