Sashe 14
Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su mommyn Meenal sunanan zaune sun tasa daddy Meenal da ke ta faman juye-juye saboda yadda kanshi ke mai .
Su hajiya Mariya na nan zaune abokin alhaji Abba ya shigo,yana zuwa ya yima alhaji Abba aune-aunan da yakamata yayi mai,ya kalli hajiya Mariya ya ce
"Hajiya gaskiya jinin Alhaji Abba ya hau,amma babu damuwa da akwai magani da zan kawo mai yanzu,kuma gaskiya ayi k'ok'arin ganin yabar shiga damuwa,Dan shi yayi sanadin halinda yakeciki yanzu haka".
Hajiya Mariya dai godiya taimai.Shi kuma fita yayi samoma alhaji Abba magungunan da suka kamata.
Hajiya Mariya ko kama hannun Meenal da keta kuka tayi suka koma Falo suka zauna.Hajiya Mariya kallan Meenal tayi ta ce
"Meenal daddynki na cikin wata damuwa wadda ita ce tayi sanadiyar da jininshi ya hau.Alhaji yau kusan kwana goma kenan baya amsa gaisuwar daddynki Meenal,k'arshema yau yace mai baya son ya k'ara zuwa inda yake,Wanda inada tabbacin shine yayi sanadiyar da jinin daddynki ya hau.Meenal daddynki na sonki da yawa baya son kwatakwata yaganki cikin damuwa ko matsala,duk wannan yana daga cikin abinda yasa jinin shi ya hawa".
Shiru mommyn meenal tayi tana kallan Meenal kamar mai nazartarta,sannan taci gaba da cewa
"Meenal ko kinsan babu abinda ke saurin kisa kamar irin damuwar da daddynki yake ciki yanzu?,ina tsoran karmu rasa shi ,ya zamu idan ya mut...".
Kukan da Meenal ta fasa ne yasa mommyn meenal yin shiru.Hajiya Mariya ganin yadda meenal ta rud'e jin daddynta zai mutu,rungume Meenal tayi tana lallashinta ta ce"Ki yi shiru,insha Allah daddynki zai samu sauk'i,amma sauk'in nada gareki ne Meenal,duk da nima ban amince ba amma sai naga da murasa daddynki gara inyi hak'uri..".
Meenal katse momynta tayi da cewa
"Mommy ki min bayani mekesa sweet daddy adamuwa?".
Hajiya Mariya kallan Meenal tayi yadda duk ta rud'e ta k'osa taji aninda zatace.Hajiya Mariya ta ce"Meenal alhaji ne wai dole sai kinyi aure ,tom kinsan daddynki nason abinda kikeso,shine yak'i yadda dan yasan baki son aure,tom shine alhaji yake fushi dashi,tom kinsan hukuncin Wanda iyayanshi ke fushi da shi, idan ya mutu wuta zashi,shi yasa daddynki duk ya tada hankalin shi har jininshi ya hau,kuma kinajin likita yace ayi k'ok'ari abarbari yana shiga damuwa.Meenal dan Allah kije ki samu daddynki kice mai kin yadda zaki auri wanda alhaji ke so dan hankalinshi ya kwanta".
Meenal da gudu tana mai k'ara tsananta kukanta ta ruga bedroom d'in daddynta,tana zuwa ta fara buga daddynta tana janye mai hannun shi dake rik'e da kanshi, ta ce
"Daddy ka tashi karka mutu na yadda alhaji yayi min auran ..............✍️
Meenalyn daddy group, Comment d'inku yayi k'aranci.Amma......🤐🤐🤐🤐🤐🤐🤐.
📚 MEENALYN DADDY 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 19 & 20.
Meenal da gudu tana mai k'ara tsananta kukanta ta ruga bedroom d'in daddynta ,tana zuwa ta fara bubbuga daddynta tana janye mai hannu shi dake rik'e da kanshi ta ce,"Daddy dan Allah katashi karka mutu ,na yadda alhaji ya yi min auran..."Meenal ta idasa maganar tana kuka.
Daddyn meenal jin abinda Meenal ta ce,lallab'awa yayi ya tashi yana kamo hannun Meenal d'in yana bubbuga baayanta,alamun lallashi tayi shiru daga kukan da take,sannan cikin dauriya dan sosai kanshi kemai ciwo,ya ce,"Yi shiru Meenalyna,ya isa haka kibar kukan".Meenal cikin kuka ta ce,"Tom daddy dan Allah karka mutu,Allah inka mutu nima mutuwa zanyi".
Alhaji Abba lallan shi meenal yayi ya ce,"Ki yi shiru tom ai bazan mutu ba sai kwanana sun k'are".
Hajiya Mariya da shigowarta kenan,zuwa tayi ta janye meenal ta ce,"Meenalyn daddy mai nake gani haka,tom ai sai kik'aramai wani ciwan".Meenal jin haka da sauri ta goge hawayanta,tana cewa"Sweet daddy sannu".Alhaji Abba kai ya jinjina ma Meenal ,dan bayason magana,kanshi saramai yake sosai.
Hajiya Mariya lallab'a Meenal ta yi ta janyeta suka fita,dan alhaji Abba ya samu ko zaiyi bacci,dan doctor ya had'a mai da maganin bacci.
Allah yasa suna fita ko bacci ya d'auke alhaji Abba.
Hajiya Mariya shiryawa tayi ta ta tafi gidan kakan Meenal.
Bayan hajiya Mariya sun gaisa da alhaji ne ta ce"Alhaji tun safe da daddyn meenal yazo gaidaka da kyar ya koma gida yanzu haka bashi da lafiya,likita yazo ya duba shi yace jinin shi ne ya hau,alhaji dan Allah ka yi hak'uri ki rik'a amsa gaisuwar daddyn meenal,Wallahi cikin damuwa yake sosai,shine ma abinda yayi sanadin ciwan shi".Shiru alhaji yayi,sannan zuwa can ya ce,"Mariya nazaci ba Sani ba na isa da abinda Sani ya haifa,ashe bahaka bane,ni Sani zai kunyata saboda karya b'ata ma 'yar shi rai,a abinda Nina san alheri ne da Amina,soboda Wallahi yadda kuka lallata Amina ba kowana yaro zai iya zama da ita ba,amma Yaran nan ina tabbacin zaiyi hak'uri da duk shurman Amina,amma Sani agaban kakan yaran nan ya nuna shi ba zaiba wannan yaran Amina ba, harda wata k'aryar banza da wofi,wai yayi ma Amina alk'awarin ba zai mata auran dole ba".Shiru alhaji yayi kamar mai tunani sannan ya ci gaba da cewa,"Wallahi Mariya indai ni ban isa da Sani ba,tom banga amfanin gaiduwar da yakemin ba,shi yasa nace bana so,sannan shi yaron fa ba a kyauyan zai ajeta ba,shi kan shi kuna gani ba'anan yake har kokinshi ba.Mariya matuk'ar Sani ba zai aminta da maganata ba ke kanki ina dab da daina amsa gaisuwarki "Hajiya Mariya numfasawa ta yi ta ce,"Alhaji yanzu haka nazo nai in sanar da kai Meenal ta amince da auran".Hajiya Mariya ta fad'i maganar kamar zatasa kuka,dan tabbas tafi daddyn Meenal tsanar auran nan dan dai bata da yadda za tai ne ,sannan bata san daddyn meenal ya sab'a da Mahaifinsa.
Alhaji jin abinda mommyn meenal ta ce wani k'ayataccan murmushi yayi ya ce,"Nagode Mariya da wannan kunyar da kika fitar dani,duk hankalina ya tashi ina tunanin yadda zanyi da alk'awarin da na d'aukar ma yaran nan,nagode yadda kika fiddani kunyar nan kema Allah ya fidda ke kunyar duniya da lahira"Mommyn meenal cikin sanyi ta ce,"Ameen alhaji"Yanzu kije gida ,anjima zansa Issuhu ya kawoni inga jikin nashi,gobe kuma insha Allah zani garin su yaran nan in mai albishir shima".Hajiya Mariya dai jikinta duk a mace yake ,haka ta tashi tayi ma alhaji Sallama ta tafi".
Alhaji ko kamar yadda yace issu na zuwa yasa ya kawo shi gidan su Meenal.Suna zuwa Meenal kad'ai suka gani zaune a Falo da waya hannunta,alhaji kallan Meenal yayi ganin yadda ta d'auke kai kamar bata san shi ba,ya ce,"Ja'ira idan biki gaidani ba,Uwarki da Ubanki za su gaidani su".Meenal dai ko kallan alhaji ba taiba taci gaba da abinda takeyi,da akwai wata sanda hannun alhaji da yake dogarawa da ita,ita ya d'auka ya kwala ma Meenal,ya ce,"Ja'ira wato ina magana kinyi banza dani"Meenal tashi tayi tana hararar alhaji ta ce"Wai kai dan Allah alhaji mai na tare maka ne da kake naiman takurama rayuwata"."Uwaki da Ubanki kika taremin kinji ko?"Cewar alhaji.
Hajiya Mariya da tajiyo muryar alhaji da sauri ta fito dan tasan yadda meenal take cike da haushin alhaji tsab za tai mai rashin kunya.Hajiya Mariya na zuwa da fara'arta ta ce,"
Barka da zuwa alhaji,rabu da Meenal karta sama Cowan's kai".
Yajiya Mariya jagora tai ma alhaji izuwa bedroom d'in alhaji Abba.
Alhaji Abba na kwance har yanzu,alhamdulilah ya samu sauk'i bakamar d'azu ba.Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce,"Sannin ko Sani,ya jikinnaka?"Alhamdulilah naji sauk'i"Cewar daddyn meenal.
Nan dai alhaji ya gama zaman shi ya tashi ya tafi"
Washe gari alhaji suka yi sammakon tafiya layin kad'anya garinsu d'an'juma.Kasan cewar sun tafi da wuri hakan yasa sukayi isar wuri sosai.Sarki sosai yayi mamakin ganin alhaji dan alisafinsu bazasuwuce wata d'aya da tafiya ba.Sarki cikin fara'a ya tari alhaji.
Alhaji bayan ya huta sosai ya sha ruwa ya kalli Sarki ya ce," Sarki wannan tafiyar ta Abdurrahman ce ,gashi naga kamar baya kusa"."Eh aikam yau yayi sammakon shiga Funtua saro kayan shago,yanzu ba dad'ewa zakagan shi".Cewar Sarki.
Nan fa alhaji da Sarki suka cigaba da fira,suna cikin firane d'an'juma ya yi sallama ya shigo.D'an'juma da fara'ar shi ya k'arasa cikin d'akin yana mai cewa"Barka da zuwa alhaji,kai ne da sammako haka,sai kace ba daga Kaduna kake ba".Murmushi alhaji yayi ya ce,"Ni ne Abdurrahman,wannan tafiyar takace baki d'ayanta"D'an'juma jin haka k'ara gyara zama yayi sosai,alamun inajinka.
Alhaji kallan d'an'juma yayi ya ce,"Abdurrahman fad'amin yau shene kake ganin kanada damar aure?".Shiru d'an'juma yayi,dan ya zaci maganar meenal alhaji zai mai.Cikin sanyi d'an'juma ya ce," Eh,idan nasamu wadda nake so zan fidda lokacin".Murmushi alhaji yayi ya ce"Abdurrahman na amso maka auran Amina shi yasa nace wannan tafiyar takace,dan haka yanzu ina son atsaida komai in tafi ma iyayanta da albishir,yanzu dai ka turomin mahaifinka muyi magana da shi shima".
D'an'juma sumar zaune yayi dan ya kasa cewa komai ma,yarasa wane hali yake ciki,dan take sai yaji fargaba ta rufe shi.D'an'juma matsowa yayi ya kama hannun alhaji ya ce"Alhaji nagode da k'ok'ari ,Allah ya sakamaka da mafificin alkairi"."Babu komai Abdurrahman maza kai min magana da mahaifinka,dan gobe zan yi saammakon tafiya".D'an'juma tashi yayi ya tafi,cikin sanyi dan sosai kuma yakejin fargaba,wata zuciyar take cewa,"Anya kuwa bakayi kasada ba?" D'an'juma ya dad'e a tsaye yana tunanin yadda zai sanar da mahaifin shi,sannan ya ce kai gaskiya bazan iya ba,gara idan yazo yaji.D'an'juma wayar shi ya ciro ya Kira mahaifinshi ya sanar da shi Sarki na son ganin shi.Mahaifin d'an'juma sosai yayi mamaki dan babu dad'ewa yaje sun gaisa,amma kuma sai ya kauda mamkin shi ya ce"D'an'juma yanzu yake son ganina d'in"."Eh yanzu ya ce".