← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 21

Sashe 8

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hajiya Mariya kallan Maryama tayi ta ce"Shine babban d'anki ko?".Kai Marayama ta duk'ar tana murmushi irin kunyar d'an farin nan.Meenal ko azuciyarta hattace kai wannan bai kama da d'an kyauyan nan ba,amma jin alamun d'an matar ne ma,sai ta ce"Koda yake ko yadda yake kallan muta ne ma yasa ka shaida d'an kyauye ne".

Mahaifiyar d'an juma kuma fita tayi ta ce"Bari a'a za ruwan shayin".Bayan mahaifiyar d'an juma ta fitane ,Mommyn Meenal ta kalli Meenal ta ce"Meenal ina miki magana amma bakyaji ko,ke ala dole sai kinyi abinda za'asan baki da tarbiya ko,yanzu wannan da kika harara tsaranki ne?".Meenal turo baki tayi ta ce"Mommy bikiga yadda yake kallona ba,nifa na tsani kallo Wallahi".mommyn meenal dai na siha irin wadda ta sabayi ma meenal ce tayi mata.

Abin mamaki d'an juma sai fara jin shi wani iri ga wata irin fad'uwar gaba da kasalar zuciya ta samai , tunda yayi tozali da bak'uwar nan tasu.Abu kamar wasa koda yaje shagon manta abinda zai d'auka yayi sai da ya Kira Mahaifiyar shi awaya sannan ta tuna mai,ya aiki yaro ya kai.Shi kuma ya zauna yayi shiru,daga ya rufe ido sai yaga fuskar yarinyar yake gani,bai kawo komai aran shi ba sai cewa yayi tsabar kyan yarinyar ne yasa take min gizo a Ido.

Can cikin gidan kuma lokacin da Yaron ya kai kayan tea d'in lokacin ruwan zafin da Mahaifiyar d'an juma tasa har yayi zafi.D'iba tayi a kofi mai kyau ta kaima Meenal.Hajiya Mariya amsa tayi ta had'ama Meenal tea d'in ta bata.Meenal tana turo baki kamar yadda ta saba in ranta na ab'ace ta ce"Mommy na k'oshi".Hajiya Mariya babu yadda batayi da itaba tak'i.Hajiya Mariya d'aukar tea d'in tayi ta kaima mahaifiyar d'an juma da ke waje tana wanke kwanonin da ta b'ata.

Hajiya Mariya zama tayi gefan Maryama ,ta ce"Kin ga 'yar gidan na ki tak'i sha".Mahaifiyar d'an juma amsa tayi ta ce"Tom ko wani abun take so ta fad'a kafin yayansu ya tafi insa shi ya kawo mata"."Ki rabu da Meenal in taji yunwa da kanta zata naima bata da juriyar yunw..."Sallamar d'an juma ce tasa Mommyn meenal yin shiru.
D'an juma kallan Mahaifiyar shi yayi ya ce"Inna zan tafi ko akwai abinda kike buk'ata".Mahaifiyar d'an juma banza tayi da shi kamar bata ji abinda ya ce ba,ta ci gaba da wanke-wankenta.Shiru d'an juma yayi sannaya juya ya ce"Inna na tafi".yana fad'in haka ya tafi dan yasan ba amsa mai za tai ba.

Bayan d'an juma ya fita ne,Hajiya Mariya ta kalli Mahaifiyar d'an juma,ta ce"Auntyna idan laifi yayi ayi hak'uri dan Allah d'a zuma ina gani yana gaidaki baki amsa mai ba".Maihaifiyar d'an juma aje wanke-wanken da takeyi ta yi ,ta ce"Hajiya dole in fushi da shi ink'i amsa gaisuwar shi,na san ke kanki kallan mai mata kike mai,amma kin gan shi nan bashi da ranar auran ma,ke budurwar ma baida ita,an bashi yara da dama agarin nan yace baiso,tom ya yake so muyi,nan fa kyauye ne ba binni ba bare yace ,na tabbata ko a binni Namiji d'an shekara talatin da bakwai ya isa afara mai surutu bare kuma anan.Mahaifin shi yanzu haka fushi yake dani yace nina d'aure mai gindi,tom kwanannan k'anwar baban shi ta bashi 'ya itama yace bai so,tom taya bazanyi fushi da shi ba".Mahaifiyar d'an juma ta idasa maganar cikin alamun damuwa"

Hajiya Mariya kallan mahaifiyar d'an juma tayi ta ce"Eh gaskiya kam kallan mai mata nayi mai,duk da da darkoma banyi tunanin anan ya ke ba,amma abinda zaku duba aure lokaci ne,idan lokacin yazo zaiyi,duk kalar fushin da za ku yi da shi dole sai ranar da Allah ya nufa zaiyi auran zaiyi.Dan haka shawarar da zan baki nisiha zaki tayi mai ".Haka dai Mommyn meenal tai ta yima mahaifiyar d'an juma nasiha,da ankarar da ita komai lokaci ne"

D'an juma ko na fita gidan Sarki ya biya wato kakan shi kenan,zaune ya iske tsofaffin biyu sai hirar su suke.D'an juma zama yayi sannan ya gaida sarki da kuma kakan Meenal.Alhaji cikin fara'ar shi ya ce"Tun da na iso nakejin ana cewa d'an juma-d'an juma amma kuma d'an juma yayi wahalar gani".D'an juma dai murmushi yayi ,kuma dama shi mutum ne ba mai yawan magana ba .Sarki amshe zan can yayi da cewa"Ka gan shi nan girman banza ne babu mata,tom ko dai Kadunar zaka tafi da shi ka zab'ar mai matar aure acan inda yak'i na mahaifar shi".Dariya Alhaji yayi ya ce"Abdurrahaman zaka Kaduna ko in baka mata".Shi dai d'an juma murmushi kawai yayi.Sannan ya yi musu sallama ya tashi ya tafi,yana mai son sanin su waye su,dan shi dai bai tab'a jin ance suna da 'yan'uwa a Kaduna ba,amma kuma abisa ga dukkan alamu wannan sun saba da Sarki .

Sarki Kiran d'an juma yayi ya ce"Yauwa d'an juma zoka kaima Yarinyar nan addu'ar nan ta fara sha tun yau".Alhji wato kakan meenal ya ce"A'a indai Amina ce bazata shaba,yaje dai su taho tare in tsareta ta sha agabana" .

D'an juma fita yayi ya d'auki mashin d'in shi roba-roba ya nufi gidan su,yana zuwa ko ya iske Mahaifi yar shi ce kad'ai atsakar gidan .kusa da ita ya k'arasa ya ce"Inna Sarki ya aikoni inzo in tafi da yarinyar nan bak'in da akayi". Mahaifiyar d'an juma ba tare da ta amsa mai ba ta shiga d'akinta inda Meenal take da Mommynta, Meenal na kwance dan yunwa ta fara matsa mata.Mahaifiyar d'an juma kallan Mommyn Meenal tayi ta ce"Hajiya wai sarki ne ya aiko kiran Amina"."Tom shikenan d'an ai kyan na nan ai sai su tafi tare".Mommyn Meenal na fad'in haka ta fara bubbuga Meenal dake jin su ,ta ce"Meenalyn daddy ki tashi kije ana kiranki".Bud'ar bakin Meenal sai cewa tayi "Mommy ni bazani ba".Hajiya Mariya d'aure fuska tayi tana mai jin kunyar maganar da Meenal tayi,ta ce"Meenal ki tashi nace ko?".Meenal turo baki ta yi ta ce"Tom mommy ni mai zanyi dan Allah ni bazani ba" .Hajiya Mariya sosai taji kunya,haka yasa k'asa-k'asa yadda Mahaifiyar d'an juma bazataji ba ta ce"Wallahi kinji na rantse idan har biki tashi ba zan kira daddynki in ce mai ba yanzu zamu koma ba,idan kina ganin wasa ne kar ki tashi ki tafi" .
Meenal tashi tayi tana zun b'uro baki tayi hanyar waje,dan ita bama ganin Wanda zai kaita tayi ba .Hajiya Mariya gyalan Meenal d'in ta wurga mata ta ce"Ga gyalanki nan".Meenal amsa tayi ta fita ba tare da ta yafa ba ,bak'ar abaya ce jikinta taji adon stone tayi mata kyau sosai dama kuma ita Meenal tafi ra'ayin dogayan riguna.

Tsaye yake da key d'in mashin d'in shi a hannu ,yayi adon shi ciki wani yadi mai kyau Masha Allah,Wanda ya dai wuce araina,dan d'an juma mutum ne mai son gayu gashi kuma shi dama hurd'ar shi tafi yawa a funtua.
Sosai ya k'osa tafito ya k'ara kallan kyakkyawar fuskarta.Meenal tsaye tayi tana kallan shi bisa ga alama shine zai kaita.D'an juma ko dama tun kafin ta k'araso ya k'ureta da ido dan ko kyaftawa ba yayi,tana zuwa kusa da shi yayi saurin kauda idon shi,Meenal tsaki tayi dan ta tsani kallo,ja tai ta tsaya ,batare da ta tanka mishi ba,shima kuma sai ya kasa mata magana.Mahaifiyar d'an juma ce ta ce"Yayan su kuje mana gata nan ta fito" .Meenal tsaki tayi tai gaba yana binta abaya.Aiko suna fitowa 'yan gidan kowa idan shi akan Meenal .Meenal na zuwa taja ta tsaya kusa da mashin d'in.D'an juma ta gefan ido ya k'ara satar kallan Meenal d'in dan ya lura bata San kallo shi kuma baya son raini hakan yasa ya kalleta asace.
D'an juma ya hau mashin d'in ,yaji bata hauba taja ta tsaya,cikin ko in kula dan shima miskilin ne ya ce"Ki hau muje ".Meenal sai da ta kallai jin yadda yayi mata magana,agadarance,ita dariyama yaso ya bata ,azuciyarta ta ce"Dan kyauye ko da me zai gadara har da zai min magana ahaka,ta ce koda yake ance d'an kyauyan mutum akwai iyayi" .
Chapter 8 · 0% Book details