← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhaji Abba zaune gaban Mahaifin shi,bayan sun gaisa ne,Alhaji Abba ya kalli Mahaifin shi ya ce"Alhaji gani".Shiru Alhaji yayi,wato kakan Meenal,sannan ya ce" Sani akan maganar da mukayi da kaine,yau kwana goma sha hud'u kenan"Numfasawa dattijon yayi sannan yaci gaba da cewa"Nagaji da zuwa nai man auran Meenal da akeyi wajena,nayi maka magana akan Yaron gidan Alhaji Musa,amma shiru Sani ba kaimin maganar ba har yau ,tom yau ya sake dawomin ".Alhaji wato kakan Meenal ya idasa maganar cikin damuwa.
Numfasawa Alhaji Abba yayi,sannaya ce"Alhaji yaron ne ban yadda da tarbiyar shi ba shi yasa kajini shiru ".
Alhaji kallan Alhaji Abba yayi kawai ya girgiza kai sannan ya ce"Sani fad'amin kai ne baka son aurar da Amina koko Aminar ce bata son yin auran inji,ina fa sane, rashin kula masu nai man auranta da bakayi ne yasa aka fara zuwa wajena naiman auran Amina".Alhaji Abba shiru yayi dan bai son abinda zai ce ba,shiko kakan Meenal jin haka sai cewa yayi,"Sani yau zan fad'a maka abinda baka sani ba,kuma itama Amina ina tunanin kai tayi gado inma ciwone ko kuma ra'ayi,wato Sani sai da nasa akai ta maka addu'a ana baka kana sha sannan nasamu hankalinka ya juyo akan maganar aure,sanin kankane abokanka babu Wanda baiyi aure ba sannan kayi,nasha surutun muta ne akanka,tom kadubafa kai namiji ne akaimaka shurutu ina ga Amina Amina fa mace, Allah ya yi Amina da farinjini amma kai da ita kunk'i,tom koma dai menene insha Allah abinda nayi maka shi zan mata,dan haka ka shirya kai da iyalanka zuwa gobe zamu je Katsina wajan Malam Abdullahi Wanda mukai karatu tare shine dama alokacin ya yi ta tofamaka addu'a aruwa ina kawoma kana nasha tom amma kai alokacin faka fashinci komai ba,kuma cikin yaddar Ubangiji Allah yasa hankalinka ya dawo akan maganar auran,tom inajin itama Amina hakan za ai mata tun wuri,kuma mu tafi gaba d'aya tare mu gaida shi zaiji dad'i kaga nima nayi tsohon zuminci,dan rabona da shi tun lokacin naje mai da albishir d'in auranka,Sai kuma gobe insha Allah zamu tafi dan haka ka tashi kaje kasanar da su"
Alhaji Abba da gaba d'aya zifa yakeyi kota ina dan shi kanshi bai shirya zuwa Katsina ba yanzu,hakan saya cikin sanyi da naiman alfarma ya ce"Alhaji Katsina fa yanzu bata shiguwa,dan Allah idan ma hakane tom ka bada sak'omana akai mai,sannan inada meeting gobe,dan Allah Alhaji kabar magan...".Hannu Alhaji ya d'agama Alhaji Abba ya ce"Wallahi koda na samu Wanda yasan gidan Malam Abdullahi tom bazan ai ka mai ba,ai da kunya shekaru kusan talatin ace in akamai da sak'o,ko bama haka ba zuwa da kai yafi sak'o.Sannan Katsina da kake maganar babu lafiya yanzu ,ai ba cikin Katsina bane kyauyan Katsina ne,dan in ba yanzu ba garin ko network basu da shi"

Alhaji Abba cikin damuwa ya ce "Alhaji ai kyauyukan ne abun gudu,saboda anan ake ta'addancin ai,alhaji dan Allah ka yi hak'uri da tafiyar nan sai n...""Sani babu abinda zai hana tafiyar nan gobe insha Allah,tashi ka tafi".Alhaji Abba da yarasa abin cewa tashi yayi ya yi ma Mahaifinna shi sallama ya tafi"

Koda Alhaji Abba ya koma gida ,Allah yasa bai iske kowa afalo ba hakan yasa yayi part d'in shi,yana shiga ya Kira hajiya Mariya awaya yace tasamai part d'in shi"

Hajiya Mariya bayan ta zauna ne ta kalli Alhaji Abba ganin yayi shiru da'ido kawai yake binta ta ce"Daddyn Meenal lafiya kuwa?"
Numfasawa Alhaji Abba yayi ya ce"Mommyn Meenal Wallahi abinne yasha min kai ban san yadda zanyi da Meenal ba ta yadda da wannan tafiyar.Alhaji wai dole sai munje Katsina gobe kuma harda Meenal,kuma kyauye ".Shiru hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Lafiya meza ayi a Katsinar?"."Wai Meenal za'aima addu'a kinsan tsofaffin nan da k'irk'irar abu,idan ba hakaba yarinya lafiyarta lau babu abinda ke damunta amma wai sai anyi tattaki anyo mata addu'a sai kace mai wata lallurar" Ita kanta hajiya Mariya shiru tayi dan ta jinjina tafiyar ,dan Meenal takan fad'i da bakinta haushin d'an kyauyan mutum takeji shi yasa tama gode da basu da 'yan'uwa akyauye.Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi da yayi tagwumi sai kace wadda aka aikoma da wani bala'in ta ce"Tom Daddyn Meenal ni kaina abin nama rasa abinda zance dan Wallahi bansan wayan da za'ai ma Meenal ba ta yadda aje kyauye da ita,dan har fariya take basu da "Yan'uwa akyauye,duk da tace koda suna dasu Wallahi bazataje ba,kuma bazatayi zuminci da suba,ba adad'e ba ina nan ina kallan wani film da arewa tasa ,ashe itama tana kallo tashi tayi ta kashe tibin ,wai da me zan k'aru zan zauna intasa tibi gaba ina kallan abin ta kaici.Gaskiya ganinake in dai dole sai antafi da ita, tom karka fad'amata inda za'a ,dan indai ta sani bazata ba"
Shiru Alhaji Abba yayi na d'an wani lokaci sannan ya ce"Kina nufin inyi ma Meenal k'arya?".Ikon Allah sai kace Uwarka.
Alhaji Abba yacigaba da cewa"Bazai yuwuba in b'oyemata gara in fad'amata gaskiya in samu in lallasheta,yanzu ki sameta ki fara mata maganar tafiyar kiji me zatacemiki,amma karfa ki mata maganar dalilin tafiyar"Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Nida nasan halin 'yan kayana akan me zan fad'amata,so kake in ruguza tafiyar kenan".hajiya Mariya na fad'in haka ta tashi ta ce"Bari inje inyima ta maganar tun yanzu"

Meenal kwance kan caution tana game awayarta,hajiya Mariya tazo ta sameta.Hajiya Mariya kallanta tayi ta ce"Sarkin buga game,daddynki ya ce ki tashi ki shirya gobe zamu Katsina"Meenal aje wayar tayi tana kallan Mommynta ta ce"Mommy katsina kuma ,wannan wata irin tafiya ce babu shiri,kuma daddy yana da dangine a Katsina?".Hajiya Mariya zama tayi ta ce"A'a abokin Alhaji ne zamu mu gaid..."Hajiya Mariya mata gama maganarta ba Meenal ta amshe maganar da cewa"Mommy nikam gasjiya bazani ba,sai kun dawo,haka kawai Katsinar da bazaman lafiya ake ba".Hajiya Mariya rufe bakin Meenal tayi ta ce"Kul!Karki k'ara cewa bazaki ba,wannan tafiyar dolece ,dan haka karma in k'arajin maganar bazaki ba.Maganar Katsina kuma ba lafiya ai ba cikin gari zamu ba,kyauyan Katsina zamu".Meenal tashi tayi ta zauna tana ajewayarta ta ce"Mommy dan Allah inma daddy ne ya aikoki ki cemai bazani ba,kema dai kinsan bazanje ba,ni me zai wani kai ni kyauye,koma lafiya bare kuma kyauyan Katsina,gaskiya mommy bazani ba"Meenal na kaiwa haka ta tashi ta nufi part d'in daddynta tana turo baki,tana zuwa ko sallama babu ta ce"Daddy kaji kuma abinda Mommy ta k'ara tsiro da shi kyauyan Katsina zamu tafi gobe wai?"Daddyn Meenal hannun Meenal ya kamo ya ce"Zokiji Meenalyn daddy,ba Mommynki bace ta ce nina ce"Meenal kamar za tai kuka ta ce"Amma dai daddy ai kaima kasan ni bazanje ba,kuma wai akanmema sai dani dole za'a?"."Haba Meenalyn daddy tunda nina ce dan Allah ki shiya mu tafi,idan mun'isa da wuri tom ba zamu kwana ba,muna zuwa zamu dawo"Meenal juya baya tayi tana turo baki,babu dai alamar ta amince.Alhaji Abba ko cigaba yayi da lallashin Meenal daga k'arshe yayi mata alk'awarin daga sun dawo zai kaita Mina wajan yarinyar k'anwar Hajiya Mariya da Allah ya had'a jinin Meenal da ita.Meenal jin haka yasa ta amince da sharad'in bazasu kwana ba.
Dole alhaji Abba ya bitada "Eh".Saboda ta yadda amma ya san dole sai sun kwana bazai yuwuba suje su dawo ranar kodan tsoran hanya".

Alhaji Abba sosai yaji dad'in amincewar Meenal,dan bai tab'a tunanin zata amince ba.

Da daddare Alhaji Abba na kallo Meenal kuma na chart da yarinyar k'anwar mamarta ta Mina wato Hafsat tana sanar da ita tafiyar da zasuyi gobe.Hafsat jin Meenal zata kyauye yasa taita mata dariya daga k'arshe ta ce"Kar dai kije wani d'an kyauyan ya mak'alemiki ,kuma wallahi bashi zamuyi"bak'in cikin maganar yasa Meenal ta aje wayar batare da ta rufe ko datarta ba.Alhaji Abba da hajiya Mariya da hankakinsu ya koma kan kallo sai ji sukai Meenal ta d'ad'e da kuka.Alhaji Abba da Hajiya Mariya kusan atare suka iso wajan Meenal ,bakamar alhaji Abba ba ,cikin damuwa ya ke cewa"Meenalyn daddy lafiya,yi shiru ki fad'amin karkanki yayi ciwo?".
Meenal cikin kuka ta ce"Ba Hafsat bace wai kar in samomusu d'an kyauye" .Alhaji Abba lallashin Meenal ya fara yana cewa"Kiyi shiru dan Allah karma kanki yayi ciwo akan shirman maganar nan"Haka alhaji Abba ya dage sai lallashi yake dakyar ya samu Meenal tayi shiru.

Washe gari da wuri suka gama shirinsu suka kama hanyar gidan Alhaji,Meenal dai yau bata magana da kowa,dan daddynta ma ganin Meenal kad'an take jira tasa mai kuka yasa shima yaja bakin shi yayi shiru.Koda suka je gidan Alhaji,wato kakan Meenal sun samu ya shirya su yakejira.
Hajiya Mariya da alhaji Abba haka suka gaisa da kakan meenal cikin girmama,inda Meenal ko kallan shi tak'iyi.
Alhaji kallan Meenal yayi ya ce"Amina har yanzu kinanan da halinki na miskilanci ko?".Meenal turo baki tayi ta ce"Karabu dani dan bagaidaka zanyi ba,kawani jawoma mutane zuwa kyauye muna zamanzamanmu lafiya"."Uwaki nace kice bazakiba mana dan'ubanki tafiyar duk danwa za'ayita badan keb....".Daddyn Meenal jin Mahaifinshi zai janyomai rigimar meenal yayi saurin katse shi da cewa"Alhaji rabu da Meenal kazo mutafi kar lokaci ya k'ure"
Alhaji Abba shiga yayi inda Meenal da Mommynta suka zauna a baya.Alhaji Abba yaja motar suka tafi..................✍️

Shere & Comment please🙏🏻

📚 MEENALYN DADDY📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Na
Fadila Sani Bakori.

Page 7&8.
Chapter 5 · 0% Book details