← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 21

Sashe 7

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

d'akine guda d'aya kamar yadda dai kukasan d'akin kyauye,sai gadaje guda biyu na k'arfe ,angyaresu tsab,d'akin irin babban d'akin nan ne watacce.Maryama tabarma ta d'akko ta shimfid'amusu tana mai cewa"Barkan ku da zuwa hajiya ku zauna".Mommyn Meenal zama tayi tana mai cewa"Yauwa sanninku ,mun sameku lafiya".Nan dai suka gaisa sosai kamar sunsan juna,inda Meenal ko kallo mata bata isheta ba,ita kuma da fara'arta ta ce"Sanninku da zuwa"."Yauwa ".Meenal tace can cikin mok'oshi.Ruwa mai sanyi na randa ta kawo musu .Dama koda Sarki ya aikomata da tayi abinci yayi bak'i da take tana saida taliya 'yar murza ita ta d'ora musu tai musu jaloup d'inta.Bayan ta aje ruwan taliyar ta kawomusu sannan ta basu waje ta tafi d'akin yara ta tada sallar acan".Hajiya Mariya da ke son taliyar hausa cigaba da cin abinta tayi ta kalli Meenal ta ce"Meenalyn daddy kinga ni ko'ina fes matar na da tsabta sosai kici kinji".Meenal fuska ta ya mutsa ta ce"Mommy nifa bazan iya cin abincin nan ba,kika sani kodan an aikomata ne anyi bak'i ta gyara gidan,sannan duk "yan kyauye k'azamai ne,masu girki da ruwan kogi,nikam bazan iya ciba, keda za ki'iya kici".Mommyn meenal kallan Meenal tayi ta ce"Meenal kenan,nan ai bawani shahararran kyauye bane,bikiga sunada da tuk'atuk'a ba da wutar Nepa?"."Uhm".Meenal ta ce. Hajiya Mariya haka taci taliyarta ta k'oshi Meenal ko tak'i'ci.Hajiya Mariya na gamaci ta d'auki buta tayi alwallah tayi sallah,Meenal ma tashi tayi tayi alwallar ta tada sallar itama.Bayan duk sun idar ne Maryama wato mai shashin tazo ta zauna ,tana mai kara musu sannu da zuwa,ganin abincin da takawo musu sunci kad'an ta ce"Hajiya abincin beyi dad'i ba ko naga kunci kad'an".Murmushi Hajiya Mariya tayi ta ce"A'a wallahi da yake ni inama son taliyar hausa naci sosai,Meenal ce bataci ba"."Ayyah tom ko fura za'a samo mata ne?".Hajiya Mariya tasan Meenal na son fura sosai,amma ganin sunan taraina musu wayau hakan yasa ta ce"A'a batajin yunwa ne aniima zataci".
Haka dai su kaita fira sama_sama ,har almuru ya gabato ,Maryama tashi tayi ta d'ora tuwan dare,tanayi suna hira da Hajiya Mariya.Kub'ewa Maryama ta d'akko zata yanka hajiya Mariya ta amsa ta yanka mata duk da tak'i hajiya Mariya ta nuna dole sai ta yanka hakan yasa ta bata.Ana sallar magriba ta tuk'a tuwan dawarta ta d'ora miyar, dama sarki ya aiko da zakaru biyu da yasa aka yanka yace ajuye su duka amiyar,da yake Maryama akwai iya girki da sarrafa girki hakan yasa ta raba uku tasa Kashi d'aya amiyar, Kashi biyu kuma ta yi musu farfesu da shi,aiko take b'angaran yahau k'amshi ,Meenal da bajuriyar yunwa gareta ba,take yunwa ta sata baccin dole.Hajiya Mariya bayan ta'idar da sallar magriba ne ta tadata akan tayi sallah,Meenal sosai tayi mamakin k'amshin da takeji azuciyarta sosai ta yaba da k'amshin dake tashi agidan,haka dai tayi sallah ta idar ta tashi ta tada sallar issha'i da ake kira.Itama hajiya Mariya sallar ta tashi tayi,dama maryama ta kawo musu tuwan ta aje musu harma da ruwan sha ,suna idar da sallah aka kawo Nepa ta haske wajan .Hajiya Mariya tana idarwa ta fara cin tuwanta dan tana marmarin tuwan dawa sosai,kallan Meenal tayi dake zaune tana kallanta, dagani kuma yunwa takeji,hajiya Mariya dai banza tayi da ita taci gaba da cin tuwanta dan sosai tuwan yayi mata dad'i.Meenal kallan hajiya Mariya tayi ta ce"Mommy kamar tuwan honey Well ko?"Hajiya Mariya Dan Meenal taci dan tasan indai tace mata irin tuwan da in sukaje Kano wajan Yayarta takeyine bazataci ba yasa ta ce"Eh Meenal shine".
Meenal kallan Mahaifiyarta tayi ta ce"Mommy Allah yana kama da tuwan da kike cewa Mommyn Aisha taimiki in munje Kano".Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Tom kici kiji mana". Meenal hannu tasa tana turo baki kamar anmata dole taci.Loma d'aya taci tayaba da dad'in girkin kuma dama gaskiya ta yaba da tsabtar matar sosai.Sosai tuwan yayi ma Meenal dad'i dan har da cewa"Mommy da kad'an kika fita iya tuwo".Hajiya Mariya dai batace komai ba,murmushi tayi ta ce"Kin ma fad'i gaskiya.

.Haka su hajiya Mariya da Meenal suka ci tuwansu sosai dan sun yaba da dad'in tuwan.Bayan sun gama ci ne nan Maryama ta dawo ta nuna musu inda zasu kwanta ,itama tai musu sai da safe taja musu k'ofar ta fita"

B'angaran su Alhaji ko suma bayan sun gamacin tuwan sun dad'e suna santin shi.Sarki d'akin d'an juma ya kai Alhaji Abba ya ce ya kwanta su kuma zasu kwanta shi da Alhaji tare .

Da daddare Alhaji wato kakan Meenal ya ce"Malam Haruna wato zan iya cewa tafiyar nan tamu gaisuwa ce da rok'on iri mu kai,wato Amina yarinyar wajan Sani,jikata kenan wadda kagani d'azu, Wallahi malam yarinyar nan in ra'ayine in ma ciwo ne dai tom ta gado wajan mahaifinta,in bazaka manta ba na dad'e ina amsar addu'a awajanka ina ba Sani dan hankalin shi ya juyo akan maganar aure,tom itama yarinyar nan da kagani Amina haka take kaganta dai babu maganar aure akanta,tom duk da mu acan Amina ba wata babba bace wadda za'aima surutu dan ba tai aure ba,amma ni gaskiya awajena tuni ta isa aure inda bamu manta al'adar iyayan mu ba,da kuma koyarwa ta addinin musulinci,tom shine fa na had'o abin biyu mu sada ziminci kuma aima Amina addu'a itama kamar yadda akaima Mahaifinta kafin ya auri mahaifiyarta".Shiru sarki yayi ,ya ce"Tom Malam garama ku can sai ace birnine babu mai maka surutu,amma bari kaga zuwa gobe zaka Abdurrahaman ,wato d'an juma kenan,Wallahi Alhaji kaikanka zaka fad'a ko acan birni yaci afara mai surutun rashin aure bare kuma munan kyauye ,da sa'annin shi sun manta da sunyi aure dan da akwai wanda ya aurar da 'Ya ma,amma shifa har yanzu babu maganar auran akan shi,nayi addu'ar nayi na kuma,tom har yanzu dai Allah bai kawo lokacin ba,Yanzu haka maganar da nakema mahaifin shi sama_sama yake mai magana saboda rashin aure".Shiru sarki yayi sannan ya ce"Yau she zaku kuma ne?,sai mu fara addu'ar zuwa gobe".Eh tom gobe gaskiya mukasa zamu koma,amma idan ba zai yuwuba sai mu k'ara kwana ai".Shiru sarki yayi sannan ya ce"Gaskiya idan sansamu ne ita Aminar abarta anan koda kwana goma ne mugani ".Tom shikenan ai ba damuwa,nima ina nan inda hakane shi Sanin sai su tafi shida Mariya,mu kuma mu zauna nida Aminar"
Haka dai su kaita firar su ta yaushe gamo har bacci ya kwashe su".

Washe gari,Alhaji Abba bayan sun gaisa da Alhaji ne yake sanar da shi sai dai shida hajiya Mariya su tafi,shida Meenal kuma sunanan har agama ma Meenal addu'ar nan da kwana goma".Alhaji Abba rasa abinda zai ce yayi dan yasan da akwai daru wajan Meenal sosai,amma babu damar yayi ma mahaifin shi gaddama hakan yasa ya ce"Tom shikenan,Alhaji idan hakane ni yanzu zan wuce dama ina da meeting yau".Alhaji Abba na fad'in haka ya tashi yayi musu sallama ya ce"Tom ni zan wuce idan munyi waya naji ranar da zaku dawo".Alhaji Abba na kaiwa haka yayi musu sallama ya tafi,dan Sarki na cewa ya tsaya ko karyawa mana yayi ,ya ce"Wallahi yanzu haka ana jirana ne".
Alhaji Abba haka ya tafi baima Meenal da Mommynta Sallama ba ,dan yasan indai Meenal taji zata zauna za'asha daru ,bazata yadda ya tafi yabarta ba,hakan yasa ya tafi bai musu sallama ba......✍️

Meenalyn daddy yanzu zamu shiga cikin labarin Sister,bini ahankali🚶‍♀️🚶‍♀️🚶‍♀️.

Share & Comment plz

📚 MEENALYN DADDY📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Na
Fadila Sani Bakori.

Page 9 & 10

Alhaji Abba sai da ya shiga cikin garin Kaduna sannan ya Kira Airtel d'in Mommyn Meenal dan yaji ance basu da network d'in M.T.N,Hajiya Mariya zaune take tana karyawa da kunu da k'osan da Maryama ta kawo musu .Meenal ko da ma ko agida ba shan kunu take ba.Hajiya Mariya na cikin shan kununta Kiran Alhaji Abba ya shigo wayarta,d'auka tayi tana mai kangawa a kunnanta .Bayan hajiya Mariya sun gaisa da daddyn Meenal ne yake sanar da ita ya tafi.Hajiya Mariya cikin mamaki ta ce"Daddyn Meenal ka tafi kuma kamar ya,mu fa?".Meenal da mamaki take kallan mommynta.Amsar wayar tayi daga hannun mommynta ta kanga akunnanta ta ce"Daddy kana ina?".Alhaji Abba cikin lallami ya fara magana,kamar haka"Meenalyn daddy meeting gareni 8:00 AM ,shi yasa banzo mu kayi sallama ba ina saur..."Meenal katse daddynta ta yi da cewa"Daddy wai kamar ya bangane ba,mu fa sai yaushe zamu tafi?".Alhaji Abba cikin lallami ya ce "Meenalyna ki yi hak'uri kinji ,Alhaji ya ce dole keda mommynki zaku zauna ku dawo tare,nan da sati mai zuw....".Ai Meenal bata gamajiba,ta yi wurgi da wayar ta fasa kuka.Maryama dake waje da saurinta har tana tuntub'e ta shigo d'akin tana tambayar lafiya.

Meenal kuka take tsakaninta da Allah ita tafiya za tai.Maryama cikin damuwa ta kalli hajiya Mariya da bata tankama Meenal ba tsabar haushi ta ce"Hajiya lafiya bata da lafiya ne?"."Wai daddynta ya tafi bai mata sallama ba,sai kace wata k'aramar yarinya".
Mariyama dai mamaki ya kamata ,amma sai ta aje mamakinta ta kalli meenal ta ce"Ki yi hak'uri kinji kar kanki yayi ciwo ".Haka dai Maryama tai ta ba Meenal baki har sai da taga tayi shiru sannan ta rabu da ita.

Hajiya Mariya kallan Maryama tayi ta ce"Dan Allah ko akwai yaro kusa in bashi ya amso ma ta kayan tea,da yake ita bata shan kunu ko agida".
Sallamar d'an juma da Maryama wato mahaifiyar shi taji ne yasa ta ce"Yauwa bari ga yayansu nan ya amso mata".

D'an juma cikin na tsuwar shi yayi sallama ya shiga,wani irin yarrrr yaji lokacin da idanun shi su kai mai tozali da Meenal da ke zaune ana bata hak'uri har yanzu dai tana shasshek'ar kukan.D'an juma cikin zuciyar shi ya ce"Ko sune bak'in da jiya sarki yace min anyi,amma kuwa wa In can kamar maza ne inda shi ya kirani yace min in samu d'akin kwana bak'i zasu kwana a d'akina".
Maryama wato Mahaifiyar d'an juma kallan d'an juma tayi ta ce"Yauwa dan Allah kawomana kayan tea".D'an juma kai ya siddar cikin sanyin muryar shi ya gaida hajiya Mariya sannan ya fita.Dai-dai k'ofar da zata sadashi da wajene yasake wai gowa,aiko take idon shi ya fad'a ana Meenal.Meenal da dama ta tsani kallo ta gallamai harara,aiko sai a idon Momnynta.
Chapter 7 · 0% Book details