← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 21

Sashe 2

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin k'arfe takwai na dare(8:00PM) Alhaji Abba ya shigo gida kamar yadda ya saba da wowa kusan kulkum.
Meenal zau ne ta ke kan caution ,ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ,ta yi kwalliyar tar bar daddynta kamar yadda ta saba kullum,haka zata zo falon ta zauna tana jiran shigowar daddynta.Aiko tana jin sallamar shi ta ta shi da gudu ta rungume daddynnata,tana mai amsar jakar hannun shi,sannan cikin sanyin muryarta ta ce.
"Welcome daddy".
Alhaji Abba cikin k'aunar 'yar tashi ya ce.
"Ina ta sauri kar inyi ma Meenalyn daddy laifi".
"Ai daddy yau da ka k'ara lokaci da bazan kulaka ba".cewar Meenal tana mai yima daddyn nata jagoranci izuwa bedroom d'in shi.
Mahaifiyar Meenal ko da fitowarta daga kitchen kenan, ta k'araso da fara'arta irin ta tarbar mai gida d'in nan ta ce.
"Oyoyo daddyn Meenal barka da dawowa"

Alhaji Abba Yana mai ci gaba da tafiya ya ce.
"Yauwa Mommyn Meenalyn daddy".

Meenal ko na rik'e da jakar daddynta da ta amsa har i'zuwa bedroom d'in shi.Sai da ta aje jakar sannan ta fita tana mai cewa .
"Tom Daddy ka fito yanzu fa kar Ulcer ta kamain kai".
Murmushi Alhaji Abba yayi ,batare da ya tankaba ya shi ge toilet"

Meenal ko na fita darning space ta nufa ,ta zauna tana danna wayarta tana jiran fitowar daddyn ta.
Meenal na nan zaune Alhaji Abba ya fito shida Mommyn Meenal.
Bayan Alhaji Abba ya zauna ne,Meenal ta ja plate d'in daddyn ta ta mik'a mai itama taci gaba tacin nata.
Hajiya Mariya Mahaifiyar Meenal kallan Meenal tayi ta ce.
"Wato Meenal ke kullum bakimin ta ido ko?,sai ki zuba ma daddynki kema ki zuba ni ina kallanku ni da nai girk...".
Alhaji Abba wuf yayi ya ce.
"Aikin ai sai yayi mata yawa,ni bari in zuba miki".

Meenala dai tanaji bata tankaba, Daddynta ya zuba Mommynta abincin.
Bayan Alhaji Abba ya gama cin abincin ne,Mahaifiyar Meenal ta kalle shi ta ce.
"Daddy Meenal na kawoma k'arar Meenal?".
Alhaji Abba kallan Mahaifiyar Meenal ya yi ya ce.
"To me kuma Meenalyn daddy tayi?".

Mahaifiyar Meenal d'aure fuska tayi,alamun maganar da za tai babu wasa,dan ta san Daddyn Meenal zai iya d'aukar maganar da wasa.Mahaifiyar Meenal kallan Alhaji Abba ta kuma yi sannan ta ce.
"Daddyn Meenal,dama akan maganar rashin yin aikin Meenal ne,nifa abinda nake nuna maka Meenal macece ba zai yuwu ba,ace kamar Meenal batasan ta d'auki d'auki tsintsiya ba tayi shara,bare kuma ayi maganar mopping, tom gaskiya nikam nagaji daga yau ga Meenal nan a gabanka koda falo ne ta rik'a gyarawa ,ahankali-ahankali watarana zata iya".
Alhaji Abba tunda Mahaifiyar Meenal ta fara magana yake kallanta,har ta kai k'arshe, ajiyar zuciya ya sauke sannan,ya kalli Meenal da ta turo baki, murmushi Alhaji Abba yayi sannan ya ce.
"Meenalyn daddy kinji abinda mommynki ta ce ko?" .
Meenal turo bakinta ta kuma yi,kamar ba za tai magana ba sannan ta ce.
"Tom Daddy waya ce ta k'i samun mai tayata aiki idan aiki ne yayi mata yawa".
Meenal ta idasa maganar tana mai ci gaba ga game d'in da take yi a wayarta"

Alhaji Abba kallan Mommyn Meenal yayi ya ce.
"Tom kinji".
Mahaifiyar Meenal cikin kwantar da kai dan daddyn Meenal ya fahinceta dan tasan idai tace da tsiya za tai tom ba zai fa yuwu ba,hakan yasa cikin kwantar da kai ta ce.
"Daddyn Meenal kafa duba lamarin nan ina teaching ,kullum sai sha biyu nake da wowa gidan nan,kuma ace kamar Meenal ba zata iya kamamin komai ba,duk bama haka ba,ni aikin gidan nan bawai ya gagaran bane,kawai dai ina duba rashin dacewar ace mukai Meenal gidan miji mata iya komai b....".

Kukan da Meenal ta fara ne tana buga k'afa abin gunin mamaki,kamar wata 'yar 4 years, tana cewa.
"Daddy kaji ko ta fara ko" .
Alhaji Abba tashi yayi Yana kamo hannun Meenal ya ce.
"Tashi mu bar mata wajan dama abinda take so kenan taga tasaki kuka".
mommyn Meenal kuwa da ranta ya b'aci ,duk da indai rashin isa da Meenal ne dama saba,sai dai aduk lokacin da hakan ta faru ranta kan b'ac.Mommyn Meenal sai dai ta bisu da ido"

Alhaji Abba ko har bedroom d'in Meenal ya kaita ,ya zaunar da ita bakin gadonta,sannan yasa hannu yana goge mata hawayanta ya ce.
"Meenalyn daddy ki yi shiru kinji ki goge hawayanki,babu bai saki aiki,wa yace ta kori masu ta yata aiki saboda wata hujjatata ta banza da wofi.ki yi shiru kinji meenalyn daddy kar ki yi ciwan kai".
Meenal da har yanzu kuka ta ke,kallan Alhaji Abba tayi ta ce.
"Daddy nifa badan ta ce inyi aiki bane nake kuka,kanaji cewa tayi wai akaini d'akin miji,bacin nace ta bar cemin haka".

"Yi hak'uri Meenalina batzata K'ara ba,d'akin miji kuma naga mai kaiki har sai ranar da kikai ra'ayin kanki sannan ko?".
Kai Meenal ta d'aga ta ce ,
"Tom ka kirata kace mata karta k'ara cemin haka"

Alhaji Abba wayar shi ya ciro ya Kira Mommyn Meenal.Tana d'agawa ya ce.
"Ki sameni a bedroom d'in Meenal".
Yana kaiwa haka ya kashe wayar"

Mahaifiyar Meenal ko da tana zaune inda sukabarta tashi tayi tana mai addu'ar Allah yasa Meenal ta amince zata rik'a yin aikin ne".

Da sallama Mommyn Meenal ta shiga bedroom d'in.
Alhaji Abba ne ya amsa mata Amma Meenal ko kallanta batayi ba dan fushi take da mahaifiyartata.
Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi alamun inajinka.
Alhaji Abba gyara zama yayi yana Kara rik'e hanun Meenal ya ce.
"Mommyn Meenal wai me yasa ne idan muka fara magana d'aya dake mun dinka nanatata kenan bazamu barta ba?,Me yasa bazaki guji duk abinda kika san Meenal bataso ba?,So nawa ina ce miki duk wata magana da ta shafi aure ki bar furtata akan Meenal ?,inda yarinyar nan ta nuna miki bataso,tom wannan shine magana ta k'arshe kar ki Kuma dan ganta min yarinya da duk wani abu da kika san bataso" .
Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba kawai tayi bata iya tankamai ba,dan idan ma tace zata tanka tasan kanta zata jawoma b'acin rai gara tayi shiru"

Alhaji Abba kuma hannun Meenal dake cikin hannun shi ya murza ya ce.
"Ki yi hak'uri kinji meenalyn daddy kinji na fad'a mata bazata Kuma ba".
Meenal gurza ido ta fara alamun za tai kuka ta ce.
"Daddy ai banji ta ce bazata Kuma ba".

Alhaji Abba kallan Hajiya Mariya ya yi ya ce.
"Hajiya Mariya wai me yasa kike haka ne,shikenan ke kinfiso kita ganin yarinyar nan tana zubba hawayanta, dan Allah ki yi mata maganar bazaki k'araba dan hankalinta ya kwanta ".

Mahaifiyar Meenal da ta fara gajiya da lamarin Meenal kallan Alhaji Abba tayi,ta ce.
"Daddy Meenal taya Meenal tana mace baliga ace bazan mata maganar aure b...".
Tsawar da mahaifin Meenal yayi ma hajiya Mariya ce yasa tayi shiru".
Meenal ko ci gaba da bubbuga k'afa tayi tana cewa.
"Ka ji ko daddy bazata bari ba ko!".
Alhaji Abba cikin b'acin rai ya huna ma hajiya mariya hanya alamun ta fita.
Hajiya Mariya tashi tayi itama cikin alamun ranta ya b'ace ta fita,tana mai jan k'ofar d'akin Meenal d'in da k'arfi"

Bayan fitar hajiya Mariya ne,Alhaji Abba cikin lallashi ya ce.
"Ki yi shiru kinji meenalyn daddy,aure ai ba farillah ba ne,bare ace dole sai kinyi shi,idan ma bakisan yi ba bu komai ki yi shiru, da take maganar aure-aure waye mahaifinki?".
Meenal nuna Alhaji Abba tayi tana goge hawayanta .
Alhaji Abba kuma yaci gaba da cewa.
"Tom kin gani nine me yi miki auran dan haka kima kwantar da hankalinki ,ita kuma kibarni da ita zata san ta sa Meenalyn daddy kuka".
Haka Alhaji Abba yi ta allashin Meenal yana nan zaune har sai da yaga tayi bacci sannan ya tashi ya fita..........✍️

Meenalyn daddy karki gaggawa Sister ki bini ahankali har in kaiki inda nake son kaiki,salon shi da ban ne daga cikin litattafan marubuciyar.

idan kin karanta sister ki, daure ki comment dan ki kasance d'aya daga cikin wa'inda zasu samu banus d'in da zan saki a littafin nan,alk'awari ne insha Allah kuma zan cika.
Share & comment pls

📚MEENALYN DADDY📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Na
Fadila Sani Bakori.

Page 3&4

Haka Alhaji Abba ya yi ta lallashin meenal yana nan zaune har sai da yaga tayi bacci sannan ya tashi ya fita. bedroom d'in hajiya Mariya ya shiga.lokacin hajiya Mariya har ta kwanta,jin sallamar Alhaji Abba ce duk da ahankali yayi sallamar ya sa ta tashi.
Alhaji Abba ya dad'e zaune bai tanka ba,dan hajiya Mariya har shirun ya isheta,jin shirun yayi yawa ne yasa ta ce.
"Daddyn Meenal lafiya kuwa?".
Alhaji Abba kallan hajiya Mariya ya yi ,nan ma kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce.
"Mommyn Meenal inaso zanmiki magana ta farko da k'arshe daga yau karki kuma yadda ki zama sanadin kukan Meenal,idan bahaka ba zamu samu sab'ani tsakanina da ke!".
Hajiya Mariya tashi tayi ta zauna tana kallan Alhaji Abba,sannan cikin nuna fushinta ta ce.
"Daddyn Meenal naji insha Allah daga yau bazan sake yi ma Meeenal maganar da ta danganci aure ba kamar yadda kace insha Allah,amma maganar Meenal ta tayani aiki agidan nan bazan tab'a janyewa ba,dole Meenal tayi aiki agidan nan".Hajiya Mariya ta'idasa maganar cikin b'acin rai.
Alhaji Abba tashi yayi zai fita,har ya kai bakin k'ofar da zata sata shi da falo ya juyo yana kallan hajiya Mariya ya ce.
"Wallahi kinji na rantse indai tai makon aiki kike so sai dai ki samu 'yar aiki,amma ba dai Meenal ba".Alhaji Abba na kai haka ya ja k'ofar hajiya Mariya da k'arfi ya fita"
Chapter 2 · 0% Book details