← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajiya Mariya sunan Meenal ta Kira,dan ta san ba bacci take ba.Meenal na jin haka ta ce"Mommy wai lafiya?"."Tashi za ki yi ku je alhaji na kiranki".Meenal ba tare da tayi wani alamu da ya nuna zata tashi ba ta ce"Mommy nikam gaskiya babu inda zani".
Hajiya Mariya kallan d'an juma tayi da ke sauraran su ta ce"Meenal ki tashi,idan kuma kink'i babu ruwana tsakaninki ne da alhaji,kinji dai abinda yace bazaki bar garin nan ba har sai kin sha addu'ar nan dan haka ki tashi kije ki sha tun wuri kinga dai kin kusa fara practical asibiti tom".Meenal wurgar da abinda ta rufa tayi ta ce" Wayyo wai me nayi ma alhaji ne da ya tsanan haka,mutum duk yabi ya ta kura rayuwata".Meenal ta idasa maganar tana sakkowa daga kan gadon batare da ta kuma cewa komai ba tayi hanyar waje da wani zin bulelan hijab blue black na Mommynta.
D'an juma fita ya yi ya bi bayanta.
Tsaye ya sameta ak'ofar gidan tana wani cin magani,d'an juma kallanta yayi ya ce"Mu je ko?".
Meenal kallan sama da k'asa tayi ma d'an juma sannan ta ce"Ba dai ak'asa ba ko ?"."Beauty mashin d'in na gidan sarki ".
Meenal kallan d'an juma ta kuma yayi sama da k'asa sannan ta ce"Kar in k'ara jin ka kirani da wannan sunan,dan kaga rannan ka kirani ban tanka maka ba shine yauma ka sake kirana da shi,karka sake !".
Kai d'an juma ya jinjina ya ce"Tom ranki shi dad'e bazan kuma ba".Meenal tsaki tayi tana wani yatsine fuska ,ta wuce.

D'an juma cikin wani irin sauk'i ya tsinci kan shi ganin yadda suka jera suna tafiya da Meenal,duk da ba magana suke ba,d'an juma so yake ya sanar da ita sak'on zuciyar shi amma kuma yana jin tsoro.Kallan Meenal yayi ta gefan ido ya ce" Hijab d'in nan yayi miki kyau".Meenal da katawa da tafiya tayi tana ma d'an juma wani irin kallo da ya kasa fassara mai kallan ke nufi.
Meenal ta dad'e tana tsaye tana kallan d'an juma tama rasa abinda zatace mai dan ita gani take rainine kamarta d'an kyauye na yaba kwalliyarta.Meenal da ta rasa abinda zata cema d'an juma sai cewa tayi"Malam yi gaba muje".Wato ma'ana subar jerawa tare"

D'an juma kallanta yayi ya ce"Don me tafiyar mu d'aya kuma zanyi gaba?".Meenal cikin d'aga murya kamar tana magana da wani sa'anta ko kuma k'aninta ta ce"Malam kaga ba wai so nake ina sa'insa da kai ba,kayi gaba nace bana son doguwar magana na shiga tsakanina da kai".
D'an juma murmushi yayi ya ce"Saboda me?,ko kina tsoran afkawa ne?".
Meenal ja tai ta tsaya tana kallan d'an juma dan gaba d'aya tama rasa abinda zatace mai,sai zuwa can ta ce cikin alamun b'acin rai"D'an asabe ka ke ko d'an me?,Ka tsarkake har shanka,kasan da wadda ka ke magana, ana cewa d'an kyauyan mutum dabba ne ban tab'a sanin haka ba sai yau,in banda tsabar dabbanci kai ni zaka cema ko ina tsoran zan abka ka ne".
Sosai kalaman Meenal zuka b'atama d'an juma rai,amma sai ya danne yaci gaba da tafiya ba tare da ya k'ara cewa komai ba.Ahaka suka shiga gidan sarki d'an juma najin zuciyar shi duk babu dad'in kalaman da Meenal ta yi mai"

D'an juma cikin sanyi yayi sallama da alamun 'yar damuwa a fuskar shi.Meenal zama tayi tana mai gaida sarki,alhaji ko kakanta ko kallo bai isheta ba.
Alhaji murmushi yayi ya ce"Ja'irar yarinya wato ni kad'ai ne bazaki gaida ba ko?,Ohoo addu'a ce dai sai kin shata ".
Meenal ba takanma alhaji ba bakin nan dai ta turo.Shi kuma alhaji ya ce"Sarki bata ta sha".
Sarki tashi yayi ya d'akko addu'ar ya mik'ama Meenal,ya ce"Yauwa Amina amsa ki sha da bismillah kin ji".
Meenal amsa tayi tana turo baki ta ce" Ni alhaji sai naje gida zan sha".
D'an juma da ke neman hanyar rama abinda Meenal tai mai yayi carab ya ce"Alhaji ban yarda ba ko taje ba sha za tai ba,tasha agabanka ka gani".
Meenal cikin d'aga murya ta ce"Waye kai!? Wa ke neman yaddarka?, kada Allah yasa ka yarda d'in,Shane kuma bazan sha anan ba d'in sai naje gida".

Alhaji kai kawai ya girgiza Ya ce"Amina amsa ki sha".Meenal baki ta turo ta ce"Alhaji nifa lafiyata lau da zaka ce aban addu'a,cama nayi ban da lafiya ne?"."Amina koma ma lafiyarki lau ki amsa kisha,dan ko ubanki yazo gunnan sai kin sha addu'ar nan yau".
Meenal kallan d'an k'ok'on da akai addu'ar aciki tayi,ita bawai bazata sha bane, taji ta hak'ura zata sha,tom amma kyankyamin abinda akai addu'ar take dama ita kanta addu'ar,hakan yasa bata son sha,amma gudin kar alhaji yaja su k'ara kwana ,dan ita gobe take tunanin zasu wuce.Meenal runtse ido tayi sannan ta d'aga addu'ar ta shanye.
Meenal da gudu ta fita saboda aman da yazo mata,hakan yasa ta ruga da gudu waje taci gaba da kwara amai,kamar zata amaye hanjin cikinta,dan hatta furar da tasha sai da ta amayeta tass"

D'an juma ko ganin Meenal ta fita da gudu tana rufe baki,yayi saurin mara mata baya,ganin yadda take aman yasa duk ya damu.
Zuk'unnawa yayi kusa ita kamar zai rik'eta yana jera mata sannu.
Meenal ko tsabar aman da tayi ne yasa cikinta ya murd'e,zuk'unnawa tayi awajan kamar zata kwanta awajan,tana rik'e cikinta.
D'an juma cikin damuwa ya ce"Sannu tashi muje chamise abaki magani".
Meenal da maganar ma ta gagareta saboda yadda cikinta ya murd'e ,banza tai da d'an juma taci gaba da murk'usanta .
D'an juma ganin haka sai yaga kamar cikin wani hali take,hakan yasa cikin rud'ewa yasa hannu zai d'agota shi da niyyar shi ya taimakamata.
Meenal da ta ga abinda d'an juma ke son ai katawa da sauri ta matsa tana d'aga mishi hannu ta ce"Karka kuskura ka tab'ani Malam,cema akai ban iya ta shine da zaka wani bud'e hannu kai gaka mai taimako mai tausai,Wallahi da ka yi gangancin tab'ani ,da ka yi da nasani".
Alhaji da Sarki da duk suna kallan abinda ya faru,da yadda d'an juma ya nuna kulawar shi akanta na son taimakonta amma k'arshe ta b'age da mai maganganu marasa dad'i.
Alhaji wato kakan Meenal cikin nuna rashin jin dad'in abinda ya faru ya kamo hannun d'an juma ya ce"Sannu ko Abdurrahman,Allah ya baka ladar niyar taimakon da kayi,rabu da ja'ira naga uban da zai taimakamata ta tashi".
Meenal jin abinda alhaji ya ce yasa ta tashi tana cewa"Ko da ban iya tashi da ya tadani gara in shekara agun kwance".

Sarki dai murmushi yayi ya ce" Abdurrahman jeka maidata gida,ku biya ka sai mata magani ".
D'an juma dai bai ce komai ba.Ya dad'e tsaye yana kallan Meenal yana yana jiran ta tashi su tafi.
Meenal sai da ta mila ta milmile sannan ta tashi,daga zuk'unnan da take,tayi hanyar waje batare da ta tankama kowa ba.
D'an juma kallan Sarki yayi ya ce" Bari in rakata indawo".

D'an juma bin Meenal yayi da tabi hanyar gida,alamun ta gane hanyar.Sunyi tafiya har sun kusa gida d'an juma ya kalli meenal ya ce" Mu biya chamise mana abaki magani".
Meenal ko kallan d'an juma ba tayi ba taci gaba da tafiyarta,ahaka suka isa gidan.Suna zuwa Meenal ta zube kan Mommynta tana sakin kuka sosai.Mahaifiyar d'an juma cikin damuwa ta ce"Yayan su lafiya me akai mata?".
"Inna ba ai mata komai ba".
Meenal tashi tayi tana harara d'an juma jin abinda ya ce ba ai mata komai ba,ta ce ma Mahaifiyar d'an juma "Dan Allah kima sarkin nan magana haka kawai zai tasani da dole sai nasha wata addu'a ni ce mai akai Banda lafiya ne,ni dai dan Allah ki mai magana".Mahaifiyar d'an juma cikin lalla shi ta ce"Ki yi hak'uri kinji Amina ki daure ki sha kinji ,ba'ama tsofaffi musu".Haka mahaifiyar d'an juma tai ta ba meenal baki.Mommyn Meenal dai bata tanka musu ba.
D'an juma ko tun tuni ya fice daga d'akin.Ba dad'ewa sai gashi ya dawo da kayan tea a hannun shi,Mahaifiyar shi ya mik'amawa ya ce"Inna gashi a had'a mata tea ta yi amai a gidan sarki".Hajiya Mariya kallan d'an juma ta yi,ta ce"Sannu da k'ok'ari Abdurrahman" .
D'an juma murmushi yayi ya fice daga gidan"
Chapter 11 · 0% Book details