← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 21

Sashe 3

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Mariya ta dad'e konce tana juyi tana tunanin ta yadda zata b'ulloma lamarin nasu,dan awannan karan ta d'auki aniyar yak'i da Meenal da daddynta.Washe gari mahaifiyar meenal haka ta tashi da wuri kamar yadda ta saba tashi ta shirya musu abin breakfast,tana nan zaune Alhaji Abba ya fito dan yau k'in shiga part d'in shi tayi dan ya san fushin da gaske take yi da shi.Alhaji Abba ko da fara'ar shi ya k'araso inda hajiya Mariya take,yana cewa"Wato yau dan ana fushi dani shine aka k'i tadani ko?".Murmushi Mommy Meenal tayi tana mai cewa"A'a daddyn meenal nikam bana fushi dake makara nayi nima".

Alhaji Abba zama yayi yana mai cewa"Ina meenalyn daddy fa?".
"Kasan indai ba Exam gareta ba sai an tadata ".
Alhaji Abba tashi yayi ya nufi bedroom d'in Meenal,lokacin da Alhaji Abba ya shiga kwance ya sameta sai sharar baccinta take.Ahankali Alhaji Abba ya fara bubbuga Meenal yana kiran sunanta.
meenal bud'e idonta tayi tana mai sakin murmushi wa daddyn nata.
Alhaji Abba kallan Meenal yayi ya ce"Meenalyn daddy tashi ki yi wanka ki yi breakfast ".meenal tashi tayi batare da ta tanka ba tana mai shigewa toilet .
Alhaji Abba ganin meenal ta tashi ,shima fita yayi"

Meenal cikin sauri ta shirya ta fita dan ta kusa late.Zaune ta iske daddynta na jiranta,tana zuwa sauri-sauri suka yi breakfast d'in ,dan dukkan su sunyi late"

Alhaji Abba kamar yadda ya saba sai da ya kai meenal cikin makarantar su sannan ya tafi private hospital d'in da yake aiki .
Hajiya Mariya ko ita ma kusan tare suka fita,dan tana son ta fara biyawa gidan kakannin meenal kafin ta shiga school d'in da take teaching"

Hajiya Mariya zaune gaban Alhaji Abdullahi ,wato kakan meenal kenan,mahaifin Alhaji Abba .
kakan Meenal da kallo d'aya za kai mai kasan datijon ya kwana biyu dan kanshi gaba d'aya farin gashi ne,sai dai da k'arfin shi sosai.
Alhaji Abdullahi ,wansa yawancin mutane da kuma sukansu suke Kira da Alhaji,da fara'arshi ya tari hajiya Mariya wato mahaifiyar meenal ,yana cewa" Mariya tunda naganki da wuri haka nasan ba gaidani akazo yi ba "Hajiya Mariya dariya tayi,ta ce"Ina kwana Alhaji,ya k'arfin jikin" "Jiki alhamdulillah"cewar kakan meenal.
Hajiya Mariya k'ara gyara zama tayi sannan ta ce"Alhaji dama wallahi akan meenal ne,kamar yadda dai kasani bani da iko akan meenal,ban'isa insata ba ban'isa in hanata ba,tom har yanzu ahaka muke.Wato abinda kedamuna meenal banda cin abinci da wankanta babu abinda ta'iya,akoda yau she ina nuna ma mahaifinta ita macece gidan wani zata,amma wallahi ita da daddynta duk ranar da na furta haka ma sai munyi ba dad'i,shine nazo nasan kai in kayi mai magana zaiji kace mai dole meenal ta rik'a tayani aikin gida ko asamu ta iya wani abun daga cikin aikin gida"Shiru hajiya Mariya ta yi ta d'an numfasa sannan ta ce"Tom Alhaji wannan ita ce buk'atata dan Allah".

Kakan meenal tashi ya yi daga shingid'an da yake ya ce"Wai Mariya kina nufin Amina bata iya komai ba na aikin ku mata?"."Wallahi Alhaji bata iya komai ba,shara wanan, Allah tunda meenal ta isa hankakinta banta b'a ganin tayita ba da idona ba,tun abin baya damuna nikam yanzu har yafara damuna".
"To shi Sani in banda abin shi haka zai d'auki "'yar ya kaita gidan aure bata iya komai ba,tom ki barshi dani ,bari Sule yazo zansa ya kiramin shi".
Hajiya Mariya godiya ta yi ma sirikinnata sosai sannan ta tashi ta tafi"

Sule mai kula da Alhaji wato kakan Meenal yana zuwa Alhaji ya sashi ya kira mai Alhaji Abba awaya ya ce daga ya tashi aiki ya biyo Alhaji nason ganin shi".

Aiko haka akayi Alhaji Abba na tashi aiki ya je Kiran Mahaifinnasa, dama kuma dai kullum sai ya laik'a Mahaifinasa.Bayan sungaisa ne Mahaifin Meenal ya ce"Alhaji gani ance kana son ganina"
"Eh Sani ina son ganinka,d'azu Mariya tazo nan ta kawomin k'ararka kai da Meenal,taya zaka ce Meenal bazata rik'ataya Mahaifiyarta aiki ba,bakasan tana da hak'i akanta ba ne?,dan haka karka kuskura kajama yarinyarka fushin Allah,karik'a barinta tanayin aiki,kamar yadda mahaifiyarta tace ita macece nan gaba gidan wani zata,dan haka daga yau duk wani aiki su rik'ayi tare,idan ma ta kama ta hak'ura da makaratun ne tom ta hakura ta zauna ta taya Mahaifiyarta aiki, itama ta iya".
Mahaifin Meenal wato Alhaji Abba kallan Mahaifin nasa yayi ya ce"Alhaji meenal fa yarinya ce ,taya za'ace ta had'a karatu da aiki,bazata juri aiki irin wannan ba,inda ba sabawa tayiba.Sannan tunda Mariya tayi min maganar zata takatar da masuyi mata aiki nahanata,gudin haka,amma saboda wata hujja tata ta banza da ta tsiro da ita tak'iji ,shine yanzu aiki yayi mata yawa zata d'orama Meenal".
kakan Meenal da tunda Abban meenal ya fara magana yake kallan shi,har ya kai k'arshe,cikin sanyin shi,dan shi ko fad'a zaiyi cikin sanyi yake abinsa,ya ce"Sani dole meenal ta yi aikin gida kamar yadda mahaifiyarta ta buk'ata ,zaka iya tafiya".
Alhaji Abba ya dad'e bai iya k'ara cewa komai ba sannan yayi k'arfin halin cewa"Shikenan Alhaji zatayi,zan tafi babu abinda kake buk'ata?"."Babu Allah yayi maka albarka "cewar Alhaji wato kakan Meenal"

"Ameen"Mahaifin Meenal ya ce ya tafi.

Sosai ran alhaji Abba ya b'ace da abinda hajiya Mariya ta yi mai,yana shiga gida hajiya Mariya ta lura da yanayin shi tasan Alhaji ya fad'a mishi,dama kuma tunda taji shi shiru ta yi tunanin hakan.
Meenal ko da ke zaune tana aikin buga game awayarta ,aje wayar tayi tana mai yin welcoming din daddynta.Alhaji Abba hannun meenal ya kama suka zauna.
Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce"Barka da dawowa daddyn meenal""Uhm"Alhaji Abba ya iya ce mata kawai.
Meenal ma ganin haka tasan yau an tab'a daddynta hakan yasa cikin sanyi ta ce." Daddyna waya b'atama rai?".Meenal tayi maganar tana kamo fuskar shi abin gunnin mamaki.
Alhaji Abba Mahaifiyar meenal ya nuna ma meenal ya ce"Kin ganta meenalyn daddy bata son farincikina".Meenal cikin sanyi ta ce"Daddy mai tayi ma?".Alhaji Abba murmushin takaici yayi sannan ya ce"Meenal ta had'ani da Alhaji wai sai dai ki rik'a tayata aiki"."Wallahi daddy bazanyi b...".Alhaji Abba saurin rufe bakin meenal yayi dan karta idasa fad'in abinda take cewa,ya ce" Yi hak'uri Meenalyn daddy karki rantse kinji,ki yi hakuri kina kallon yadda take aikin,ahakama zaki iya,basai kin amsa kinyi ba ".Meenal kuka tasa tana cewa"Daddy inje school in dawo inyi aiki Allah bazan iya ba ni kam bazanyi ba". Alhaji Abba hannun meenal ya kamo ya shigar da ita side d'in sa ,cikin falonsa suka zauna ,cikin lalla shi ya ce"Meenalyn daddy tausayin daddynki zakiji ki yi badan Mommynki ba,kinga Alhaji zai iya fushi dani".Bud'ar bakin meenal sai cewa ta yi"Yo daddy ya dad'e bai yi ba,ba shi ya sani b..." .Alhaji Abba rufe bakin meenal ya yi ya ce"Meenalyn daddy Mahaifina ne fa,ni dai dan Allah ki tai maka kirik'a ganin yadda ake girkin zanma rik'a biyanki ba kyauta ba zaki yi".meenal dai turo baki ta yi bata ce komai ba,haka Alhaji Abba ya yi ta rok'on meenal daga k'arshe dai sai da ya yi kamar zaiyi kuka ta yadda,amma fa ta d'auki matakan yak'i da Mommynta dan acewarta bata sonta .Niko abin ta kaicima ya ke ban dan tab'arar tayi yawa"

.

Ranar dai abincin da Hajiya Mariya ta yi daga Alhaji Abba har meenal babu wanda ya kallai dan dukkan su fushi suke da ita.Tsaddan restaurant Daddyn Meenal ya kaisu sukaci abinci"

Washe gari takama Weekend ,hajiya Mariya da wuri taje ta tada Meenal,Meenal da ke kan duniyar bacci kallan Hajiya Mariya ta yi tana turo baki ta ce"Lafiya".",Tashi zakiyi muje kifara gani inda kice bazaki ba,naji ki kallama ya wadatar "cewar Mahaifiyar meenal. Meenal turo baki tayi tana k'unk'u nai ta ce" Tom kije ganinan zuwa"."Tashi zakiyi muje ".

Meenal sakkowa tayi tana mai bin bayan hajiya Mariya tana mai goge hawayan da ya fara zubar mata.

Hajiya Mariya cigaba tayi da gyaran falon da tafara ta tuna bata tada Meenal ba.Hajiya Mariya tanayi tana surutu ,kinga idan kika fara share duster d'in sanna sai ki share ki goge,duk abinda hajiya Mariya za ta yi tanayi tana magana,irin dai na masu koyama mutum abu.Meenal ko kallanta kawai take da na goge hawayan da ke zubar mata akai-akai. suna gamawa hajiya Mariya ta kalli meenal da yanzu tabar kukan sai dai baki da ta turo ta ce"Yauwa Meenalyn daddy ba gashi har mun gamaba,yanzu saura mana mu had'a breakfast".

Nan ma dai haka meenal ta bi Mommynta tana turo baki,ahaka dai suka dama kunun gyad'ar da suka dama ,ana cikin dama kunun ne Alhaji Abba ya shigo kitchen d'in,cikin fad'ad'a murmushin shi ya ce"Sannu da k'ok'ari meenalyn daddy".meenal turo baki tayi bata tanka ba.
Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi ta ce"Barka da safiya daddyn meenal".
maimakon alhaji Abba ya amsa hannun meenal ya kamo ya ce"Tom aikin ya isa haka muje ki huta".

Meenal hannun daddynta ta rik'e suka tafi suka bar Hajiya Mariya nan ,hajiya Mariya da kallo kawai da bisu taci gaba da aikinta.Alhaji Abba kallan Meenal yayi ya ce"Jeki shirya meenalyna mu je muyi breakfast bama k'aracin abincinta sai dai taci ita kad'ai ki rabu da ita karma ki k'ara b'ata ranki ko kiyi kuka ".Meenal kallan daddynta ta yi tana goge hawayan jin dad'in son da daddynnata ke mata ta ce"Daddy me yasa mommy da tafi sona yanzu ta ke min haka ne?".Alhaji Abba goge ma meenal hawayan da ke zubar mata ya yi ya ce"Ki yi hak'uri kinji meenalyna ni bagani ba kuma ina sonki,kibarni da ita zanyi maganinta kwanannan,maza kije ki shirya muje muyi breakfast".

Meenal cikin jin dad'in daddynta yace zaiyi maganin takurawar da Mommynta ke mata ta shirya da wuri.Haka suka zo suka wuce hajiya Mariya da ke zaune daga gani jiran fitowar su take suyi break tare,amma sai ta ga sun fita.

Alhaji Abba restaurant d'in jiya da ya kai Meenal su kai breakfast,can ya kaita yau ma,sai da suka yi breakfast d'insu sannan suka koma gida "
Chapter 3 · 0% Book details