← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

📚 MEENALYN DADDY 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Na
Fadila Sani Bakori.

Page 23 & 24

Meenal cikin kuka ta ce"Bazan bud'e ba har sai alhaji ya ce ya fasa min wannan auran sannan,idan kuma ba haka ba Wallahi anan zanta zama babu ci babu sha har in mutu kowama ya huta inda abin hakane"
Daddyn meenal cikin rud'ewa ya ce"Alhaji kaji ko abinda tace,dan Allah kataimakamin afasa wannan auran."
Alhaji Abba ya idasa maganar yana rik'e da hannun mahaifinsa kamar zaiyi kuka.
Alhaji shiru yayi baice komai ba sai zuwa can ya ce"Sani ka yi hak'uri inajin kunyar sarki,bazan iya zuwa insanar da shi abinda kakeso ba,muyi ta addu'a Allah ya karkato da hankalinta kafin lokacin bikin."
Daddyn meenal cikin marairaicewa ya ce"Alhaji ni zanje zansanar da sarki da kaina"Bazai yuwu ba Sani,addu'ar dai ita zamuyi Allah ya juyomana da hankalin Amina kafin bikin"

Meenal da tayi tunanin abinda tace zaisa alhaji ya janye maganar fasa auran,amma sai taji kuma yana cewa wai suyi addu'a Allah ya juyo da hankalinta,meenal rugawa tayi da gudu ta d'akko wata k'aramar wuk'a tasa dai-dai wuyanta tana cewa"Daddy shikenan kashe kaina zanyi yanzu nan ,dan wallahi bazan zauna da ranar d'an kyauye akaina ba,gara in kashe kaina kowama ya huta kafin inga wannan bak'ar ranar"Meenal ta fad'i maganar tana d'ora wuk'ar awuyanta alamun zata yanka.
Daddyn meenal fasa kuka yayi jikinshi ko ina yana rawa yana cewa"Alhaji dan Allah kataimake ni dan Allah! dan Allah!!"
Alhaji ganin yadda jikin Alhaji Abba ke rawa abin sai ya bashi tsoro,hakan yasa bawai dan yaji tsoran abinda Meenal zatayi ba dan yasan k'arya take baban take godawa.Alhaji ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"Shikenan gobe zanje in yima sarki magana abashi wata yarinyar"Alhaji na fad'in haka ya juya ya tafi.

Daddyn meenal cikin k'osawa ya ce"Yauwa meenaln daddy kinji dai alhaji ya fad'a da bakinsa aje wuk'ar dan Allah ki bud'emin kinji".Meenal turo baki tayi sannan ta aje wuk'ar ta bud'e d'akin.Meenal na bud'e d'akin daddyn meenal ya shiga da sauri ya rungune Meenal yana mai sauke ajiyar zuciya yana mai bubbuga bayan meenal d'in.Sun dad'e ahaka sannan Alhaji Abba ya kamo hannunta ya ce" mu je kici abinci"

Alhaji Abba a caution d'in falonshi ya zaunar da Meenal ya shiga kitchen da kanshi ya d'ebo mata taliya ya kawo mata.
Kasan cewar Meenal yunwa takeji hakan yasa ta amsa taci,tana gama ci baccin wahalar kukan da tayi ya kwasheta,sanna Alhaji Abba shima ya tashi yaje ya gabatar da sallolonshi "

B'angaran alhaji ko,hajiya Mariya ganin yadda ya fito jikinshi asanyaye yasa cikin sanyi tabi bayan shi tana cewa"Alhaji lafiya kuwa?"
Alhaji kamar ba zai yi magana ba ,sai kuma ya tsaya yana kallan Mommyn meenal ya ce"Mariya ke ma baki son auran Amina ko?"
Shiru hajiya mariya tayi tana tunanin abinda zatacema alhaji,sannan ta ce"A'a alhaji bawai bana so bane,kawai ina tunanin yadda Meenal ta saba rayuwar nan kuma ace ta koma rayuwar kyauye,sannan kuma mahaifin Meenal yariga ya shagwab'a Meenal da yawa bazata iya bibiyayya wa mijinta ba,garama idan ta auri Wanda ta ke so k'ila tayi biyayya tabishi,amma wannan kamma ina hangyan zamanda za ai"
Shiru Alhaji yayi sannan ya ce"Eh tom Mariya maganarki hakane,amma yaran nan yace ba'a kyauyansu zai ajeta ba,magabar so kuma ke kina ganin da akwai Wanda Amina zata so,yarinyar da kullum kallan kanta take kamar wata jinjira"Shiru Alhaji yayi kamar mai tunani,sannan zuwa can ya ce"Mariya ki sanar da Sani maganar auran Amina na nan,dan bazan iya tunkarar sarki ba da maganar warware auran nan gaskiya,ita kuma Aminar ina tunanin aci gaba da b'oye mata har izuwa ranar bakin,ni kuma zanci gaba da addu'a kuma sai ku tayani Allah ya karkato mana da hankalinta akan al'amarin"
Mommyn meenal cikin sanyi ta ce "Tom insha Allah za'ayi."

Meenal na tashi bacci ruwa ta watsa ,sannan ta koma wani baccin inda dama hutun sallah take"

Da daddare alhaji Abba na zaune falonshi yana kallo Hajiya Mariya ta yi sallama ta shiga.Bayan hajiya Mariya ta zauna da d'an jimawa sannan ta kalli daddyn meenal ta ce"Daddyn Meenal alhaji ya bani sak'o in baka"
Alhaji Abba maida hankalinshi yayi ga Hajiya Mariya alamun inajinki.Hajiya Mariya cikin sanyi ta fara magana kamar haka"Daddyn Meenal sai dai muyi hak'uri kuma muyita addu'a Allah ya sa haka shi yafi alkairi,d'azu Alhaji yacemin maganar auran meenal da yaran nan tananan,amma wai mu b'oyema meenal har sai ranar bikin ta sani"
Shiru Alhaji Abba yayi dan yama rasa abinda zai ce,sai zuwa can ya ce"Amma baki tunanin halinda Meenal zata shiga tana mai sa ran anfasa auran nan gaba kuma sai dai taji an d'aura mata aure da yaran nan?" "Tom daddyn meenal maganar halinda Meenal zata shiga ni sai inga sai dai muyita addu'ar Allah ya tabbatar mana da abinda yafi alkairi amm...."Alhaji Abba cikin jin zafi ya katse mommyn meenal ya ce"Mariya wata kalar magana kikeyi haka,Allah ya tabbatar mana da alkairi kinsan dai yaran nan bazai tab'a zama alkairi ga meenal ba, dan haka idan zaki addu'a kice Allah yasa afasa kawai bawai Allah ya tabbatar da alkairi ba,alkairin me?,wana alkairi wannan yaran yake dashi?,nifa dama kallo d'aya na yi ma yaran naji bai min ba." "A'a daddyn meenal dan dai baima meenal bane,amma gaskiya Abdurrahman nada hankali da natsuwa,danni Wallahi lokacin da naga yaron banzaci a kyauyan yake ba ma,amma da meenal zata kwantar da hankalinta inda ba a kyauyan zai ajetaba sai inga da...."Tsawar da daddyn meenal yayi ma mommyn meenal ce tasa tayi shiru bata k'arasa fad'in abinda take fad'a ba.

Alhaji Abba cikin alamun jin zafn Hajiya Mariya ganin bata goyan bayan meenal ya ce "Mariya Wallahi na fara tunanin da had'in bakinki za ai ma Meenal auran nan,dan haka indai kinsan dasa hannunki akan maganar nan tun wuri kafin in ganoki ki cire hannunki,kuma yadda ki kai aka had'a kiyi yadda zaki a raba,Meenal nawa take da ake k'ok'arin sata cikin wannan tashin hankalin."Alhaji Abba kamar wani zararre yazo ya kama hannun mommyn meenal yana cewa"Mariya na rok'eki idan kina da sa hannu a maganar nan dan Allah ku janye,kuji tausaina nida meenal,meenal shekarunta sunyi kad'an da zata fara fuskantar tashin hankali irin wannan."
Hajiya Mariya shiru tayi tana kallan daddyn meenal dan tsakanin shi da Allah yake magana,hajiya Mariya cikin sanyi ta ce"Daddyn meenal Wallahi Allah d'aya bana farinciki da auran nan na Meenal,hasalima hankalina atashe yake, amma da alhaji yayi min bayani shine hankalina ya kwanta har ma ke ganin kamar koda had'in hannuna za ai hakan,karfa ka manta nina haifi meenal taya zan so abinda nasan meenal bazata so shi ba.Abinda na ke tunani shine inda har yace ba akyauyansu zai ajeta ba babu wani makusa alamarin inda....."Alhaji Abba hannu ya d'aga ma mommyn Meenal ya ce"Je ki kawai ."
Dan sosai ranshi ki b'aci idan tana yabon d'anjuma.

Hajiya Mariya fita ta yi batare da tak'ara magana ba.

Haka Rayuwa taci gaba da tafiya batare da meenal tasan ba awarware auranta ba,inda alhaji Abba ko kullin cikin fargaba yake da tsoran halinda meenal zata shiga aduk lokacin da taji za'a d'aura auranta da d'anjuma"

B'angaran d'anjuma ko shi da sarki suke shirye-shiryansu inda shima iyayanshi bason auran nashi suke ba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya dan yanzu haka saura wata d'aya auran,sosai d'anjuma ke cikin damuwa da fargaba, saboda tun lokacinda akai maganar saranar shi da meenal har yau daga mahaifiyarshi har mahaifinshi babu Wanda ya kuma mai maganar auran,sai dai shi da sarki kawai suke shawarwarinsu,yanzu haka d'anjuma yazo gaida sarki ne bayan sun gaisa har d'anjuma zai fita sarki ya kirashi ya ce "Abdurrahman yaufa saura kwana ashirin da bakwai bikinka ,ya maganar lefan ,ka gama had'awa inda kace saura kad'an?."
"Eh sarki nagama ."maganar wajan zama fa inda dai ka amsa ma alhaji zaka ajeta a Funtua."Cewar Sarki.
Shiru d'anjuma yayi sannan ya ce "Eh dama da akwai wani gida da nakeso in kama haya sai in ajeta nan,tom amma Baba nake tunanin ba zai yadda ba."
Sarki gyara zama ya yi ya ce " Kaje ka kama hayar zanma mahaifinka maganar anjima idan yazo duk da banso na kuma yi mai maganar ba har izuwa ranar d'aurin auran,saboda tunda akasa ranar nan bai kuma zuwa yayimin maganar ba,amma ni zanmai anjima idan yazo."
D'anjuma cikin jin dad'i ya ce"Yauwa idan kaine nasan bazai musaba."
Chapter 17 · 0% Book details