Sashe 18
Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yadda sarki yace haka ko akai,da daddare mahaifin d'anjuma da yaje gaida sarki ,sarki ke sanar da shi maganar kama hayar da d'anjuma zaiyi a Funtua.mahaifin d'anjuma "To"kawai ya iya cewa,dan bazai iya yima mahaifinshi gaddama ba,yana komawa gida yasanar da mahaifiyar d'anjuma abinda sarki yace mai,aiko nan mahaifiyar d'anjuma tanuna bazata yadda ba,suna cikin maganar ko Allah ya kawo d'anjuma.
Mahaifiyar d'anjuma kallan d'anjuma tayi ta ce"Nasan kai ka sa sarki ya sanar da mahaifinka a Funtua zaka zauna,saboda ita yarinyar bazata iya zama a mahaifarka ba,tom ka bud'e kunnanka da kyau kaji idan har bazaka ajeta garin nan ba,sai dai ka fasa auranta,ka naimi wadda zata iya zama damu,dan bazaka jamana surutun jama'a acikin garin nan ba,tunda ka ke garin nan ka tab'ajin wanda yayi aure bai fara aje matarshi gidansu ba,koda zai ajezata agidansa saninkanka ne sai ya barta agidansu tayi kamar shekara ko k'asa da haka sannan ko zai fidda ta gidansu,amma kai gaba d'ayama garin zaka bar da ita,tom Wallahi banyarda ba , sarki kuma zanje in sa mai muyi magana wata k'ila ya manta al'adar garin nan ne."
D'anjuma dai baice komai ba,dan yadda mahaifiyarshi ta d'auka da zafi haka yasan saukarta sai Allah,gashi duk yadda takejin kunyar sarki ko magana akan abinda ya shafai kasan cewar shi d'an fari amma tana maganar zataje tayi magana da sarki,gashi tabbas sarki na kunyar mahaifiyarshi sosai yadda take darajashi yasan babu yadda za ai yak'i buk'atarta,tom amma indai hakane sai dai in tayi hakane dan afasa auran inda itama tasan meenal bazata tab'a iya zama a kyauyan nan ba,mahaifintama yasan bazai bari ba.
Mahaifin d'anjuma tsawa ya dakama d'anjuma ya ce "Bamu waje ka tsayama mutane akai!"
D'anjuma da yashiga duniyar tunani da sauri ya d'ago yana kallan iyayannashi da yake hango tsantsar k'iyayar auranshi da su ke.Fita ya yi ba tare da yace komai ba.
B'angatan daddyn meenal ko yau alhaji ya aiko yana son ganinshi shida hajiya Mariya.
Da daddare alhaji Abba ya d'auki hajiya Mariya suka je Kiran alhaji,bayan sun gaisane alhaji ya ce "Sani dama nakirakune in tunasar da ku yau saura kwana goma sha shida d'aurin auran Amina,kuma naga har yanzu baku sanar da kowa ba kamar ma baku da niyyar yin hakan?"
Daddyn meenal shiru yayi dan tashin hankalin da yake jin shi ciki ba'a magana.
B'angaran hajiya Mariya ma haka take,shiru tayi dan batasan mai zata ce ba,yan'uwanta ko daddyn meenal ya hana ta sanar da mutane dan yace hakan zaisa meenal taji,tom gudun rigimar alhaji Abba yasa hajiya Mariya taja bakinta tayi shiru,amma tasanar da yayarta da k'anwarta suma kuma sai da ta gargad'esu su yi shiru.Alhaji ko jin sun mai shiru ya ce"Mariya bakujina ne,nace yau saura kwana goma sha shida d'aurin auran Amina,amma buku cemin komai ba,sannan zuwa yanzu ya kamata ace kun sanar da Amina dan banga amfanin b'oye-b'oyan ba."
Sai anan daddyn meenal ya d'ago ya kalli alhaji ya ce"Alhaji dan Allah ina rok'onka alfarma naji na yadda ka aurama meenal yarannan,amma dan Allah dan annabi inaso ab'oyema meenal maganar nan har sai an d'aura aure ni zansan yadda zanyi in sanar da ita,sannan bana buk'atar aimin taro agida saboda yin taron zaisa meenal ta fahimci abinda akeyi dan Allah ataimakamin aimin haka."
Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce "Sani ko mutuwa anatara mutane bare kuma taron biki taron farinciki,amma saboda b'acin ran Amina kace baza ai ba,tom ba zaiyuwu ba."
Daddyn meenal ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Alhaji bawai bana son tara mutane bane saboda b'acin ran meenal a'a,bana son tara mutane ne saboda sanin halin meenal da nayi zatayi abubuwan da mutane zasu tashi da ita,sai inga gara duk abinda za tai da haukar da za tai ace muka d'ai mukaji muka gani ,shine kawai dalilina."
Shiru Alhaji yayi yana tunanin maganar daddyn meenal,sannan ya ce "Eh nagamsu da maganarka,bayan biki sai aba mutane hak'uri"Shiru alhaji yayi sannan yaci gaba da cewa"Dama maganar da nakiraku muyi kenan,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka."Daddyn meenal cikin sanyi ya ce "Ameen"
Daddyn meenal bayan sun dawo gidane ya kalli Hajiya Mariya ya ce "Mommyn meenal nama rasa abinyi game da lamarin nan,wallahi ji nake kamar in gudu kafin bkin ayi komai ba'agabana ba,dan bana son ganin halinda yarinyar nan zata shiga"
Hajiya Mariya kallan alhaji Abba tayi ta ce "Daddyn meenal nifa bana ganin auran nan na Meenal zaije ko ina saboda meenal dai batasan wani abuba waishi biyayya ,garashin kunya daga yaron har iyayan yaron bazasu laminci halin meenal ba,hakan yasa nake ganin abun babu inda zaije ,dan haka ka kwantar da hankalinka mu zubama abin ido muga yadda Allah zaiyi da ikonshi,amma tabbas nikam zanso meenal tayi biyayya ta amshi auranta hannu biyu,amma nasan hakan ba zai yuwu ba.........✍️
Zan rik'a fashin kwana d'aya a posting,mana idan nayi posting yau ba zanyi gobe ba.
📚 MEENALYN DADDY📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Na
Fadila Sani Bakori.
page 25 & 26.
Hajiya Mariya kallan alhaji Abba tayi ta ce "Daddyn meenal nifa bana ganin auran nan na meenal zaije ko ina,saboda meenal dai batasan wani abuba wai shi biyayya ,ga rashin kunya,hakan yasa nake ganin daga yaron har Iyayan yaron bazasu laminci halin meenal ba,hakan yasa nake ganin auran babu inda zaije ,dan haka ka kwantar da hankalinka mu zubama abin ido muga yadda Allah zaiyi.Amma tabbas nikam zanso meenal tayi biyayya ta amshi auranta hannu biyu,amma nasan hakan ba zai yuwu ba."
Alhaji Abba dai bai tankaba dan tuni ya lula duniyar tunani bajin abinda mahaifiyar meenal tace yayi ba ma.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya meenal batasan da maganar auranta nanan ba.
sauran sati biyu bikin meenal ta fara practical a asibitin da daddynta ke aiki.Yau
ya kama saura kwana goma d'aurin auran kamar yadda suka tsayar,yau ne kuma sarki yayima alhaji maganar suna nan zuwa,sosai alhaji yayi mamakin jin zasuzo amma sai bai ce komai ba yayi musu fatan zuwa lafiya .Alhaji daddyn meenal ya Kira awaya ce yasa mommyn meenal tayi girki da yawa masu auran Amina ne zasu zo.Daddyn meenal to ya ce sanan ya Kira hajiya mariya awaya ya sanar da ita.
Sarki su uku sukazo shida k'annan mahaifin d'anjuma.Alhajima kafin su iso ya kira aminin mahaifin meenal ,wato alhaji Kabiru dama alhaji ya sanar da shi maganar auran meenal.Bak'i ko tun kafin su iso alhaji yasa aka kawo musu abincin da akai musu .
Bayan sun gamacin abincin ne an gaggaisa Sarki ya ce tom dama dai akan maganar bikin nan ne naga lokaci ya k'arato nace bari inzo muyi magana,Abdurrahman ya gama kammala kayan lefe,gidama ya kama haya acikin Funtua kamar yadda yayi alk'awari kafin Allah yasa yayi nasa,tom amma dai dalilin zuwana shine tom kasan mu mutanan kyauye da al'adu kala-kala,wato yau kwana bakwai kenan da Abdurrahman yake sanar dani wai mahaifiyarshi tace bata yadda ya aje Amina Funtua ba sai yayi kamar yadda akeyi,wato mu acan yaro ko da ya gina gida tom ba zai aje matar can ba sai ya fara ajeta gidan iyayanshi sannan koda zai ajeta gidan shi,tom shine kar kukaga abu ba yadda mu kaiba da yake ni namamanta da wannan al'adar tamu shine nazo in sanar da ku,Amina zata fara zama agidan su Abdurrahman koda na sati biyu ne dole abisa al'adar wajanmu kafin ta tare gidanta da mijinta."
Murmushi alhaji yayi yace mata kenan masu rik'o da al'ada,ai inda wannan ne bakomai ,ni Wallahi al'adar sai ta burgenima ankoyama yaro abinda bai iyaba ai,kuma yaro ya saba da surikanshi sosai,gaskiya hakan yayi kuma babu komai,ai ni da kasanar da ni aida bakazo ba,yanzu dan wannan maganarce kawai ka kwaso jiki kazo?."
Dariya sarki yayi yace wallahi Abdurrahman ne ya matsamin wai sai dai inzo in sanar da kai."Abdurrahman kenan ya kwantar da hankalinshi babu komai zai auri Amina insha Allah,wannan ai ba komai bane,ni hakanma yayimin dai-dai ta saba da surikannata da sauran mutane ai kafin su tashi."Cewar alhaji.
Sarki sosai yaji dad'in hakan,godiya sosai yayima alhaji ya ce "Alhaji mungode da wannan k'yauna da kake nunamana,kuma insha Allah nayi maka alk'awari kamar yadda kayima Abdurrahman hallacin wannan auran baka duba matsayishi ba,tom insha Allah shi kuma zai saka maka na rik'e Amina tsakani da Allah."
Alhaji ma sosai yaji dad'in furucin sarki,ya ce "Nagode da wannan albishir d'in,yanzu idan kun koma ana gobe d'aurin aure ko jibi dan Allah ku sanar da Abdurrahman ina son ganin shi kafin bikin."
Haka Sarki suka koma gida,duk da alhaji yayi-yayi su kwana sunk'i.
Yau saura kwana bakwai d'aurin auran d'anjuma da meenal, yau ne kuma alhaji yayi Kiran hajiya Mariya da alhaji Abba.
Alhaji Abba kuwa zuwa yanzu ba k'aramin rama yayi ba,dan har meenal takan tasashi da tambaya tana cewa daddy yanzu kabar fira dani, kabar yawan magana,kabar yawan dariya.Alhaji Abba sai dai yayima meenal dariya yace aikine sukai mai yawa,meenal tun tana tanbayar mahaifinnata har ta bar tan bayarshi tayi shiru,idan kuma ta tambayi mommynta sai ta ce mata meenal duk halinda kikaga daddynki ciki akanki ne,ni dai abinda nikeso da ke duk radda mahaifinki ya naimi kemai wani abu tom komai wahalarshi ki mai meenal,dan mahaifinki bak'aramin so yake miki ba,baki da hanyar da zaki sakamai sai ta hanyar bin umar nin shi,da kuma aminta akan duk abinda kikaga shima ya aminta dashi meenal."
Meenal ko sai dai tayi murmushi ta ce "Mommy kenan,nima ina son sweet daddy kamar yadda yake sona."