← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a shake ya ce menene wannan? Na ce ka duba ka gani mana. Sai da yau dauki lokaci har ina tunanin ba zai karba ba sannan ya karba ya karanta. A firgice ya tashi tsaye ya na fadin what! Ciki?ina ki ka samo ciki? Na dallah ma sa harara cikin takaici na ce cikin biyu akwai daya ko a daren yan maye na samo ko kuma a ruwan gidan ka na sha…ya daka min tsawa ke kar ki min rashin kunya,ma za ki shirya mu je a zubar da cikin. Ban san sanda na saki murmushin takaici ba na ce ai ni Suleman ban taba tunanin rashin mutuncin ka ya kai matuka haka ba,an fada ma daya daga cikin karuwan ka da ka saba zubar mu su da ciki ce? Ya ce ni ki ke fadawa haka? Who are you? kin san ko da wa ki ke magana kuwa? Na ce ni ce Jauda yar soja matar soja na ke magana da kai soja,kakin ka da ihun ka be tsorata ni bare kai kan ka captain Suleman Matazu! Yayi kasa da murya ya ce how dere you?ni ma na yi kasa da tawa muryar na ce I dare whenever i like. A fusace yayi sama da gudu ya na fadin yau i wil teach you the right time to dare,sai jikin ki ya gaya miki! A rude na kalli gabas da yamma,kudu da arewa ina nemam wajan tsira,na ga mukullin motar C. Suleman a kasa,ai tini na dauka na yi waje a guje,ban zame ko ina ba sai cikin motar na tada ina yiwa Ema hon ba kakkwatawa. Da sauri ya zo ya na kokarin bude min gate din C. Suleman ya fito dauke da dorinar shi mai baki uku. Cikin tsawa ya ce Ema don’t you dare open dat gate! Ema ya ce yes Sir ya ja gefe,na juya na ga Suleman ya nufo ni gadan gadan,na sa wa motar lock,na daura seat belt,na tada motar na je na daki gate din garam! Ema ya daura hannu biyu a kan sa,shi kan shi Suleman sai da ya runtse idanun shi,na sake komawa da baya da nufi komowa na sake dukan gate din sai na ji muryar C. Suleman ya ce kai Ema ba ta da hankali dan ubanka bude mata,da gudu Ema jiki na rawa ya bude min,na figi motar a guje na fice….. [12:53pm, 11/27/2014] Salma Ateeku: [11:02pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 19;20;21:Kai tsaye gidan Anty Sa’a na je,na tarar da ita zaune a falo ko da ta ganni na shigo mata a rude tini hankalin ta ya tashi. Ni kuwa ban boye ma ta ba na fada mata komai. Cikin jimami Anty Sa’a ta maimai ta a zubar da ciki?kai ni Sa’adatu ban san na biyun Suleman ba! Kwantar da hankalin ki babu mai raba ki da cikin nan sai Allah,ai zai zo ya same ni ne! Ile ko sai gashi ya iso cikin mota ta,ko ya aka yi ya iya binciko mukullin ma oho. Ku sa da ta shi motar ya faka,ya fito da sauri ya duba gaban motar shi ya ga yanda na lotsa masa gashi na fasa madubin duka biyu,ya girgiza kai,ya shiga ciki rai a bace. Kamar daga sama mu ka ji muryar shi ya na fadin ina mara kunyar nan,iyaka nan gudun na ki ya kare?ina ganin shi da sauri na koma kusa da Anty Sa’a cikin tsoro. A fusace Anty Sa’a ta ce kai kunyar gare ka da ka shigo min gida ba sallama! Kamar tababbe ya ce Salama alaikum,babbar yaya na same ki lfy,toh dan Allah kar ki sa baki ki bar ni na suburbudi yarinyar nan! Anty Sa’a ta ce ka ji hauka,kai da suburbudar ka ake yi dan abubuwan da ka ke ai da ba ka kai ie yanzu ba. Jauda tashi ki shiga ciki abun ki,na tashi simi simi na wuce C. Suleman kamar zai wafco ni. Bayan shiga na ciki ta kalle shi,kar ka tsaya min a kai kamar dogari pls!cikin huci ya sami waje ya zauna. Anty Sa’a ta ce wai kai Sule dan Allah yaushe za ka gane annabi ya faku?ya matar ka ta aure ta na da ciki ka ce ta zubar,kai da zubarwa ake a haife ka?ka na gani haihuwan nan nemanta mu ke ido rufe Allah be nufa ba amma kai tsageri ka samu ka ce kyautar ba ta ma ka ba? Suleman ya ce ba haka ba ne,dama akwai abunda ban sanar da ke ba babbar yaya,amma yau zan sheda mi ki,amma ki yi alkawari ba za ki fadawa General ba dan Allah. Cikin zumudi ta ce ta yi alkawari dan Allah Allah ta ke ta ji abunda Suleman zai fada. Ya fara da aure na da Jauda na yarda zan yi shi ne a matsayin auren kisan wuta…..Auren kisan wuta sule?Anty Sa’a ta maimata. Ya gyada kai ya ce haka,nan ya kwashe lbry komai da komai,be buye ba ya fada mata. Anty Sa’a salati kawai ta ke,amma Hajiya Mairo ta yi asara! Kai ko Sule me ya hana ka neman shawara ta? Dama akwai sirri tsakanin mu?yanzu ai ga irin ta nan,ga kuma rashin amfanin shan giya,ga shi ka sha ka afkawa yar mutane kamar dabba,kai kai kai Jauda abun tausayi ce,wallahi yarinya karama ta sha wahala! C. Suleman ya ce yanzu dai kaddara ta riga fata,dan Allah Anty Sa’a ina mafuta?kin ga gwara dai kawai a zubda da cikin…inaaaa! Anty Sa’a ta katse shi,wallahi nan kuma ba ka isa ba,babu wanda ya isa ya zubarwa yar mutane da ciki,sai ta haife shi,idan kai ba ka so mu muna so,bayan ta haife ka sake ta din abokin na ka ya aura. Anty Sa’a zumunci na ke ji,ban san zumunci na da Aliyu ya lalace ki taimaka min. Anty Sa’a ta ce zumunci ai tin ranar da ka yarda da wannan auren kisan wutan ka sa wuka ka datse zumunci,ai yanzu kuma sai dai gyaran ubangiji kawai. C. Suleman ya dafe kai ya ce na shiga uku. Anty Sa’a ta ce mu ko daya ba mu shiga ba,kuma wallahi ko ciwan kai na ba gaira ba dalili Jauda ta yi toh kai ne,kuma sai na fadawa General. C. Suleman ya dafe kai,ya ce toh dan Allah kar dai ki fadawa General,ta ce indai ka kiyaye sharadai na babu mai ji. Ya yi ajiyar zuciya,kin ga kuwa yanda ta bata min mota? Ka godewa Allah da ba ta kashe kan ta ba,da alhaki a kan ka.Ya ce karbo min mukulli na,kuma dan Allah ki ja mata kunne kan gangacin da ta yi yau,wallahi na tsorata,ga na ta mukullin. Anty Sa’a ta amsa ta ce zan mata sosai ma kuwa,dole ta kula musamman yanzu da ya ke ba ita kadai ba ce.ta shige ciki. A fili ya ce na fuskanci babbar yaya ita burin ta ta matsa min kawai ta ji dadi… Ta karbar ma sa mukullin ta bani nawa. Bayan tafiyar shi ne tamin nasiha mai shiga jiki akan zaman aure da kuma gangacin da na aikata yau. Sai bayan magariba na koma gida. [01/11 22:47] Salma Ateeku: :56am, 11/22/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 37;38;39:Washagari da safe bayan na yi wanka na ji saukin jika na sosai,amma dai ban dai na amai ba. Ina fitowa falo kamshin suyan kwai ya doki hanci na,gaba daya na ji zuciya ta na tashi,da sauri na koma ciki ina karasawa toilet sai amai,kamar hanjin ciki na zai fita. Bayan na gama na daddafa na dawo daki na zauna ina sakar zuci,shin waye ma mai soya kwan?S.Man be ta office ba?bayan wani dan lokaci na sake fita dan zuciya ta ta zaku da ta ga wanda ya ke suyan. Akwai karnin suyan kwan amma ba kamar na da ba. A kitchen na same ta,fara ce kakkaura,ta na da zane guda uku,daga ganin ta ka san ba bahaushiya ba. Ta waigo da sauri da ta ji motsina a bakin kofa,irin kallan da na ke ma ta ya sa ta gane ina bukatar bayani. Ta yi sauri ta ce ina kwana madam? Cikin mamakin ganin ta na ce lfy,yau kuma ke ya turo ki masa girki? Na ki aikin kenan? Ta susa kyeya tare da fadin ni?ni ce sabuwar mai aikin ki,Hajiya Sa’a ta turo ni,Oga ya ce kar a tashe ki bacci ki ke. Na saki numfashin da ya tsaya saman kirji na,na ce ina Ogan ya ke?ta ce tin dazu ya fita. Na kalle ta tin daga sama har kasa na ga ba laifi ta na da tsafta amma bana bukatar mai aiki,da na sami sauki sosai zan sallame ta. Na tambaye ta sunanta ta ce jummai. Na ce wa ya sa ta girki toh? Ta ce Oga ne ya ce ta hada min brkfast,na ce toh bana san kwai ya na sani amai,daga yau ma na hutasshe ta zan na yin girki na da kai na,za dai ta na min wanke wanke da shara. Ta amsa da toh. Na ce wanda ta dafa yanzu za ta iya cinyewa. Na koma falo na zauna ina tunanin me zan ci txt din S.man ya shigo,na karanta….. “I hope kin tashi by now,ya jikin na ki. Ga mai aiki Anty Sa’a ta turo,ba kwana za ta na yi ba,amma in ba ta miki ba pls notify me,tak kia…..” Bayan na gama karantawa,sai na mai reply da…. “All is well,tnx” Ni na ji zaman gidan ma ya ishe ni,na kira Jiddah na ji zancen admsion din mu ta ce ai an tafi strike,na dai yi addua a dawo,shin S. Man zai ma bar ki ki bar kano ki je yola yin MBS da auren shi akan ki,a rai na nace auren ai suna ne. Na ce me zai hana,ki dai da an koma an saki addmision din ki fada min. Ta ce toh InshaAllahu. Sati biyu kenan jummai ta na min aiki,yanda ta ke da tsafta da kuma ladabi ya sa na sami saukin ma amma na kasa sallamar ta. Dangantaka na da S.man ba wani cigaba,amma na lura ya rage kwana a waje in dai ba wai aiki ba. Da yamma ina zaune ina karatun al- qurani,takun takalmi na fara ji tare da wani ni’imantaccen kamshi,daga ido na na yi ido biyu da wata kyakkawar
Chapter 12 · 0% Book details