← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BAYAN SATI D'AYA.
Gaba d'aya satin nan haka hajiya Mariya ta yi shi duk ba dad'i dan tagaji da fushin da Meenal da daddynta su ke yi da ita,gashi aikin ma Meenal ba wai yi take ba sai dai tai mata tsaye akai dan ita bata ce tanama fahimtar abinda take koya mata ba.
Fushin da Daddyn meenal ya ke yi da hajiya Mariya sosai abin ya fara damunta hakan yasa yau da daddare bayan meenal sun rabu da daddynta ta kwanta ,hajiya Mariya ta turo d'akin Meenal d'in ta shiga,kamar ko yadda ta zata zaune ta iske Meenal d'in tana game awayarta.
Meenal najin sallamar hajiya Mariya ,kamar bazata amsa ba ,sai kuma ta amsa ciki-ciki,amma ko tad'aga kai ta kalleta.
Hajiya Mariya amshe wayar hannun Meenal ta yi.meenal turo baki tayi sannan ta juya zata kwanta,hajiya Mariya da sauri ta rik'o Meenal tana cewa"Haba meenaly daddy da mommynki kike fushi?,dan nace ki koyi aikin gida ne kike fushi dani keda Abbanki ko,tom indai hakane kisha zamanki daga yau ni kad'ai zan rik'a aikina shikenan ko ?".
Meenal turo baki tayi ta ce"Tom ba ke bace yanzu kin canza".Murmushi hajiya Mariya tayi ta ce"Meenal ba canzawa nayi ba bakudai fahimtan bane keda daddynki shi yasa"."Ni kam Mommy indai kina son mushirya sai dai ki dawo kamar da ".Shiru hajiya Mariya ta yi sannan ta ce"Tom meenalyna na daina ,mun shirya ko?".Meenal rungume hajiya Mariya ta yi ta ce"Yauwa mommyna har naji dad'i".
Murmushi hajiya Mariya ta yi ,ta ce"Meenal kenan,ke kikasa daddynki ya yi fushi dani ko?"."A'a mommy Allah babu ruwana ".

Murmushi hajiya Mariya ta yi ta ce" Tom ki aje game d'in ki kwanta ki yi bacci".Hajiya Mariya nakaiwa haka ta tashi tajama ma Meenal k'ofa,ta nufi bedroom d'in Alhaji Abba,koda taje ya rufe k'ofar shi hakan yasa sai da ta bubbuga Alhaji Abba da har bacci ya fara d'aukar shi ya ce"Waye"yana sane yace haka dan yasan ba meenal ba ce.
Hajiya Mariya kamar karta tanka dan tasan yana sane da ita ce,amma sai ta daure ta ce"Daddyn Meenal ka bud'e ni ce" Alhaji Abba tashi yayi ya bud'e ,yana kallan hajiya Mariya kallan har yanzu fa ina fushi dake.Hajiya Mariya kutsawa tayi ta shiga .Alhaji Abba kallanta yayi ya ce"Zan kwanta ne lafiya?".Shiru Hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Ka zauna mana,magana zamuyi"Alhaji Abba zama yayi ya ce"Inajinki?".
Hajiya Mariya cikin siririyar muryarta ta fara magana kamar haka"Yanzu daddyn meenal fushi kake dani dan nasa meenal aiki?,Shikenan insha Allah daga yau bazan kuma sata ba".Alhaji Abba cikin d'aga murya alamun yaji zafin abinda mommyn meenal ta yi ya ce"Eh Mommyn meenal fushi nake da ke kamar yadda kika ce,akan me na d'aukar miki masu aiki ki koresu kice ke sai dai meenal ce zata ta ya ki,tom da me zataji da karatun da takeyi koko da aikin gida zataji!?".Numfasawa mommyn Meenal tayi sannan ta ce"Shikenan daddyn meenal ai ya wuce dan Allah kayi hak'uri insha Allah hakama ba zai sake faruwa ba duk yadda kace haka za'ai".Murmushi Alhaji Abba yayi ya ce"Yauwa,bawai bana son Meenal ta tayaki aiki bane,a'a nafi son sai ta gama karatunta kar abin yayi mata yawa".Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Tace tom ai shikena,ni kunsa duk na rame kai fushi meenal fushi.Memakon ko kaine kaji tausaina,amma kaziga 'yarka kuka had'emin kai kuka sani gaba,tom nadai janye".
Dariya sosai Alhaji Abba yayi ya ce "Yauwa mommyn meenalyna koke fa,amma nima fa naga kamar kinrane da gaske ,kamarma hadda k'ashin wuya mugani" Alhaji Abba ya idasa maganar yana jawo mommyn meenal.Hajiya Mariya buge mai hannu tayi ta ce"Ni rabu dani tashi zanyi in tafi "Hajiya Mariya ta fad'i maganar tana tashi zata tafi.Alhaji Abba jawota yayi ta fad'o kanshi ya ce"Ai inkinga kin fita nan tom kin ba Abban meenal gamsassan hak'uri dan Wanda kikaban yayi kad'an "Alhaji Abba na fad'in haka ya had'e bakin shi da na Hajiya Mariya..............✍️

Yadda kike tunanin labarin ba haka yake ba sister bini ahankali😇😇😇

kada ku manta da akwai banous da zan saki , masu Comment ne kad'ai zasu samai

Shere & Comment please

📚 MEENALYN DADDY 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*
NA
Fadila Sani Bakori.

Page 5&6.

Washe gari ,hajiya Mariya da wuri ta tashi kamar yadda ta saba tashi ta shirya komai ta d'ora musu abin breakfast.Lokacin da Meenal da daddynta suka tashi hajiya Mariya ta kammala komai kamar yadda ta saba.
Yau cikin fira da tsokana Meenal suka yi breakfast da daddynta da mommynta.Sosai hajiya Mariya taji dad'in hakan,amma satin nan gaba d'aya da suka daina cin abincinta firama suka bar zama suy da ita'dan hatta kallo Meenal a Falon daddynta take zuwa tayi.Bayan sun gama karyawa Alhaji Abba ya d'auki Meenal ya direta a school d'in da take karatu sannan shima ya tafi wajan aiki"

ASALIN LABARIN.
Alhaji Abba shine d'aya d'aya tilo wajan mahaifin shi,hakan yasa mahaifin alhaji Baba wato kakan meenal,ya ba Alhaji Abba gata sosai,alhaji Abba na matakin k'arshe na karatu Allah yayi ma mahaifiyar shi rasuwa.
Tunda Mahaifiyar Alhaji Abba ta rasu hankalin Alhaji wato kakan Meenal ya koma akan Alhaji Abba yayi aure, dan dama tun da ran mahaifiyar shi taso haka Allah bai yi ba. Babu maganar da Alhaji wato kakan meenal bayi ma Alhaji Abba ba akan aure amma yak'i,hakan yasa sai ya fara bincikin abokan shi ko sun sa budurwar shi amma abin mamaki sai suka sanar da shi bashi da budurwa,dan shi alakacin babu abinda yakeso kamar karatun shi,gani yake yin budurwa kamar b'ata lokaci ne,hakan yasa ya maida hankalin shi sosai akaratu,har ya kammala ya samu aiki,amma babu maganar aure aran shi.
Atak'aice dai Alhaji wato kakan meenal ya sha fama sosai kafin mahaifin meenal yazo mai da maganar auran mahaifiyar meenal itama lokacin ansha karatu.Cikin k'ank'anin lokaci aka tsaidar auran su akayi,za'a'iya Kiran auran da auran tazurai.Mahaifin meenal ana d'aura auran shi da hajiya Mariya bai yadda ya kusanceta ba sai da ya kaita asibitin da ya ke aiki akai mata tsarin family planing,acewar shi sai sun mori k'uruciyarsu sannan ko zasu haihu.
Atak'aice dai ,sai da sukai shekara tara babu haihu,daga nan suka fara bin asibitoci ,amma za'a'iya cewa ba adace ba.Nan fa abin ya fara damun su. Suna shekara ta goma da aure Allah ya ba hajiya Mariya ciki.kalar munar da sukai da cikin nan ba'acewa komai.Nan da suka fara tarairayar cikin .
Wayyo Allah ranar da hajiya Mariya ta haihu sai da alhaji Abba yayi kukan dad'i ,tun daga nan fa ya d'auki son duniya ya d'orama babyn ,ranar suna taci sunan mahaifiyar shi wato Amina,sukarik'a mata lak'abi da Meenal ,alhaji Abba kuma yana kiranta da meenalyn daddy kamar wasa sunan ya bita.
Tsabar son da alhaji Abba da hajiya Mariya suke nuna ma meenal yasa duk abinda tayi basa ganin laifinta,gashi tun daga kanta hajiya mariya bata kara koda b'atan wata ba.Hakan yasa meenal ta taso a sangarce, babu mai kwab'amata,tom garama hajiya Mariya dake shiga cikin mutane tana ganin yadda iyaye ke iko da yaransu takanji dama ita,dan ita kome zatai ma Meenal bata isaba tasa ta daina abinda takeyi,hakan sai ya fara damunta,tom shine fa yanzu ta fara k'ok'arin gyarawa amma ina abin ya ci tura.
Wannan shine dalikin da Mahaifin Meenal ya d'auki son duniya ya d'aura ma Meenal ganin ita kad'ai gareshi,gashi yasha wuya sosai kafin susameta .Wannan kenan"

Tunda hajiya Mariya tabar sa Meenal aiki suka dawo kamar yadda suke da Meenal da daddynta,suka dawo kamar da.
Yau ta kama Weekend Alhaji Abba zaune suke shida iyalinshi suna fira Kira ya shigo wayar shi,Alhaji Abba shiru yayi yana sauraran Kiran da aka ce mahaifin shi na mai,cikin fargamar zarkin Kiran nashi da ya yi ya ce"Okey,gani nan zuwa yanzu".
Dama Alhaji Abba da shirinsa na fita,hakan yasa ya tashi ya nufi gidan Mahaifinsa da baida nisa da gidan shi.
Chapter 4 · 0% Book details