← Book details Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 21

Sashe 12

Meenalyn Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari,d'an juma yana d'akin shi da ke gidan Sarki,bayan ya kai ma su sarki abin Karin kumallo bayan sun karya ne,yaga shigar alhaji woto kakan Meenal ban d'aki.D'an juma d'akin sarki kakan shi ya shiga,zama yayi kusa da sarki ya ce"Sarki wai ya kake da alhajin nan ne?".
Sarki murmushi yayi ya ce"Abdurrahman Malam Abdullahi,a nan garin mahaifin shi ya kawo shi karatun allo,tun da aka kawo sai tamu tazo d'aya muka k'ula abota mai k'arfi dan so dadama nike biyamai alllan shi saboda na wuce shi akaratu.Abdullahi ya yi nisa akaratu sosai ya tafi kaduna ganin gida,tom dama muna karatu da shi yana yawan sanar da ni ba da son mahaifiyar shi yake karatun allon nan ba,ita fati son yayi agabanta,tom tun daga zuwannan ne dai bai koma ba.Sai dai duk da haka alak'armu na nan dan duk lokacin da ya samu dama yana zuwa nan,kaji alak'armu da shi abota ce,kuma sai shi yama fi ni rik'e amanar abotar,inda ni ban tab'a zuwa wajan shi ba shike zuwa wajena.Kaji alak'ata da shi".Shiru d'an juma yayi sannan ya ce"Tom naga kana ma yarinyar nan addu'a me ke damunta?"."Irin lallurarka ke damunta,yarinya kamar wannan ace bata son aure ,batama son ai mata maganar auran,kamar kai agari".Cewar Sarki.
Dan juma murmushi yayi ya ce" Sarki ni kam daga yau kafara lissafi dan na samu matar aure".Allah sarki sarki da babu abinda yake son gani kamar auran d'an juma cikin tsantsar farin ciki ya ce"Alhamdulilah,Allah ya amshi rok'on mu,Abdurrahman ina yarinyar take?" D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Ni ka d'ai ke sonta sarki ita bata sona,ni kuma ita kad'ai na tab'ajin sonta araina,har nakanji idan tak'ini bazan yi aure b..." .Sarki da sauri ya rufe bakin d'an juma ya ce"Haba Abdurrahman wannan wata irin magana ce,in dai ba sokake kasani adamuwa ba,karka sake furta kallmar baza kai aure ba dan Allah,yarinyar kuma insha Alllah zata soka,ko ko ita tace bata sonka da bakinta?".
Kai d'an juma ya girgiza ya ce"Ina fargabar sanar da ita ina sonta,dan bana tunanin zata amince min"."Shurman banza kenan,waya fad'ama namiji na karaya wajan furta so,ai wanna mace aka sani ba namiji ba,ka cire fargabar komai ka tun kareta kai tsaye, insha Allah zata soka,ka cire fargaba ,da rashin tayi akan bar arha" .
D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Ka yi min addu'a ta soni Allah idan tak'ini haka zan ci gaba da zamana bazanyi aure b...".Sarki da sauri ya k'ara rufe bakin d'an juma ya ce"Abdurrahman kabar furta kallamar nan, dan wata tak'ika sai ka ce baza kai aure ba,idan fa Allah bai tsara aure tsakanin ku da ita ba fa?,shikenan ba za kai aure ba,dan Allah kabar furtawa ,ganin auranka shine burina .Ayanzu haka babu abinda nake fatan Allah ya k'aramin tsawan rai in gani kamar matarka, Abdurrahman dan Allah kabar furta kallamar nan mai fad'ar min daga ba".
D'an juma ganin yadda sarki ya shiga damuwa,yasa ya kamo hannun shi yana murmushi ya ce"Kwantar da hankalinka bazaka mutu ba sai ka ga d'ana insha Allah,daga yau sai ka fara k'irga ranar aure na nan da watani kad'an musu zuwa".Sarki cikin jin dad'i ya ce"Allah yasa Abdurrahman ,dan baka tab'amin maganar aure ba sai yau,ko ba komai insha Allah nasan ko mai ya kusa zama tarihi".
D'an juma har ya fita alhaji bai shigo ba yana ban d'aki ".

B'angaran Meenal kuma ta hura ma mommynta wuta ita fa bazata kuma kwana garin nan ba daga gobe ba.
Meenal sai nai man wayar da zata Kira daddynta take babu,gashi wayar mommynta tunda ta bugata da k'asa ta d'auke,wayarta kuma M.T.N gareta batayi hausar cire Sim d'in mommynta ba tasa awayarta ba.Mommyn Meenal kuma ta hana mahaifiyar d'an juma taba Meenal wayarta ta ce ta ce mata bata da caji.Sosai Meenal ta shiga damuwa dan so take tai waya da daddynta ruwa ajallo.Tana nan tana tunanin ya za tai d'an juma yayi sallama ya shigo"

D'an juma da ledar kayan tea d'in Meenal hannun shi,ya mik'ama mahaifiyar shi,sannan ya gaida su,ya kalli Meenal ya ce"Sarki na kiranki".Meenal har zatace bazata ba,amma da ta tuno d'an juma na da waya zata ara ta kira daddynta batare da mommynta bama taji abinda zatace ba,hakan yasa ta tashi ta yafa d'an kwalin abayarta ta fita,d'an juma yabi bayanta shima.

Suna fita daga gidan Meenal ta kalli d'an juma ta ce"D'an aramin wayarka". "Ayyah nabadata caji amma idan na amso zan baki idan kuma kin matsu da yin kira idan mukaje sai ki amshi ta sarki kiyi amfani da ita".
Meenal shiru tayi sannan ta ce"Badamuwa idan ka amso nayi kiran".Meenal na fad'in haka ta juya zata tafi.D'an juma yayi saurin cewa "Sarki na kiranki fa nace"."Bazan je ba".Meenal na fad'in haka ta juya tayi ta fiyarta.D'an juma d'aga murya yayi ya ce"Bari inzo in cema Mommy kince bazaki ba".
Meenal da dowa tayi taja ta tsaya gaban d'an juma tana kallan shi,shima ita yake kallo.Meenal tsaki ta yi ta ce"Uhm dan Allah ka d'an taimakeni magana,Wallahi bazan iya shaba,kuma alhaji ya sa daddyana indai ban sha ba sai dai in ci gaba da zama kyauyan nan,ni koma gaskiya bazan iya shaba,dan Allah ka san abinda zaka ce mai ya baka ka kawomin".Shiru d'an juma yayi sannan ya ce"Tom Mommynki fa ai zataga biki shaba".Meenal ta ce"Ai idan ka amso zuwa zan rik'ayi da sunan zanje amsowa idan nagama zamana in koma".Murmushi d'an juma yayi ya ce"Shikenan sai anjima,bari inje in amso".
Meenal juyawa tayi ta shige gida tana jan tsakin takurata d'in da duk akayi".

D'an juma gidan Sarki ya koma yace ya bashi ya kai ma Meenal ,yaje ya isketa batajin dad'i.Sarki ba d'an juma yayi ya ce ya tabbatar ta sha.D'an juma na fitowa ya kurb'e addu'ar acewar shi ayar Allah ce,inda yasan ko ya kaima Meenal ba sha za taiba,zubarwa za tai"

Yau d'an juma da wuri ya dawo daga funtua,yayi wankan shi cikin wani brown d'in yadi,masha Allah sosai d'an juma yayi kyau ya shafe kayan shi da aribian oud.
D'an juma ya fito zai tafi gidansu,suka ci karo da sarki ya fito ban d'aki.
Sarki murmushi yayi dan indai kaga sauri ya d'au wanka da daddare tom ba sai ya fad'aba kasan inda za shi.Sarki da fara'ar shi najin dad'in d'an juma ya fara nai man aure ya ce" Abdurrahman daga ganin kwalliyar nan nasan gimbiyarka zaka gani".Murmushi d'an juma yayi yana mai jin wata irin fargaba ya ce"Sarki yau ne zan fad'ama yarinyar da nace maka ina so,tom ina fargaba ka tayani addu'a Allah yasa ta amince".Sarki hannun d'an'juma ya kamo ya ce"Bacin kayi addu'ar fita gida,ka karanta izaja'a,insha Allah zaka samu nasara".D'an juma cikin jin dad'i ya ce"Nagode ,bari in tafi" .
Sarki Kiran shi yayi ya ce"Bari in d'akkoma addu'ar Amina idan ka dawo wajan gimbiyartaka ka biya ka kai mata".
Sarki d'akin shi ya shiga ya d'akko addu'ar yaba d'an juma.
D'an juma amsa yayi ya tafi ,azuciyar shi yana cewa"Sarki wadda zan ba addu'ar nan ita ce gimbiyar tau,amma kai kanka fargabar sanar maka nake yi".

Haka d'an juma ya kama hanyar gidan su ,zuciyar shi na cike da fargaba"

B'angaran Meenal kuwa ta k'osa d'an juma ya shigo ya bata wayar shi ta Kira daddynta,dan jin shirun yayi yawa,yasa ta ce ma mahaifiyar d'an juma "Wai yau ba zai zo bane?".Mahaifiyar d'an juma da bata gane abinda take nufi ba,ta ce"Waye ba zai zo ba?" ."Wanda ke ....".Sallamar d'an juma ce tasa Meenal ta yi shiru............✍️

Idan kin karanta ki daure ki Comment Sister.

Share & Comment please🙏🏻🙏🏻

📚 MEENALYN DADDY 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Na
Fadila Sani Bakori.

Page 17 & 18.

Daddyn Meenal tashi yayi yazo inda Mahaifinshi yake ya rik'e k'afar alhaji ya ce" Alhaji dan Allah ka canza wani abun ba wannan ba,na yi ma Meenal alk'awarin ba zan mata auran dole ba,dan Allah ka barni in cika alk'awarin da na d'aukar mata".
"Kwantar da hankalinka Sani,babu wanda zai ma Amina auran dole".Cewar Sarki.Alhaji kallan sarki yayi ya ce"Alk'awarin da na d'aukarma Abdurrahman fa?,Sannan Amina bawai Abdurrahman bane bata so kuwa ma baso take ba".
Shiru sarki yayi sannan ya ce"Duk da haka alhaji baza ai ma Amina auran dole ba".
alhaji da ran shi sosai ya b'ace ganin yadda Sani ya fito k'iri-k'iri ya nuna baya son d'an'juma,hakan yasa alhaji cikin tsantsar b'acin rai irin Wanda daddyn meenal bai tab'a gani ba ya ce"Sani tashi ka tattara kaida iyalinka kubar garin nan yanzu-yanzun nan!".
Daddyn meenal ganin yadda ran mahaifinshi ya b'ace sai kuma hankalinshi ya tashi ,kallan maihaifinsa yayi ya ce"Alhaji dan Allah kayi hak'uri".Alhaji cikin d'aga murya ya ce"Sani ka d'auki iyalanka nace ku koma Kaduna ka cikama 'yarka alk'awarin da kai mata ".
Daddyn Meenal cikin sanyi ya ce"Alhaji kai fa?".Bazan tafi da kai ba,gobe Sule yazo ya d'aukeni ".
Daddyn meenal shiru yayi,k'arshe ya gama zamanshi ya tashi ya tafi cikin sanyin jiki".

Alhaji Abba ko da ya fita rasa inda zaiyi ya yi , dan baisan gidan da su meenal sukeba.Tunanin number da meenal ta kirashi ta fad'omai,hakan yasa ya ciro wayar shi ya Kira number d'an'juma.
D'an'juma ko dama yayi serving number daddyn meenal,hakan yasa daddyn Meenal nakiranshi ya gane mai Kiran ya d'aga yana mai yin sallama.
Alhaji Abba amsawa yayi sannan ya ce"Meenal ce ta kirani da number nan,dan Allah ko tana kusa"."A'a bata kusa, ina Funtua ne ,sai dai in nadawo".Cewar d'an'juma"
Shiru alhaji Abba yayi sannan ya ce"Ina son inje wajan su ne,babu yadda za ai?".D'an'juma cikin girmamawa kamar daddyn meenal na kusa da shi ya ce"Kana ina ne sai in turo yaro ya tafi da kai?"."Ina k'ofar gidan sarki"."Tom bari in turo yaro sai ya k'arasa da kai gidan".
D'an'juma na fad'in haka ya kashe wayar ya kira yaran shi sule mai tsaran shagon shi ".

Daddyn Meenal na jikin motar shi tsaye cikin damuwa sosai,sai ga Sule da d'an'juma ya turo.Sule gaida daddyn meenal yayi sannan yayi mai bayanin shine Wanda d'an'juma ya turo yaraka shi gidan su.
Alhaji Abba motar shi ya bud'ema sule ya shiga suka tafi.
Chapter 12 · 0% Book details