Sashe 9
Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce shikenan tunani na ya tabbata,Ali da ka zauna a gida babu abunda ka ke sai shaye shaye,gashi har ta fara taba kwakwalwar ka,ya dada bushewa da dariya. Aliyu ya sassautar da murya dan Allah C. Suleman ka taimaka min,wlh lfy lau na ke. C. Suleman shi ma ya tsuke fuska tare da fadin bazan iya ma ka wannan ba,shin wanda ya ba ka shawarar auren kisan wutar be fada ma ka ba auren ba ya hallata a musulunci? Aliyu ya ce shaye- shaye ko bin mata wanne ne daga ciki ya halatta wanne ne ba ka yi? Sai da aka zo wajan taimako na ka ce za ka bada hujja da Allah? C. Suleman ya tashi ya je ya bude kofa ya juyo ya kalli Aliyu ya ce like seriously ba ka cikin hayyacin ka,duk sanda ka fara tunani da kyau let me knw pls. Ka rufo min office idan ka tashi fita. Ya fice abun sa. Aliyu ya buga hannu a table ya na fadin i hate this more dan you dammit!ya tashi ya fita a fusace. Bangaran Hajiya kuwa tin tafiyar Aliyu be kara waiwsyar su ba,har wajen mallam da boka sun je dan a mantar da Aliyu abunda ya faru a jawo hankalin shi gare su amma abu ya gagara,kullum lamari dada lalacewa ya ke. Yau ma daga wajan wani bokan su ke. Hajiya ta ce Allah dai ya sa ba wahalar banza mu ka sake yi ba Indija. Indija ta ce amen dai Hajiya,wlh ni abun har tsoro ya ke ba ni. Hajiya ta ce ba ki ji bokan ya ce taurin kai gare shi ba? Wlh halin uban sa ne ai. Tashi ki dauko turmi ki ga mu fara daka maganin. Indija ta dauko turmi suka fara aikin boka Matar mu 45;46;47:ko da C. Suleman ya koma gida da daddare sai ya nemi bacci ya rasa,taba kuwa ya shanye kusan kwali biyar ya kan na shida,da ya dau tsinke daya zuka biyu ya ke ma ta ta kare. Gaba daya Aliyu ya jagula masa lissafi,mtsw ya ja tsaki yayinda ya tsuki taba ya fuzar da yaki saba. Ya ma za a yi Aliyu ya tinkare shi da zancen nan? Ya za ayi shi Suleman ya auri Jauda? Wai auren kisan wuta?Ai ko na kisan gobara ne da sake! Nan ciyar shi ta shiga sake saken yanda zai kaucewa zancen Aliyu,dan shi mutum ne mai dan karan naci idan ya so abu,tabbas sai ya dawo gare shi… Bangaran Aliyu kowa dama tin rabuwar mu ya yi hannun riga da bacci,in har ya sami bacci toh sai dai sace shi ya yi. Shima zaune ya ke a falo,hannun shi rike da hoto na. Cikin zuciyar sa kuwa saka yanda zai yi ya Sule ya yarda da kudirin shi ya aure ni ya kuma sake ni dan ya samu ya dawo da ni,idon shi ya rufe sam baya cikakken tunani,shi dai kawai ya maido ni gidan sa. Birnin yola ni ma hakan take,ba na iya bacci dan da na fara tashi na ke a firgice. Sai da aka dage da addu’a sosai. Cikin zuciya ta na kasa gane mai na kewa Aliyu,tsana ce ko kyewa?da ga baya na yanke hukuncin duka biyun ne,kai ba ma Aliyu ba,duk wani da namiji na tsane shi… Ranar wata lahadi da yammaci C. Suleman na shirin fita sai ga C. Aliyu,da ganin shi sai da gaban shi ya fadi dan rabon shi da Aliyu tin ranar da ya zo ma sa da zencen auren na,ko waya ma sa ba ya dagawa. Kamar mara gaskiya C. Suleman ya rasa makama. C. Aliyu ya karaso gare shi ya ce Suleman,kan ka cemai kawai sai ya durkusa gaban shi,ya sake cewa Suleman na durkusa gaban ka,na zo gare,ka taimaka min ka rufa min asiri. Tini C. Suleman shi ma ya durkusa ya ce ni ma na durkusa ma Aliyu,ka taimake ni ka janye wannan maganar. Aliyu ya ce auren kisan wuta ba wai auren da za ku zauna zaman aure ba. C. Suleman ya ce martaba da kimarta ya fi gaban haka,Aliyu ya ce ba dadewa za ka yi tare da ita ba,idan ka ga dama ko tariya ba za ta yi ba. C. Suleman ya ce ko na sakanni uku ne bazan iya ba,Aliyu ya ce ka duba dangan takar mu da zumunci… C.Suleman ya ce su na dabu shi yasa bazan iya ba….Aliyu ya mi ke a fusace ya na fadin an gaya ma ka ni ma ina jin dadin tambayar ka ne Suleman! Wallahi ji na ke tamkar rai na zai fita duk sanda na maka maganar,amma sai dada kunta ta min ka ke,ka kasa taimaka min,haba dan Allah,idan ba kai ba wazan yarda da shi da wannan maganar,dan na yarda da kai ne Suleman,yarda ce ta kawo na san ba za ka cutar da ni. C. Suleman ya tashi a sanyaye ya ce Aliyu na yarda zan yi abunda kake so na yi maka,amma bazan buye ma ba,ka takura min,ka matsa min ka shiga rayuwata Aliyu. Aliyu ya dafa kafadar shi tare da fadin na sani Suleman ,na kuma gode Allah ya bar zumunci,inshaAllahu ba za ka yi dana sani ba. Ya fice ba tare da bata lokaci ba dan karda ma Suleman ya canza ra a yin sa. C. Suleman rai a bace ya koma dakin ya bude kwabar giya ta konkwada ya yi tatir. [7:07pm, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 47;48;49:Washagari C.Suleman ya je ya sami Anty Sa’a ya sheda mata ya sami matar da zai aura,ta rangwada guda,ta ce ai bari ta yi sauri ta yiwa General albishir. Ko da General ya ji yayi matukar farin ciki,ya kira C. Suleman domin jin maganar da ga bakin shi. General ya kalli C. Suleman da ke durkushe gaban sa ya ce waye mahaifin yarinyar ka ga ya kamata mu je mu gabatar da kan mu ko? Nan fa daya zufa ya shiga ketowa C. Suleman,ya sa hannu ya share ya ce ai Sir dama duk gida ne,Jauda ce wacce na ke so na aura idan ta gama idda…Anty Sa’a ta doka salati,shi kan shi General maganar ta ma sa ba zata,amma sai ya yi sauri ya mai da mamakin shi cikin rai sa. Anty Sa’a ta ce sam da sake,ba za ka ja mana zagi ba,matar tsohon abokin na ka Sule?ko iddar ba ta gama ba kafara kai hari? General ya ce ina Sule,ka na ji na? C. Suleman ya amsa da kasan makogwaro Ina ji Sir. General ya ci gaba a hakika nin gaskiya ba zan iya goya maka baya a wannan magana ta ka ba. Anty Sa’a ta ce ko ni ma ban goyi baya ba. General ya ce sannan kuma ba zan hana ka neman auren Jauda ba, Anty Sa’a ta karbe ni zan hana… Rai a bace General ya ce haba Sa’adatu!ya ina magana ki na katse min haka,wannan ai ba tsari ba ne. Anty Sa’a ta ce Allah ya baka hakuri. General ya koma ga C. Suleman ya ce umarnin da zan baka shi ne bayan Jauda ta gama idda ka je ka sami Mahaifiyar ta ka tambayi Izinin ta,idan ta amince ka nemi auren na ta sai ka zo ka same mu,mu kuma sai mu tinkari dangin mahaifin ta da zancen. C. Suleman ya ce toh madallah,na gode Sir,zan je yolan bayan ta gama idda. General ya ce toh Allah ya zaba abunda ya fi alkhairi. C. Suleman ya ce amen. Ya tashi tare da fadin ni zan tafi,a tashi lfy,General ya ce Allah ya sa,Allah ya kiyaye,ya ce amen ya fita ba tare da Anty Sa’a ta sake ce masa kala ba. Bayan fitar shi General cikin rarrashi ya ce Haba madam,ai irin wannan ba a nunawa kiri kiri ba a so,yanzu ma toh menene lefin auren idan ya nema? Ince ba mu muka dage ya fito da mata mu aura ma sa ba? Yanzu ya ce ga wacce ya ke so sai mu ce ba mu san zance ba?Anty Sa’a ta ce yanzu Oga ya rasa wacce ya ke so sai tsohuwar matara abokin sa? Ai sai jama’a su Zage mu! General ya murmusa ya ce tsohuwar matar abokin na sa dan ya aura haramun ne?yaya fa na saki kani ya aure bare kuma abokai,ba sakin ta yayi ba? Anty Sa’a ta ce amma dai halin suleman ne sai shi,shi Aliyun da mu ke gani nitsastse ga abunda ya aikata,bare kuma Sule wanda ba sai an tona ba ka dai san halin shi.. General ya ce haba madam kamar ba dan uwan ki ba?me zai hana ki masa fatan alheri,ki ka sani ko Jaudar ta zama ita ce hanyar shiriyar shi? Anty Sa’a ta ce Allah ya tabbatar da alkhairi,General ya murmusa yauwa ko ke fa. Ta tashi bari dai na karasa aiki na kar na bar zancen Suleman cikin rai na ya samin hawan jini. Kwanci tashi aka ce asarar mai rai,na kusa gama idda,na fara shirye shiryen komawa makaranta domin yin MBA(Masters in bussness admin) wanda na ke neman admsion anan Federal Uni ta yola,na kuma shiga wata islamiya ta matan aure wanda na ke zuwa weekends.Ina kwance a daki waya ta ta fara kara,na dauka gami da karawa a kunne na na ce Salama’alaikum,na ji shiru,na ce hello,hello,tsit ba amsa. na katse ina fadin na tsani irin haka wlh,Jiddah ta shigo ta ce ke dawa kuma? Na ce wlh wata number ce ta matsamin kwanan,kamar dai waccar,sai a kira a ni amma a ki magana,ina ga zan dai na daga number da ban sani ba kawai,Jiddah ta ce shikenan ya fi sauki ma. [10:19pm, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 50;51;52:Aliyu ya kalli wayar da ke hannun sa ya ce Suleman kullum muryar Jauda dada dadi ta ke min. C. Suleman ya murmusa kawai ba tare da ya ce komai ba. Zaune su ke a Airport,C.Suleman ya rako Aliyu,a ranar jirgin su na zuwa sudan zai keta hazo. Aliyu ya dubi Suleman ya ce Suleman na san ba karamin takura ma ka na yi ba,na gode,Allah ya bar zumunci. C. Suleman ya ce karka gode min tukunna,ka bari na je yola na tattau na da Innar Jauda tukun,ta iya yiyuwa su hana ni. Aliyu ya ce abu ne mawuyaci