← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 21

Sashe 15

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mahaifin d'an'juma da yana can gona yana aiki,aje aikin yayi ya hawo keken shi ya kamo hanyar gida.
Can wajan su Sarki ko,bayan d'an'juma ya fita Sarki ya kalli alhaji ya ce"Alhaji auran nan fa da kake son had'awa gaskiya za ashiga hak'in Amina,ni sai inga yanada kyau dan aji dad'in abinnan sosai ace da amincewar Amina za'ayi" Alhaji dan yayi maganin Sarki sai cewa ya yi "Malam Haruna indai ba wai kafi son Abdurrahman ya auri 'yar nan bane,dan Allah ka sama abin nan albarka kawai,Amina kuma muna fatan tabamu mamaki".Sarki jin haka sai yayi shiru ya ce"Tom inda kayima maganata wata fassarar nayi shiru alhaji,Allah yasa duk muce gara da akayi" "Yauwa tom haka zaka ce".
Su alhaji su na nan suna tattaunawa akan maganar ,Mahaifin d'an'juma yayi sallama ya shigo.Mahaifin d'an'juma da fara'arshi suka gaisa da alhaji .Nan dai yayi musu anzo lafiya,sannan ya kalli Sarki ya ce"D'an'juma ya jirani inakan aiki da yake yau naje sharar gona yace kana kirana?".Alhaji ne ya amshe zan can da cewa"Eh ,ni nace ya kiramin kai.Wato zuwan yarinyar ta wajan Sani wato Amina Abdurrahman ya nuna yana sonta,ni kuma nayi mai alk'awarin samo mai auran Amina,tom atak'aice dai yanzu haka na samoma Abdurrahman auran Amina,shine nazo yanzu mu tsaida lokacin biki".
Mahaifin d'an'juma rasa abin da zaice yayi, dan sai yaji maganar wata iri,da kyar dai ya samu ya bud'e baki ya ce"Tom amma alhaji ina d'an'juma ina Yarinyar nan,ai tafi k'arfin shi,sai dai kankanba irin ta yaran yanzu,amma ni gani nake ai ba biyema d'an'juma za'ai ba,taya yarinyar da ta tashi cikin kankara yace zai zo ya aje ta a nan ai abinnan ma ba zaiyuwu ba"
Sarki gudin kar alhaji yaga kamar basu San abinne ya ce"A'a ya ce wai a Funtua zai ajeta"
Mahaifin d'an'juma shiru yayi dan bai san abin da zai ce ba kuma.Sarki ganin Mahaifin d'an'juma ya kasa magana tashi yayi ya je inda yake ajiyar kud'i ya k'irgo dubu goma ya kawo ya ce"To dama dai ni zan biyama Abdurrahman komai na aure,dan haka ga kud'in sarana inda kace gobe da wuri zaka shige sai ayi komai yau,shi kuma Abdurrahman d'in zansa ya kawo alawa da biski(biscuit) da kan shi" Alhaji sosai yaji dad'in abinda Sarki yayi hakan yasa ya ce"Ai wannan kud'in sun isa,daga su ma ba sai ankawo komai ba,yanzu bari Abdurrahman yazo sai muji yaushe za'a tsaida auran" "Eh tom bari in kira shi awaya ai yana kusa".
Sarki Kiran d'an'juma yayi awaya.Suna nan zaune d'an'juma ya shigo,bayan d'an'juma ya zauna ne Sarki ya kallai ya ce"Abdurrahman nan da wata nawa kake ganin zaka iya gabatar da hidamar auran nan da muke son tsaidawa yau insha Allah?" D'an'juma rasa abinda zaice yayi dan sai yaji maganar kamar wasa.Sarki murmushi yayi dan ya fahimci d'an'juma al'ajabi ne yasa ya kasa magana,hakan yasa ya ce" Abdurrahman wata nawa kake ganin idan munsa ka shirya?" D'an'juma d'agowa yayi ya kalli mahaifin shi,ganin ba shi ya ke kallo ba sai ya maida kallan shi ga Sarki ya ce "Duk yadda kukayi yayi" "A'a Abdurrahman ai kaine mai hidima kai zaka fad'i lokacin da kake ganin ka shirya sai mu kuma muduba mu gani" Cewar alhaji.Shiru d'an'juma yayi dan baima san abinda zai ce ba,kallan Sarki yayi ya ce"Duk lokacin da kukasa yayi alhaji"Magana Sarki zai kuma yi,alhaji ya rigashi da cewa"A'a Malam Haruna inda yace duk lokacinda akasa yayi,ma'ana kenan yanada shiri,dan haka ina ganin mubar abin wata uku ai yayi ko?" "Eh yayi ,Allah ya kaimu lokacin"Sarki ya fad'i hakane kawai amma shi bai tab'ajin sarana wata uku ba,su da duk saranar su shekara guda wasu shekara biyuma,akasarima wata yarinyar kusan tun kan ta idasa auran ake badata asa rana,daga lokaci yayi sai dai asha biki.
Alhaji kallan Sarki yayi ya ce"Tom Masha Allah na cika alk'awarin da na d'aukar ma Abdurrahman,yanzu Abdurrahman sai ka samu lokaci ka je Kadunar ku gaisa da Aminar" D'an'juma dai kai ya jinjina.Mahaifin d'an'juma ko kasa cewa komai yayi .
Ahaka dai suka gama zantawar su suka tashi "

Mahaifin d'an'juma na zuwa gida ya kalli mahaifiyar d'an'juma ya ce"Ashe d'anki aure zaiyi amma Banda labari?" Mahaifiyar d'an'juma da alamun mamaki ta ce"Wana d'annawa?"Mahaifin d'an'juma ,d'an'juma ya nunama mahaifiyar d'an'juma da zuwanshi kenan.
Mahaifiyar d'an'juma da mamaki da kuma alamun farincikin d'annata zai aure ta ce" Kai Alhamdulilah,Allah mungode maka,tom ni inama nasani,har'an bashi auran yarinyar ne?" "Har'ansa rana ma wata uku masu zuwa".
"To fa amma dai yarinyar banan garin take ba?" "Yarinyar da tazo nan ta zauna 'yar Kaduna ita"Mahaifiyar d'an'juma cikin zaro ido ta ce"Amma dai bata amincewar yarinyar ba ko?,dan ko ranar da zasu bar garin nan ta ce ma mahaifiyarta bata fatan abinda zai k'ara kawota garin nan,dan haka idan ma maganar nan wasace tom banason k'ara jinta,idan kuma da gaske ce in dai nina haifeka tom wallahi kayi gaggawar janye maganar nan ,dan bazaka auri Yarinyar nan ba,yarinyar da bata kallan kowa da mutunci ,mu nan duk ba kallan mutane takemana ba,taya zakaji dad'in zama da yarinyar nan,daga kai harmu babu Wanda zai ji dad'in auran nan,dan haka kai maza-maza kafin Sarki ya fitar da maganar nan kowa ya sani ka tafi ka sanar dashi ka fasa "

D'an'juma shiru yayi dan yana ganin halaccin da alhaji yayi mai amma kuma sai ya ce mai ya fasa.D'an'juma kallan mahaifiyar shi yayi ya ce"Innna alhaji yayi Mana halacci sosai,mu ya kamata muje wajansu naiman aure amma shine yazo,yanzu kuma angama magana sai ince mai na fasa?" Mahaifiyar d'an'juma zata k'ara magana mahaifin d'an'juma ya d'aga mata hannu ya ce" Maryama inda dai anriga an tsaida magana shikenan,duk Wanda ya d'akko da zafi bakin shi,ban mai baki ba,amma dai nasan ba zai tab'ajin dad'in zama da yarinyar nan ba.Allah ya sanya alkairi sai ka k'ara hak'uri akan wanda kake da shi tun yanzu.......✍️

📚 MEENALYN DADDY 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Na
Fadila Sani Bakori.

Inama 'yan'uwa da abokan arzik'i barka da sallah,musamman masoya littafin meenalyn daddy.

Page 21 & 22.

D'anjuma shiru yayi dan yana ganin halaccin da alhaji yayi mai Amma kuma sai ya ce mai ya fasa auran da bakinsa ya amsa yana so.D'anjuma numfasawa yayi sannan ya kalli mahaifiyarshi ya ce"Inna alhaji yayi mana halacci sosai ,mu ya kamata muje wajansu naiman aure amma shine yazo wajan mu yanzu kuma angama magana sai ince mai na fasa?"
Mahaifiyar d'anjuma zata k'ara magana mahaifin d'anjuma ya d'aga mata hannu ya ce"Maryama indadai anriga an tsaida magana shikenan duk Wanda ya d'akko da zafi bakinsa,ban mai baki ba amma nasan ba zai tab'a jin dad'in zama da yarinyar nan ba.Allah ya sanya alkairi ,sai ka k'ara hak'uri akan Wanda kake dashi tun yanzu"
D'anjuma shiru yayi kanshi ak'asa,dan tabbas shi kanshi yarasa acikin halin da yake ciki,shin murna yake ko fargaba.Mahaifiyar d'anjuma kuwa cewa tayi"Malam bamu tab'a jayayyaba ,amma gasjiya yau zamuyi,dan ban yadda da wai inda anriga anyake magana shikenan ba,gasjiya banyadda ba,ya koma yasanar da sarki idan kunyar kakan yarinyar yakeji alabashi sarki sai ya sanar dashi ya ce anriga anbashi yarinya"daga mahaifin d'anjuma har d'anjuma shiru su kai dan shi kanshi mahaifin d'anjuma bawai son auran yake ba,mafitace kawai da yarasa.Mahaifin d'anjuma ya dad'e bai iya cewa komai ba,sannan ya kalli mahaifiyar d'anjuma da kallo d'aya za kai mata kasan ranta ab'ace yake .Maihaifin d'anjuma kallan d'anjuma yayi da kanshi ke duk'e ya ce"Tashi kaje abinka Abdurrahman"D'anjuma tashi yayi ya fita.Bayan d'anjuma ya fitane,mahaifin d'anjuma ya kalli mahaifiyar d'anjuma ya ce"Maryama naji abinda kikace,amma da zaki bud'e zuciyata ki gani wallahi nafiki k'in wannan auran da akaba Abdurrahaman,saboda tunda yarinyar nan tazo gidannan har suka tafi bata tab'a min kallan arzik'iba,amma tabbas mahaifiyarta mutuniyar kirkice,tom amma tafi k'arfinta ,ni aganina mutaya Abdurrahman da addu'ua Allah tabbatar da abinda yafi alkairi,saboda abinda kikeso ba zai tab'a yuwuwaba,maganace sun riga sun yanketa,dan haka saidai fatan alkairi kuma".
Har mahaifin d'anjuma ya gama magana mahaifiyar d'anjuma bata iya kuma cewa komai ba.

B'angaran alhaji ko sa sarki haka suka raba dare suna hira akan auran jikokinnasu.
Washe gari da wuri alhaji ya tasa Isuhu suka kama hanyar Kaduna.
B'angaran daddyn meenal ko alhandulillah jikinshi da sauk'i sosai ,sai dai tunda hajiya Mariya ta sanar dashi alhaji ya tafi garinsu d'anjuma ya shiga cikin farkagaba ,kuma tun daga lokacin yanayinshi gaba d'aya sai ya canza.
Yauma haka daddyn meenal ya wayi gari da fargabar nan,haka dai ya daure yayi breakfast.
Chapter 15 · 0% Book details