← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misakin k'arfe sha d'aya na safe alhaji wato kakan meenal suka shiga garin Kaduna,suna isa alhaji yacema Isuhu yayi gidan Sani da shi.Daddyn meenal na zaune meenal na mai hirar tak'osa ta ga ta fara aiki alhaji sukayi sallama suka shigo.Bayan alhaji ya zaunane daddyn meenal ya gaidashi yayi mai ya hanya.Alhaji cikin fad'ad'a fara'arshi ya ce"Ina Mariya ne,tafe nake da albishir mai kyau so nake sai agabanta zan fad'a?"Daddyn meenal da gabanshi ke dukan uku-uku kallan meenal yayi ya ce"Kira mommynki idan kinkirata ki je Falona ki zauna nan zamuyi magana ne".Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce"A'a ta dawo dan maganar tatace ai"Daddyn meenal shiru yayi meenal kuma ta shiga kitchen ta kira mahaifiyarta da ke aikin girki.
Hajiya mariya waje ta samu ta zauna sannan ta gaida alhaji.
Alhaji K'ara gyara zama yayi sannan ya ce"Alhamdulillah dama ance komai yayi farko zaiyi k'arshe,kuma matar mutum kabarinsa wani baya auran matar wani,sannan tunda yaran nan ya furta yana son yarinyar nan sai da nayi kwana bakwai ina addu'a indai ba alkairi acikin lamarin Allah ya kaudamin son abun,amma naji son abin k'ara k'aruwanmin yake,hakan yasa na tabbatar da akwai alkairi alamarin,shi yasa kukagananace,jiya da na koma munyi magana da Sarki dan antsaida komai ansa rana wata uku masu zuwa,dan yaron ma da yake akwai himma har yaba da biskit (biscuit)an taho da shi nasa ranar da akai"Alhaji har ya gama maganar shi babu Wanda ya tankamai daga daddyn meenal har hajiya mariya,itako meenal bama fahimtar abinda alhaji yace tayi ba,dan tuhda ya fara magana ta d'auki wayarta ta fara buga game.Alhaji ko jin babu Wanda ya tanka mai ,kallan daddyn meenal yayi Wanda kallo d'aya ya hango tsantsar damuwar da yashiga najin abinda yace,alhaji share daddyn meenal yayi ,dan ya hango damuwar da ya shiga najin abinda yace,alhaji yana sane yace"Sani ko bukuji abinda nace bane nayi magana kunajina kun shareni?"Daddyn meenal da gaba d'aya yarasa abinda ke mai dad'i da kyar ya bude baki ya ce"Alhaji munji abinda kace"Alhaji cikin jin dad'i ya ce"Yauwa isuhu dan Allah shigo da biskit d'in da suka bada nasa ranar".

Wanda aka kira da Isuhu tashi yayi yaje ya shigo da kwalayan biskitin da d'anjuma ya bada amatsayin kayan sa ranarshi da Meenal.
Bayan isuhu ya aje kwalayan biskit d'inne ,Alhaji ya kalli Meenal dake ta famar danna waya wadda hankalinta gaba d'aya ba akansu yake ba,da alamama batagane abinda ake magana akai ba,hakan yasa alhaji ya kalli meenal ya ce"Amina bani hankalinkinan,wannan kwalayan biskit d'in da kike gani nasa ranarki da Abdurrahman ne,yaron nan d'anjum......".Yadda meenal ta mik'e azaburene har wayar hannunta na fad'uwa yasa alhaji yayi shiru.Meenal cikin zazzare ido na alamun furgicin abinda alhaji yace ta ce"Alhaji banganeba,kana nufin ni wai akasama rana da d'an kyauyan nan kome?"Alhaji da k'uwa yayima meenal yace"Amina k'aniyarki nace,dan garinku ni zaki rik'a zaroma ido kina tambayata,tom ki k'ara bud'e kunnanki da kyau inma jine biki ba,d'anjuma dai yaro mai hankaki na garinda kikaje shi aka samiki ranar aure da shi wata uku masu zuwa.....".Meenal wurgi tayi da wayarta tana mai fasa kuka iya k'arfinta tana mai kallan daddynta tana cewa"Daddy wai kaji abinda alhaji yakecewa ko daddy?".Meenal ta idasa maganar tana mai k'ara tsandarewa da kuka.

Alhaji Abba tashi yayi yazo ya kama Meenal cikin damuwa ya zaunar da ita kusa da shi yana mai cewa"Ki yi shiru Meenalyn daddy alhaji wasa yake mik....."Kaine dai kake mata wasa ,ga biskit nan dan haka duk ku rabama mutanan arziki,idanma bazaku rababa Mariya gashi nan ke duk kiba mutanan da kuke tare da su,ki shaida musu wata uku masu zuwa insha Allah biki"Alhaji na kaiwa nan ya tashi yayi ficewar shi,ya iske isuhu acikin mota yaja suka tafi.

Meenal ko kukanta taci gaba dayi tana mai cewa"Wallahi daddy tunda wuri kajema ka tsaida maganar nan dan Wallahi kajima na rantse bazan auri d'an kyauye ba".Aifa nan hankakin alhaji Abba ya kuma tashi sosai,dan yama rasa abinda zai cema meenal ya samu tayi shiru ta saurareshi,kallan hajiya Mariya yayi dake zaune tayi tagwumi tana kallansu ya ce"Haba Mommyn meenal kizo ki tayani ba yarinyarnan hak'uri mana kinyi shiru kina ganin ahalinda take"Tom daddyn meenal mai zance?,aikin gama yariga ya gama meenal sai dai tayi hak'uri".
Meenal tashi tayi da gudu ta tura bedroom d'inta ta shige tana mai k'ara tsananta kukanta.Alhaji Abba ma tashi yayi ya bita da gudu amma kafin yaje ta sama d'akin key dole ya tsaya yana buga k'ofar yana mai rok'on Meenal da cewa"Dan Allah meenalyn daddy ki bud'e ki saurareni kiji abinda zance miki,Wallahi meenal hankalina yafi naki tashi bana son auran nan,kuma insha Allah baza ayishi ba,dan Allahi ki bud'e k'ofar"Babu yadda alhaji Abba baiyi da meenal ta bud'e k'ofar ba amma tayi banza dashi taci gaba da kukanta.Alhaji Abba jingina yayi da k'ofar yayi ta gwumi dan sosai kukan meenal d'in ke k'ara d'aga mai hankali.
Hajiya mariya da ita kanta cikin damuwa take najin abinda alhaji yace, fitowarta kitchen kenan jin abincinta na kyauri tazo ta iske daddyn meenal ya rafka uban tagwumi yana jingine da k'ofar d'akin meenal.Yajiya Mariya k'arasawa tayi ta zuk'unna kusa da daddyn meenal ta ce"Daddyn meenal kayi hak'uri dole muyi hak'uri mujure ire-iran halinda zamuga Meenal ciki,idan ko ba hakaba tom sai dai mu bujirema maganar alhaji,wadda hakan kuma ba abu bane mai yuwuwa,yanzu ga abinci nan na sauke dan Allah kazo muje kaci..." .Wata irin tsawa alhaji Abba yayima hajiya Mariya ya ce" Wata irin banzar magana kike fad'amin ko sokike mutaru makashe meenal ne ko me?,Yarinya tana cikin wannan halin zaki cemin wai inzo inci abinci,wato in rabu da ita ta mutu,ba zanci abincin ba ,ki b'acemin da gani Mariya kafin ranki ya b'ace!!".
Hajiya Mariya da mamaki ta kalli alhaji Abba dan ita bataga abin da ta fad'a na fad'a ba sai dai in zai hucekanta ne.Hajiya Mariya tashi tayi taba alhaji Abba waje kamar yadda ya naima.

Alhaji Abba kukan meenal ba k'aramin d'aga hankalinshi yake ba,alhaji Abba kamar zai yi kuka ya tashi yana mai bubbuga k'ofar d'akin meenal ya ce"Meenalyna dan Allah ki yi shiru tom kibar kukan,dan Allah ki bud'e muyi magana kinji Meenalyn daddy"Mennal ko ai babu alamunma taji abinda alhaji Abba yace bare har ta wani saurarai .Alhaji Abba jin Meenal bata tanka mai ba kamarma bataji abinda yaceba hakan sosai ya k'ara d'aga hankalin shi,hakan yasa kamar wani zautacce yaci gaba da buga k'ofar yana cewa"Meenalyna dan Allah ki bud'ema daddynki ki saurareni muyi magana dan Allah".

Hajiya Mariya da takasa fushi duk da abinda alhaji Abba yayi mata,zuwa tayi takamo hannun Alhaji Abba ganin yadda ya dage yanata bubbuga k'ofar ko zafin hannun shi bayaji.Yajiya Mariya cikin lallami ta ce"Daddyn meenal dan Allah ka saurareni nimafa kaina adamuwa nake,kuma kasan ni kaina bazanso in aurar da Meenal ga Wanda bataso ba,bare kuma ace za ad'auketa kaita kyauye bazanso ba,sai dai in ba yadda zanyi shine zanyi hakuri ,yanzu kamata yayi mu zauna mu sami mafitar abinnan,itacan ta rufe kanta tana kuka tak'i saurararka ,kai kuma kazo nan sai famar bubbuga k'ofa kakeyi kak'i natsuwa ka samo mafita,yanzu zaunawa zamuyi muyi magana muji ta ina zamu b'ulloma al'amarinnan,dan Allah kazo muje ka zauna muyi magana,saninkankane Meenal bazata sauraremu ba yanzu,dan haka sai mu tafi mu samo mafita"Mariya banda wata natsuwa inajin kukan Meenalyn daddy ,dan Allah ki gwada mata magana ke ko zata bud'e sai ayi shawarar baki d'aya da ita" Shiru Hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Tom mu zagaya baya muyi mata magana ta window"

Ta baya hajiya Mariya da daddyn meenal suka je ,Allah ko yasa suka samu window abud'e.Daddyn meenal da saurinsa ya k'arasa jikin window inda ya hangi meenal d'insa ta tusa kanta k'ark'ashin cinyoyinta sai kuka take,babu alamun za tai shiru.Alhaji Abba cikin damuwa ya ce"Meenalyn daddy ki yi shiru dan Allah karkanki yayi ciwo ,ki bud'emin k'ofar muyi magana dan Allah"Meenal d'agowa tayi tana kallan daddynta kamar bazatayi magana ba,sai can ta ce"Daddy Allah bazan bud'eba gara in mutu ma kawai in huta inda kaima kadaina Sona,agabanka akecewa za aimin aure kakasa hanawa,kuma auranma d'an kyauye,ai wallahi sai alhaji yazo gidan nan da bakinsa yace anfasa sannan zan bud'e ,idan ko ba hakaba zamana zanyi babuci babu sha har mutuwa tazo in mutu"Alhaji Abba kamar zaiyi kuka ya ce"Ayyah meenalyn daddy dan Allah ki bud'e kin manta kince bazaki mutu kibar daddynki ba tare zamu mutu?"Alhaji Abba babu kalar allashin da baiyima Meenal ba dan ta bud'e amma tak'i,gashi ta dage sai kuka take kamar wadda ranta zai fita,hajiya Mariya ko babu yadda batai da daddyn meenal ba akan yazo yaci abinci ya barta zata gaji tai shiru,amma k'arshema fad'a yarufeta dashi dole tayi shiru ta tafi tabasu waje.
Abu kamar wasa har akai sallar la'asar amma meenal batabar kuka ba kuma bata bud'e k'ofar ba,nan fa hankalin alhaji Abba ya gama tashi.Wayarshi ya ciro ya kira alhaji,alhaji na d'agawa daddyn meenal cikin alamun tsantsar damuwar da yake ciki ya ce"Alhaji Wallahi tunda kabar gidannan Meenal tarufe kanta ad'aki take kuka ,anyi-anyi tak'i bud'ewa wai sai kazo kace mata anfasa auran nan sansan zata bud'e, dan Allah alhaji kayi wani abu idan bahaka ba yarinyar nan zata iya shiga wani halin,Wallahi yanzu haka bakaga yadda ta fita hayyacinta ba"Alhaji shiru yayi dan shi kanshi saiyaji badad'i jin gudaliyar jikarshi tana cikin wani hali,hakan yasa ya ce"Shikenan bari inzo gidan"alhaji Abba na cewa haka ya kashe wayar.

Daddyn meenal har bakinsa narawa wajan lek'awa ta window yana cema meenal,"Meenalyna kinji munyi waya da alhaji yanzu zaizo dan Allah ki bud'e min kinji "Meenal ka fad'a ta mak'ale alamun bazata bud'eba,alhaji Abba zamewa yayi ya zauna bayan window yana mai sauraran zuwan alhaji.
Alhaji Abba nanan zaune alhaji ya shigo shida hajiya Mariya,alhaji k'arasawa yayi jikin window yana ma meenal kallan mamakin yadda take kuka kamar wadda iyayanta suka mutu,daddyn meenal ko yana ganin alhaji ya tashi da sauri yana cewa"Yauwa Meenalyn daddy kinga alhaji yazo ko tashi ki bud'e min dan Allah" Meenal cikin kuka ta ce"Bazan bud'e ba har sai alhaji ya ce ya fasa min wannan auran sannan ,idan kuma ba hakaba Wallahi anan zanta zama babu ci babu sha har in mutu..........✍️
Chapter 16 · 0% Book details